Rubutun da Danjuma Katsina yayi kan Hon. Mansur Ali da ya jefa shi a hannun Yan Sanda (Karanta)

Rubutun da Danjuma Katsina yayi kan Hon. Mansur Ali da ya jefa shi a hannun Yan Sanda (Karanta)

Rubutun da Danjuma Katsina yayi kan Hon. Mansur Ali da ya jefa shi a hannun Yan Sanda (Karanta)

0
0

BINCIKE NA MUSAMMAN; MATSAYIN GWAMNAN KATSINA DA ZABEN CIKE GURBIN MASHI/DUTSI DA AKAYI. WANDA AKA RANTSAR DA MANSUR ALI MASHI

Daga Danjuma Katsina.

Na saba yin bincike na musamman in kuma yi  rubutu  akai.wannan rubutu  yana daga  cikin wadanda  na saba yi. Wata    shaida  da  akayi  wa  GWamnan  Katsina Aminu  Bello  masari itace  gwamna ne  day a bai  yarda da  a  cutar  da al umma ba. bai  kuma yarda  da  dibar  dukiyar gwamnati  ba.

Gwamna ne  da akayi  shaida  yake  son barin  tarihi.da  kuma kyakykyawan sakamako  gaban Allah. Ko  kana kinsa in ka matsa  kusa  dashi. Sai ka fahimce shi  ka kuma  tausaya  masa.

Zaben  fitar  da dan takara.  wanda  akayi na cike gurbin dan majalisar wakilai na  mashi/Dutsi,  ya  baiwa  kowa  mamakin yadda Mansur Ali mashi  ya  canye . duk  kuwa  da cewa  Mansur  yana fuskantar  tuhume  tuhume  daban daban a kotu na .duk  wadanda  suka  shafi  zargin   kudade  na miliyoyin nairori.

Masu mamakin  sun rika bada misalin a gwamnatocin  baya..in akwai  zargi  irin wannan muraran na  kotuna akan kudade  akan ka.sukan hana ka takara.  Su  baka matsayin siyasa.na cikin gwamnati  jaha ko tarayya.

Wannan  cece kuce  na gefe  ya sanya na fara   binciken  me yasa  Gwamnan Katsina ya marawa  dora  Mansur  Ali  mashi  yayi  takarar  dan majalisa..da  kuma  tsayawa  kai  da fata  sai yayi nasara?

Binciken  da  na tabbar  cewa  Dallatun Katsina  bai  wani  tsaya  kai da  fata  sai  Mansur  Ali ba.Amma  abin da  kawai  yayi  ya bar  wa  jam iyya da  wasu  jami an  gwamnatin sa.amanar   da  aje  ayi  adalci a  zaben  fidda  dan  takara  a  zaben  cike  gurbin.

Koda  ya bayar  da  Wannan Amanar, sai  ya kyale  su  suyi  aikin  da  ya basu  tsakaninsu  da  Allah.bincike na,y a  tabbatar mani  in ma har anyi  wani  ba dai  dai  ba.a  zaben fitar da  gwani to  bada  ruwan  gwamna ba. gwamna  baya  kasar  akayi  zaben,  sai  dai  aka shaida masa  cewa Mansur  Ali  yaci   zabe.

Wani na kusa da gwamna ya  shaida  mani  cewa  a kwai  lokacin da gwamna yaje  Daura  bayan ya  dawo  yake korafin cewar.akan hanya  babu  inda  yaga  foster  din dan takarar  APC   a koina .tun daga  dutsi  har  mashi.amma ga  posta  da alluna na dan takarar  adawa.

Duk  wanda yaje ko  ya kalli  kaddamar  da  dan takarar  APC  a  dutsi..gwamna  a jawabinsa bai kirara  dan takararsu  ba.amma yayi  misalai  ne  da ayyukan alhairai na gwamnatin APC da  yadda  ta  ke cika  duk alkawullan da ta dauka. Sannan  ya  nemi  jama a su  jefawa  dan takarar  da  jam iyyarsu  ta tsaida.

Haka kuma  duk  yawon takarar  da  dan takarar  APC   ya rika yi..ba wani karsashin  alamar  yana tare  da gwamnati.  Wanda alama ce  na akwai  wata  a  kasa  a fadar  gwamnati.

Bincike  na  ya  tabbatar  da cewa.gwamnan Katsina  ya goyi  bayan  takarar  ne  dari  bisa  dari  don biyayya ga matsayar  jam iyyarsa  ta  APC  da  kuma tsayawa  tsayin daka  kar  aji  kunya  a  jihar  shugaban kasa a kuma   yankin da shugaban ya fito.

Gwamnan ya yi  wata Magana a wani  taro da yan APC  Daga karamar  hukumar Rimi suka kai  masa  ziyara…yace  a siyasa  dole  ka  dage  ka  tabbatar  da  cewa   dan jam iyyarka   shine  yayi nasara  a  zabe..koda  kuwa  baka  son  sa  baka  gamsu  dashi  ba.  domin  in dan wata  jam iyya ka bari  yaci  bakin  cikin  da   zaka  fuskanta  yana  da  munin  gaske,

Wani  lamari  da  manazarta  ke  tsokaci  a binciken nawa  shine.yadda  duk   rubuce  rubucen da  jaridu  suka  yi  da  taron manema  labarai  da  aka  gabatar  kashi  daban a kan   zaben  ..gwamantin  Katsina  da  jam iyyar  APC  basu  ce  uffan ba..wanda  kamar  alamar  kodai  .sun  kyale  dan  majalisar  da yaci  zaben yak are kansa da zabensa..ko kuma  ko  in  kula.

Bincike  nay a  tabbatar  mani  gwamnan Katsina ..baya  da  hannu  kowane mummunan  zargi  a  zaben   da  ya fito  da Mansur  Ali mashi. Binciken na  zargi  wasu  ne  a  jami an  gwamnati  da  kuma jam iyya   suka yi  sukayi   ruwa  da  tsaki.  Amma a ra  ayin    gwamna yaso a  tsaida mutum  wanda  baya  da kowace irin   LAM ,A   a  tare  dashi.

Danjuma Katsina..08035904408. twitter  @danjuma Katsina.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *