Gwamnatin Jihar Katsina Ta Zabtare Kudin Takardar mallakar filaye  

Gwamnatin Jihar Katsina Ta Zabtare Kudin Takardar mallakar filaye  

Gwamnatin Jihar Katsina Ta Zabtare Kudin Takardar mallakar filaye  

0
0

Gwamnatin jihar Katsina ta fitar da bayanin zabge kudaden malakar kadarori (C of O) a duk fadin jihar.

Kwamishinan Kasa da Sufiyo na jihar Abubakar Sada Ilu ya bayyana haka a lokacin da tawagar hukumar ta kai ziyara a fadar mai martaba Sarkin Katsina, inda ya bayyana cewa wannan shi ne matakin da aka fara dauka kenan wajen mallakar kasa da muhalli.

Ya kara da cewa a da mutane sai sun sha dan karen wahala da kudi wajen akalla naira 200,000 wajen neman izinin C of O inda yanzun muka yi gyara a kan dokar ,mutane a cikin tsohon birnin Katsina za su mallaki takardar cikin sauki da sauri a kan naira 5000 , wadanda ke a cikin sabuwannin unguwanni kuma za su iya mallakar nasu a kan naira 25,000 kacal.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *