Wanene Arc. Kebram a siyasance?

Wanene Arc. Kebram a siyasance?

Wanene Arc. Kebram a siyasance?

0
0

Katsina Post Hausa ta yi waiwayen baya na bin diddikin rawar da Arc. Kabir Ibrahim Faskari wanda wasu suka fi sani da Kebram, kuma shugaban kungiyar manoman Nijeriya ‘AFAN’ , ya taka a fannoni daban daban na rayuwar siyasa musamman tun lokacin da jam’iyyar gwamnati mai ci a yanzun take cikin sahun jam’iyyun adawa a Nijeriya.

A binciken da Katsina Post ta yi a kan gudunmuwar da Arc. Kebram ya taka, wajen kafa gwamnati mai ci tun daga matakin Tarayya har zuwa jihohi a iya cewa Kebram ya kai gwarzo kuma cikakken dan amana a cikin wadanda suka yi tsayuwa irin ta daka har jam’iyyar APC ta kai inda ta kai a wannan iskar dake kadawa.

Kadan daga cikin wasu muhimman gudunmuwar da ya bayar a cikin jam’iyyar APC ta kai ga samun nasara a zaben da ya gabata sun hada da;

Shi ne ya yi shugaban zaben fitar da gwani na dan takarar Gwamna a jihar Jigawa da aka yi a 2014 , wanda ya bayya Gwamna Badaru a matsayin sahihin dan takarar Gwamnan Jigawa a jam’iyyar APC, da ya zama Gwamna bayan lashe zaben 2015. (Chairman, APC Congress in Jigawa State 2014)

Yana cikin mambobin kwamitin sha’anin kudi na yakin neman zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2015. (Member, GMB Finance Campaign Committee 2015)

Babban mamba ne a cikin kwamitin tsarawa da kula da yadda zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari zai wakana a ga baki dayan jihar Katsina a 2015 . (Member, GMB Campaign Committee on Election Planning & Monitoring in Charge of Katsina State Situation Room 2015)

Mamba kuma sakataren kwamitin kudi na yakin neman zaben Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari a 2015. (Member/Secretary Finance Committee, Masari Campaign 2015)

Mamba cikin kwamitin tsara sabon birnin Katsina a lokacin yakin neman zaben Masari a 2015.  (Member New Katsina City Committee, Masari Campaign 2015)

Mamba kuma sakataren kwamitin tsara yadda za a rantsar da zabebben Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari a 2015. (Member/Secretary Katsina State Gubernatorial Inauguration Planning Committee 2015)

Mamba kuma sakataren kwamitin  tallafin kayan azumi na 2015. (Member/Secretary Ramadan Assistance Committee 2015.)

Mamba kuma sakataren kwamitin  tsara yadda za a raba kayan tallafin azumi a 2015. (Member/Secretary Ramadan Assistance Distribution Monitoring Committee 2015.)

Matasan Faskari, sun mika wa Kebram akalar siyasar su

Baya ga wadanan abubuwan da Katsina Post ta wallafo Arc. Kabir Ibrahim yana taka muhimmiyar rawa wajen taimakawa da aljihunsa da shawarwarinsa domin ganin al’umma ta ginu tare da tsayuwa da kafafunta da bodaro da wani ba, musamman wajen kafa kamfanoni da masana’antu domin rage yawan masu zaman banza a fadin jihar.

Ko a kwanakin baya Katsina Post ta wallafo labarin sadaukar da katafaren gidansa na Faskari da ya yi domin ganin Makarantar diyan Sojoji da aka samu a mahaifar tasa ya tsayuwa da gindin zamansa har zuwa lokacin da gwamnatin jihar Katsina za ta gina masu matsugunin dindindin.

Za mu ci gaba da zakulo wasu humimman al’amura da ya taka a rasuwarsa don ci gaban al’umma nan gaba

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *