Riga-kafin kora: Muttaqa Rabe zai horas da malaman Katsina dubarun cin jarabawa

Riga-kafin kora: Muttaqa Rabe zai horas da malaman Katsina dubarun cin jarabawa

Riga-kafin kora: Muttaqa Rabe zai horas da malaman Katsina dubarun cin jarabawa

0
0

Wata kungiyar da ba ta gwamnati ba a karkashin jagorancin shugaban ta fitaccen dan siyasa kuma na hannun damar tsohon shugaban kasa marigayi Alhaji Ummaru Musa Yar’adua, Injiniya Muttaqa Rabe mai suna Pleasant Library and Book Club , PLBC a turance ta shirya tsaf domin bada horo na musamman ga daukacin malaman makaranta (primary & secondry) kimanin sama da dubu talatin da muke dasu a fadin jahar Katsina.

Horon zai wakana ne a dukkanin tsoffin kananan hukomi bakwai da muke dasu (Funtua, Katsina, Daura, Mani, Kankia, Dutsinma da Malumfashi).

Shehunnan malaman Ilmi daga Jami’oi da kuma sauran makarantun Ilmi mai zurfi zasu gabatar da wannan horo, domin tanadi da kuma shiryar da malamai ga ire-ire hanyoyoyin amsa tambayoyi (teacher competency test) domin kaucewa matsalolin faduwan jarrabawa da ka iya tasowa ga malaman Jahar Katsina.

Haka ma dai kungiyar ta bayyana cewa horon kyauta ne.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *