Jaridar KATSINA POST ta sadaukar da kyautar da ta samu ga al’ummar jihar Katsina

Jaridar KATSINA POST ta sadaukar da kyautar da ta samu ga al’ummar jihar Katsina

Jaridar KATSINA POST ta sadaukar da kyautar da ta samu ga al’ummar jihar Katsina

0
0

Kamfanin jaridar nan taku mai farin jini watau Katsina Post ta sadaukar da kyautar da ta samu ga dukkan daukacin mutanen jihar Katsina musamman ma masu bibiyar mu da kuma karanta labaran mu.

Ita dai jaridar ta Katsina Post ta samu tagomashin karramawa ne daga wata kungiya mai suna ‘Pleasant Library and Book Club’ dake da mazauni a jihar ta Katsina.

Kungiyar da ta shirya wani kwarya-kwaryan biki ne a inda ta karrama mutane da dama masu sana’oi kala kala dama sauran harkokin rayuwa wadanda acewar su ba kasafai suke samun karramawa ba daga al’umma.

Kamfanin na jaridar ta Katsina Post dai ya samu nasarar zama gwarzon ‘Dan Jaridar shekara’ na Katsina a cikin shekara ta 2016.

Daga karshe kuma muna mika cikakkiyar godiyar mu ga Allah madaukakin sarki sannan kuma da wadanda suka shirya wannan taron na karramawa sannan kuma muna mika goiyar mu ga dumbin masu karanta labaran mu da kuma bibiyar mu.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *