Alkalancin Shehu Jaha

Alkalancin Shehu Jaha

Alkalancin Shehu Jaha

0
0

Wata rana wani mutum ya yo itace a daji yana kan hanyarsa ta dawowa sai suka kwance suka zube, ya rasa ya zai, sai ga wani mutum ya zo zai wuce, sai mai itace ya ce Malam ka taimaka ka taya ni mu tara itacen nan mu daure.

Mutumin ya ce idan na tayaka me zaka ban? mai itace ya ce
zan baka ‘babu’. Mutumin ya taya shi suka daure sannan ya ce bani abun da ka ce za ka ban.

Mai itace ya ce ai babu na ce zan baka. Mutumin ya ce to bani babun, ai ko sai rikici ya balle a tsakaninsu har ta kai su
ga alkali suka yiwa alkali bayani, alkalin ya yi dabaransu na alkalai, amma ina mutumin ya ce dole sai an ba shi babunsa,sai mutane suka bawa alkali shawarin a nemo shehu domin shi kadai ne zai iya warware wannan sharia.

Aka nemo Shehu da ya zo aka shimfida masa darduma ya zauna mai kara ya yi bayani wanda ake kara ma ya ce gashi gashi.

Ko da Shehu ya ji haka, sai ya ce wa mutumin kanaso a baka babun ka ko? Mutumin ya amsa
da eh ,kawai sai shehu ya daga dardumar da yake zaune akai ya ce leka, mutumin ya leka sai
shehu ya ce me ka gani ?Mutumin ya ce babu, sai
Shehu ya ce to dau babun ka yi tafiyarka, kana wahalda sharia.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *