PDP na nan a raye kuma zata karbi mulki a Katsina- inji Tata

PDP na nan a raye kuma zata karbi mulki a Katsina- inji Tata

PDP na nan a raye kuma zata karbi mulki a Katsina- inji Tata

0
0

Daga Sadiq Tijjani Bakori

Mai neman tsayawa takarar Gwamnan Jihar Katsina a inuwar Jam’iyyar PDP, Alhaji Umar Abdu Tsauri wanda aka fi sani da TATA ya ce, jam’iyyar shi ta PDP na nan a raye, kuma za ta karbi mulki daga hannun wad’anda ya kira da y’an kwanta-kwanta. Wannan ya biyo bayan taron bude ofishin shiyya da PDP ta gabatar a garin Funtua a ranar lahadin da ta gabata.

A wata sanarwa da Shugaban kungiyar Tata Social media forum, Abdul Danja ya fitar a shafinshi na  kafar sadarwa ta Facebook, Tata ya nuna matukar farinciki da godiya bisa tarbar karamci da ya samu a wajen taron, kuma ya yi addu’ar Allah ya saka wa wannan yanki da alheri.

Tata ya ce” Ina mai matukar godiya da bangajiya ga daukacin al’ummar wannan yanki mai albarka bisa gudunmuwa, karramawa  da kaunar da suka nuna mini da kuma jam’iyyata ta PDP a taron bude ofishi na jamiyya da muka gudanar a ranar lahadi…”.

Tata ya kara da cewa, taron da suka gudanar a garin Funtua wata yar manuniya ce cewa, jamiyyar PDP ta na nan a raye kuma ta d’auko hanyar karbar mulki ga wad’anda ya kira y’an kwanta-kwanta. ”Tabbas wannan taro ya nuna cewa jam’iyyar PDP ta na nan a raye kuma cikin yardar Allah ta dauko matakin karbar Katsina daga  yan kwanta kwanta.”

Umar Tata ya kuma bayyana cewa yanzu babban muhimmin abu da ke gabansu, shi ne bud’e ofishin shiyya na garin Daura. Daga karshe ya yi jaje ga mutanensu na garin Matazu wad’anda suka rasa rayukansu sakamakon hatsarin mota da ya ritsa da su akan hanyarsu ta komawa gida daga wajen taron.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *