Madalla: Gwamnatin jihar Katsina zata gina matatar bakin mai a garin MASHI

Madalla: Gwamnatin jihar Katsina zata gina matatar bakin mai a garin MASHI

Madalla: Gwamnatin jihar Katsina zata gina matatar bakin mai a garin MASHI

0
0

Gwamnatin jihar Katsina ta ce zata samar da matatar bakin mai a karamar hukumar Mashi dake jihar. Alhaji Abubakar Yusuf, kwamishinan kasuwanci, masanaántu da kuma yawon shakatawa, ya bayyana hakan a ranar Lahadi, 30 ga watan Yuli a lokacin kaddamar da wani aiki a kamfaninb Kankia Metals Works.

Ya bayyana cewa an rigada an amince da filin da aka nema domin wannan.

Yusuf ya bayyana cewa dukkan masu ruwa da tsaki na aiki tukuru domin ganin an cimma wannan kudiri na masanaántu mai muhimmanci.

Gwamnatin jihar Katsina zata samar da matatar mai Ya bayyana cewa jihar na da albarkatun kasa da zai sa su cimma wannan cigaba a fannin noma, maádinai, gine-gine da ma harkar kasuwanci baki daya.

Kwamishian ya bayyana cewa kudirin samar da maáikatar da gwamnati me ci keyi zai taimaka gurin samar da ayyukan yi, kudaden shiga da kuma samar da arziki, sannan kuma zai taimaka gurin kawo ci gaban chanji ga jihar.

Kwamishina ya kara da cewa hakan zai rage talauci da kuma kawo ci gaba ga alúmman jihar. Kwamishinan ya kuma bayyana cewa gwamnati ta bayar da fili ga SASCO Limited domin samar da maáikatar nama a karamar hukumar Mai’adua.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *