Firar Tata da Katsina Post Hausa (KASHI NA DAYA)! Ko kasan asalin sunan ‘TATA’? (KARANTA)

Firar Tata da Katsina Post Hausa (KASHI NA DAYA)! Ko kasan asalin sunan ‘TATA’? (KARANTA)

Firar Tata da Katsina Post Hausa (KASHI NA DAYA)! Ko kasan asalin sunan ‘TATA’? (KARANTA)

0
0

Kamfanin jaridar POST MULTIMEDIA da suke wallafa jaridun Katsina Post da kuma Katsina Post HAUSA sun samu damar tattaunawa da tsohon dan takarar Gwamnan jihar Katsina a karkashin jam’iyyar APGA a zaben da ya gabata na 2015.

A cikin firar ya yi bayanai masu tsawo da muhimmaci tun daga tarihin sa zuwa darussan da ya samu a siyasance.

Ya kuma bayyana mana ra’ayin sa game da gwamnatin APC mai ci yanzu da kuma ainihin alakar sa da tsohon Gwamnan jihar Alhaji Ibrahim Shehu Shema.

Firar tana da tsawon gaske don haka muka rarrabata don jin dadin ku masu karatun mu.

Da fatan za’ayi karatu lafiya, zakuma a ci gaba da bin mu don karanta sauran karashen firar.

A sha karatu lafiya.

Katsina Post: Da farko dai muna son sanin tarihin ka.

Tata: Ni suna na Umar Abdullahi Tsauri, tun ina yaro wani mai reno na ya samani suna ‘Tata’, Tatan kuma ta biyo ni har yanzu. An haifeni a cikin garin Dutsin-ma a 14 ga watan Fabrairu a shekara ta 1968. Nayi karatun firamare da sakandire a cikin garin Dutsin-ma sannan na wuce Jami’ar Bayero dake Kano inda nayi karatun share fagen shiga jami’a. Allah cikin ikon sa naci gaba da karatun zuwa shekara ta 1990 inda na kammala sannan kuma na tafi bautar kasa a jihar Borno lokacin tana tare da jihar Yobe na koyar a wata makaranta a garin Potiskum daga nan kuma na samu aikin gwamnatin tarayya a Legas inda na cigaba da aiki har 2013 inda na aje aki a matsayin mataimakin Darekta a ma’aikatar man fetur ta kasa baki daya.

Ina da mata 3 (cikin dariya), akwai sauran wajen mace 1 har yanzu. Ina da yara 12 sannan ni maraya ne.

Katsina Post: MashaAllahu. Da alama kam an sha gwagwarmaya sosai. Zamu so muji me yaja ra’ayin ka ka fara siyasa?

Tata: Hakane kam. Amma dai duk da haka na taba kwatanta takarar shugabancin karamar hukumar Dutsin-ma a 1992-1993 lokacin Shonekan kafin Abacha ya karbi mulki amma dai ban shiga siyasa ba gadan-gadan sai a shekara ta 2010 zuwa 2011 lokacin da na shigo domin in kawo gudummuwa ta ga dan takarar gwamnan jihar Katsina mai neman komawa a karo na biyu watau Ibrahim Shema a garin Dutsin-ma saboda irin kalubalen da yake fuskanta a garin.

A lokacin na kalli ayyukan alherin da yayi a wancan lokacin sai kuma naga sakayyar mutanen garin batayi dai-dai ba da yadda yake mulkin. Wannan ne yasa nazo na kafa kungiya domin muzo mu taimaka masa wajen zaben nasa ba wai don shi ba -a’a sai don al’ummar Dutsin-ma don mu fita kunyar cewa anyi mana alkhairi amma mun maida da sharri.

To wannan dai a takaice shine sanadin shiga ta siyasa, daga nan kuma sai Allah ya daukaka abun har zuwa yau. Ban zaci zanyi siyasa ba har inyi takara amma dai Allah cikin nashi ikon ya canza lamarin zuwa hakan.

Katsina Post: Zo zaka iya kwatanta mana ya rayuwar ka ta kasance kafin shigar ka siyasa da kuma yanzu bayan ka shiga?

Tata: Gaskiya akwai bambanci kwarai da gaske. Kafin in fara siyasa ina gudanar da rayuwa tane ta wa amma daga sadda na fara siyasa sai na koma rayuwar al’umma. Wannan shine babban bambancin da na samu gaskiya.

Katsina Post: Kamar wane irin darussa ne da kuma ilimi shigar ka siyasa ta koyar da kai musamman ma tsayawar ka takara a 2015?

Tata: (Dariya) To babban ilimin da na koya daga siyasa shine:

Na farko dai shine dole sai mai hakuri zai iya siyasa. Wanda bai da hakuri ba zai iya ba.

Na biyu shine sadaukaswa. Yau idan mutum zai so kan sa to ba za’a so shi ba. Duk wani matsayi da na kawo yanzu a siyasar jihar Katsina ba komai bane illa rashin rowa. Da na sa rowa a cikin rayuwa ta da ba’a kawo haka ba.

Na ukku shine rayuwa gaba dayanta ibada ce. Na fahimci cewa shugabanci wajibi ne a addinance, haka manzon Allah SAW ya koyar da mu. Shi kuwa shugabanci a yanzu bai samuwa sai ta hanyar siyasa. Don haka ni na shiga siyasa ne ba don komai ba sai don yi ma addinin Allah aiki. Amma sai wasu daga cikin al’umma suka dauka cewa ni kawai wani yaro ne ya samu kudin da bai san abun da zaiyi da su ba so nikeyi sai na sayi Gwamna da karfi da daji.

Shi yasa zaka ga suna cewa muje wajen Tata mu samo amma duk da hakan bai hanani kyautata masu ba dai dai karfi na. Wasu na san su wasu ban san su ba.

Na hudu shine na fahimci cewar kayi abu don Allah kawai ka bar mashi sakamakon. Duk abun da mutum zai yi to yayi shi kawai don Allah ba don mutum ya saka mashi ba.

Daga karshe na fahimci cewa addinin Allah bai da gata -yana neman gata yana kuma neman taimako. Wannan taimako kuma zai zo ne ta hanyar shugabanci kyakkyawa. Wannan yana daya daga cikin abubuwan da suka rikeni cikin siyasar duk kuwa da cewa bani son ta.

Katsina Post: Muna so muji karin bayani game da shari’oin da kakeyi da mutumin nan da ya ci kudin marayu a garin Faskari.

Tata: To. Ita dai shari’ar garin Faskari Alkalin garin ya kori shari’ar ya kuma wanke wanda ake zargin da cewar bai ci kudin kowa ba. Wannan ina ga idan zaku samu alkalin to shi zai kara baku bayani.

Ko da yake magana ta gaskiya abunda ya faru shine; shi wanda muka maka kotun watau Bishir Wada yana jagorancin tattaro mashi mutanen da suka ko da taba gaisawa ne da Tata, saboda wannan matsayin da yake shine sai Gwamna yake ganin kamar so a keyi a tozarta Bishir Wada din. Don haka a maimakon ya biya kudin da ake zargin ya cinye ko ya tabbatar da an yi ma marayun adalci sai ya tsawata ma Alkalin kan lallai sai ya kashe shari’ar. Ni kuma na sha alwashin idan har na zama Gwamna to wannan hakkin zai fito inshaAllahu.

ZAMU CIGABA INSHA’ALLAHU..

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *