CANJIN RAYUWA [Kashi na biyu] Tare da Halima K Mashi (Shafi 26 – 30)

CANJIN RAYUWA [Kashi na biyu] Tare da Halima K Mashi (Shafi 26 – 30)

CANJIN RAYUWA [Kashi na biyu] Tare da Halima K Mashi (Shafi 26 – 30)

0
0

Ta yi dan huci,ta mike. har ta kai bakin kofa,ta kasa jurewa,ta dawo, Alhaji wai laifin me na yi maka da duk ka canza min.ya kalle ta,baki san kin yi laifin ba ko?ta ce,wallahi ban sani ba.ka sanar da ni mana.ba sai in baka hakuri ba.ya ce, ban zaci zan ce ki yi abu ba,amma ki ce min ba za kiyi ba.ni ne na ce kiyi wa MIMI fada kan ta bi zabin da nayi,amma kika ce min ba za kiyi ba,karshe ma sai kika zuga ta ta katse shi,na zuga ta kuma?

ln ji ta ne ta ce na zuga ta?shawara na ce zan bata,kuma na bata. ka tambaye ta wace irin shawara na bata?zan yi mamaki sosai in ka ce ka mance halina.a tunanina mun kai matsayin da zaka san abin da zan iya da kuma wanda ba zan iya ba.don ni yanzun zan iya rubuta kundi a kan halayyarka.haka kuma in an fadi wanda ba za ka iya ba,zan ce sam baza ka iya yin haka ba.kansa yana kasa,yayi shiru,domin ya san cewa gaskiya ta fada.can ya dago kai,me kika ce mata?ta mike ta koma kusa da shi.bayan ta dauki wayarsa ta soma latso lambobin ta kai kan lambar MIMI  ta dannan kira,ta latsa handsfree sai da ta soma ringing ta mika masa,ina son ka tambaye ta,mu ji.

Kafin ya ce,aa,har MIMI ta daga,muryarta ta ratso,inda ta ce,hello dad.ya ce,MIMI,in tambaye ki?ta ce, eh dad.ya ce,me mamarki ta fada miki game da auren abbas?ta ce,wace maman,momy nafisa?ya ce, mahaifiyarki.ta tura baki,dad cewa fa tayi wai in hakura in bi abin da kake so,ko don irin kaunar daka nuna min.wai shawara ta bani.ya ce,shi ke nan.     yana kashe wayar sauda ta mike.ya kamo hannunta, kar ki yi fushi matata,ki yi hakuri,na fahimce ki.bai-bai ta dan yi jim,ta ce,shi ke nan ya wuce.ya ce,to zauna muyi maganar auren MIMI.ta ce bani da ta cewa game da auren MIMI,face allah ya bada zaman lafiya. yanzu ka hakura zaka ci abincin?ya girgiza kai,aa sai in kin zauna.ta lumshe ido, ta zauna.ya ce,ni ma na yi miki laifi ban fada miki komai ba.yau saura kwana bakwai.kuma za a yi bikin ne a can abuja.sauda ta ce,babu damuwa. allah ya sa a yi lafiya.ya ce ameen.

Ameen.me kuke bukata a cikin bikin ke da yaranki? ta ce,ba ma bukatar komai bikin da ba a nan za a yi shi ba.mu ma fa yan gayyata ne.ya ce,ba na son kina fadin haka.ba za kuyi ashoben ba?ta ce,aa ba za mu yi ba.ya ce,don me?ta ce,ba za mu samu dinki ba kar ka damu.ya ce,shi ke nan.ya kwana,washegari ya wuce malumfashi.ya koma abuja saura kwana biyar biki.kuma ranar ne aka yi jeren amarya a gidan angonta. lsma’il ya isa abuja yammacin magariba. maigadi da ya soma ganin sa ya sha mamaki.ya ce, malam kai ne ka dawo?ya ce,ni ne daga kiran sallar lsha’i ne,alhaji ya bukaci ganin lsmail a kebe.bayan sun gaisa ne alhaji ke tambayar lsma’il lafiya ya dawo da wuri?lsmil bai boye masa komai ba.ya fada masa abin da aka yi masa,ya ji ya tsanin garin katsina.alhaji ya ce, kar ka damu.allah yasa haka ne mafi alheri a gare ka.lsmail ya ce,amin na gode

Washe gari saura kwana hudu biki,amarya ta sha gyara jiki,ita da na’ima.duk abin da aka yi mata,an yi wa na’ima.mai gyara ta musammam momy nafisa ta dauko.an zuba musu zanen lalle har ba za ka iya bambance amarya ba.kawayen MIMI su mina suna ta kai koma don ganin shirye-shiryensu sun kayatar.yammacin laraba za su yi family night. na’ima tayi zaton zuwan ‘yan katsina,amma shiru. MIMI bata damu ba,don ta san ita ba zama za tayi ba. rashin zuwansu ma zai fi mata.a ranar alhamis kuwa za su yi ‘mothers day, wanda momy nafisa ta shirya.kuma a ranar ne MIMI suka shirya guduwa,ita da khalil dinta.amma momy nafisa a nata tsarin sai daren jumaa,in an dawo daga kumbo,an yi kamu ke nan sai ta sa MIMI ta tubure.daga nan sai ta tura na’ima ta ce wa dad din su ita ta yarda a daura da ita.

An yi mothers day lafiya an tashi ana ta daukar hotuna,MIMI ta daga wayarta ta kira khalil ta ce su zo,shi da wani abokinsa kamar za ta yi magana da wani ta fita wajen hall din ta nufe su.da mota suke,don haka ta shige.kai tsaye gidan su MIMI suka koma.babu kowa,duk ana gurin biki,amma dad yana nan.da ta dauko jakarta za ta sauko sai ta ji shi yana waya.tana fitowa ta ji ashe a falonsa yake,amma daf da babban falon nasu. sai ta yi sanda ta fice.da gudu ta ja mota suka tafi.

Ta dubi khalil,yanzu ina muka nufa?ya ce,kaduna. don in muka ce za mu kwana a abuja,da safe za a kama mu.haka cikin dare nan suk dauko hanyar kaduna,gudu suke yi sosai. ga shi lokacin sanyi.ga MIMI ba ta son sanyi,kuma kayan jikinta irin na amare ne,ba na dumi ba.ta kudundune duk da cewa khalil ya cire t-shirt din sa ya bata ta dora a kan kayan jikinta.shi kuma ya zauna da singileti.zuciyar MIMI ta kasa natsuwa,wani gefen yana fada mata cewa ba ta kyauta ba,za ta yi nadama,ta kunyata mahaifinta.wata zuciyar kuma tana zuga ta da cewa ke ki tafi kina kan daidai.alamarin dai ga shi nan.

Dayan dare suka shigo garin kaduna.sadau abokinsa shi ne ya kawo shawarar su shiga cikin wata unguwa su nemi otal,kar su kama na bakin hanya.ta titin kagoro suka shiga,inda suka sami wani otal suka kama.MIMI ta ce su kama mata dakinta daban khalil ya ce,dear za ki iya kwana ke kadai?ta ce,eh mana kar ka damu.ta yae,shi ke nan. daki biyu suka kama a sama.khalil ya kalli sadau bayan sun kwanta,abokina ina kake ganin ya dace mu je?sadau ya ce,gobe ku shiga motar sakkwato ko zamfara.ba za a yi tunanin za ku je can ba.khalil ya ce,ni da lagos na so mu tafi,mu boye kamar na sati daya.sadau ya ce,kai banza ne.wane sati daya.ai in ni kai sai na dinke yarinyar za mu fito. yadda dole za a aura min ita.

Khalil ya tashi zaune,ban gane ba.sadau ya ce,ina nufin,yayi kwatance da hannunsa da cikinsa.khalil ya ce allah ya sawwake.ba ni da niyyar in cutar da MIMI zan barin mu yi halastaccen aure da ita. sadau ya ce,ka ji matsalarka.a shawarwarin da na baka,wacce ce aka samu matsala?na ce ka sai da gwal din mom dinka,mun sai da na ce ka dauke ta ku gudu.ba ga shi ka yi nasara ba?khalil ya ce,ban dauke ta da niyyar aikata wani abu ba,sai don in fid da ta daga auren wani na.kai dai naka da safe ka kai mu garejin mota mu tafi.kai kuma koma gidanku mun gode.

MIMI kuwa ta kasa barci, sai juyi take yi.wayarta tana,silent,amma tana kallon kira.da wani ya yanke,wani zai shigo da farko ta ki dubawa,amma daga baya sai ta duba.kiran dad dinta ne da momy nafisa har da su na’ima. kuka take ta tayi tare da tausayin mahaifinta.ji take kamar ta daga ta ce su zo su dauke ta,kuma ta amince za ta auri wanda suke so.amma sai shaidaniyar zuciyarta ta kangare,ta kuma hana ta aiwatar da hakan.da zazzabi ta farka tare da ciwon kai mai tsanani,don haka sai batun tafiya ya fasu.sun fita suka sayo mata doguwar riga da hijabi ta saka,suka dauke ta zuwa asibitin biba.gado likita ya bata,don tana cikin damuwa.hankalin khalil ya kara tashi, tsoron sa kar wanda ya san shi ya gan shi burinsa su bar kaduna,

Amma da yaje daki na musamman suka kama,sam ba ya fitowa ko kofar daki.duk abin da suke so sadau ke zuwa ya sai musu.su kuwa su momy nafisa ba su ankare ba,suna can suna ta hidimar ganin kowa ya samu abinci. a zatonsu tana can suna hotuna da kawayensu sai lokacin da na’ima ta zo tana cewa momy ina sis MIMI?ga abbas sun zo da abokansa.nan fa aka shiga neman amarya,ba ta babu dalilinta.hankula suka tashi. nan dai biki ya kare.momy nafisa kuka wi-wi.nan ta kira alhaji bishir tana fada masa cewa MIMI ta zo gida?ya ce babu wanda ya zo gidan nan.shi ma zuwansa ke nan.daidai lokacin da suke yin wayar da a ce ya waiwayo da zai ga MIMI,tunda gilashi ne ya raba falonsu da nasa.

Ta ce masa,to MIMI dai an neme ta an rasa ta,ko kasa ko sama.har zuwa sha biyun dare ana ci gaba da neman ta lungu da sako, banda wayoyi da ake ta yi don ji gurin abokanen arziki. matuka hankalin alhaji ya tashi sosai.alhaji akilu ya kira shi yana jajanta masa. ya ce,amma alhaji bishir da ma yarinyar nan ba ta hakura ba?alhaji bishir ya ce,ta hakura mana.ga shi ana ta biki.sai yau a ce ta gudu?alhaji akilu ya ce,baka ganin ko yaron da suke yin soyayyar ne ya zo ya sace ta?alhaji bishir ya ce, komai zai iya faruwa.amma bari mu gani zuwa da safe.alhaji akilu ya ce,in ko ya tabbata yaron nan sace ta yayi,lallai babu abin da zai hana shi zaman gidan yari.ka ga halin da abbas yake ciki kuwa?ya ce,ko ni ma ba zan kyale iyayansa ba bare shi,tunda daga gani ba da yardarta ya sace ta ba, domin bata bar wani sako ba,ba ta dauki komai na sawarta ba.

Alhaji akilu ya ce,kun kira lambarta?ya ce tana ta ringing ba ta daga ba.kusan karfe dayan dare alhaji bishir ya kira hajiya sauda tana barci,ta dauka, tana fadin,alhaji lafiya?ya ce ina fa lafiya,an sace MIMI.ta diro daga kan gado.an sace MIMI kuma?ya bata labarin komai hajiya sauda ta ce,ko dai guduwa suka yi tare da saurayin nata?ya ce, bana tunanin haka,ta nuna min ta hakura.kuma sun shirya komai da mijinta, har kudi ta cire a account din ta don gyaran jiki.

(Zamu ci gaba)…

Halima Kabir Mashi.

08081165107

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *