Kotu ta garkame wani saboda yi wa Gwamna Masari ‘kazafi’ a shafukan zumunta

Kotu ta garkame wani saboda yi wa Gwamna Masari ‘kazafi’ a shafukan zumunta

Kotu ta garkame wani saboda yi wa Gwamna Masari ‘kazafi’ a shafukan zumunta

0
0

Babbar kotun majestare ta Katsina ta daure wani matashi mai suna Gambo Sae’ed wata tara a gidan yari.

Gambo Sae’ed dan asalin karamar hukumar Mani ne ta jihar Katsina. 

Isfecta Isa Lili ne ya gabatar da karar a gaban kotu bisa karar da mai taimakawa gwamnan a kan rediyo Mansur Ali Mashi, ya shigar.

Mansur ya shigar da karar ne sakamakon yada jitajitar da Gambo Saeed din ya rika yadawa a kafafen sadarwa na zamani, inda yake cewa gwamna Masari ne ya yi rawa ya yi tsaki wajen tunbuke tsohon kakakin majalissar dokokin jihar Alh Aliyu Sabiu Muduru, tare kuma da kalaman batanci ga gwamnan.

Kotun ta bayyana cewa laifin ya sabawa kundin dokokin kasa ta 399, 392 da kuma 114 na kundin dokar kasa.

Da yake yanke hukuncin alkalin kotun Chief Magistrate Abdu Ladan laifuffukan da aka kama mai laifin dukkaninsu daurin shekaru uku uku ne, a don haka kotu ta yanke masa hukuncin wata tara a gidan kaso. 

Daga kamfanin dillancin labarai na kasa NAN

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *