CANJIN RAYUWA [Kashi na Hudu] Tare da Halima K. Mashi (Shafi na 46 – 50)

CANJIN RAYUWA [Kashi na Hudu] Tare da Halima K. Mashi (Shafi na 46 – 50)

Daukar Nauyi: Funtua Mandate Promoters

CANJIN RAYUWA [Kashi na Hudu] Tare da Halima K. Mashi (Shafi na 46 – 50)

0
0

Shiru yayi tamkar ruwa ya cinyeshi, nazarin zantukanta yakeyi. ya dan qara matsowa kusa da ita, ya tausasa muryarsa qwarai. “Yi haquri khadija, inda zaki bani labarin soyayyarku da khalil, zanso ji. Ta dubeshi, fuska cike da hawaye, ba zan iya ba.

Banason in tuna da komai game da labarin. Abinda kawai ba zan manta ba shine tsananin son da khalil yayi min. Haka kuma ba zan manta da yadda nayi ta wulaqantashi ba. Salon son da khalil yake nunamin ta hanyar chatting dina a facebook, wtsapp, da sauran irin wadannan kafofin, tun bana bashi amsa, har dadin kalamansa suka sa na soma bashi amsa, duk da ni ba amsa mai dadi nake bashi ba. Ranar dana soma son khalil, yawun bakina na watsa masa fa a cikin mutane. Amma kasan me yayi?

Ismail yace, a’a tace,, ga mamakina sai naga kurum yasa harshensa ya lashe yawuna daya sauka kan kafadarsa, sannan yayi murmushi, “komai naki inason sa. In na bari yawunki ya sauka a qasa nan, nayi muguwar asara. Ta soma sabon kuka, wannan kadan ne daga irin son da khalil yayi min. Ismail yace, shikenan kiyi haquri. Allah ya yafe masa tace Ameen. Yayi shiru. Yasan ynxun yaya Amina ta rage mashi hanya da tayi wannan jihadin, na yiwa mimi nasiha harta fahimci cewa tayiwa iyayenta laifi, ba zai wahalar shawo kanta don zuwa basu haquri ba.

Amman wannan ba ynxun ba. Ya dubeta, har ynxun tana share hawaye. Nace kiyi haquri. Kuma zaki iya samun wanda yafi khalil sonki, kema kuma ki soshi fiye da son da kk yiwa khalil din. Ya girgiza kai, Da wuya hakan ta kasance, nina kulle babin so, koda na samu mai sona, ni kam na tabbata ba zan soshi ba. Ismail yayi murmushin yaqe, to yaya batun islamiyya fa? Mimi tace ina daukan karatuna a gurin yaya Amina. yayi dariya, shikenan Allah ya biyata da aljannarsa.

Ya miqe ya dauko jakar tsarabarsu, ya dawo ya zauna bakin gado, “zo ki za6i abinda kk so cikin tsarabata. Ta matso. Ya dauko jakar ya dora ta saman Gadon. Ya soma ciro jallabiya, pink mai ratsin baqi, sai jarta, itama mai ratsin baqi, sai takalma da riga da wando kala biyu, duk ire-iren wadanda take sawa. Ta tsaya tana kallonshi, sbd ta san tsadar kayan. Kafin tace wani abu, sai  kurum taga ya ciro wani gwangwani a can qarshen jakar, ya miqo mata. Da sauri ta kar6a sbd irin turarenta ne. Ta soma karanta rubutun jiki a fili tace, “tabbas shine” ta dago ta dubeshi, “siyan turarennan kayi? Yace eh,  siya miki nayi.

Tace ina ka samu kudi haka? Na ga kai din dalibi ne, kuma duk kayan nan suna da tsada, musamman wannan turaren? Yayi murmushi, “munyi aikin raba abinci ne ga mabuqata aka biyamu. Ta soma hawaye, ban ta6a tunanin zan qara amfani da wannan turaren ba. Nagode sosai. Ya tausasa murya don jin dadin sake burgeta. Karki damu khadija, nayi miki alqawarin in Allah ya buda min, zanyi miki gatan da yafi wanda kk ta6a shiga a fannin jin dadi.

Ta sa idanunta cikin nasa, “nasan zaka iya, domin duk abinda kayimin alqawari, ka cika. Ina ganin kimar ka sosai, ynxun saura abu daya ya rage. Ya zaro mata manyan idanunsa, me? Tayi shiru, gabanta yana faduwa. Yace karki damu ki fadamin, qila na manta ne. Ta sunkuyar da kai, “maganar rabuwarmu.” Gabansa yayi wani mugun faduwa. Dakin yayi tsit na wasu daqiqai kamar hudu. Maimakon yaci gaba da zancen, sai kawai yace, yau yau dale kuka karya ne a gidan nan? Yunwa nakeji.

Tace, ruwan Lipton ne da biredi. In zaka ci ina zaton akwai a flask. Yace zansha shayin, kinsan mu shine ma abin shanmu kowane lokaci. Ta miqe ta nufi kicin ya bita da kallo, tafiyarta ta dawo tamkar da, cikin nutsuwa da kamewa. Ta dauko filas din ta hado da kofi da cokali da kuma suga. Sai ledar bread din. Zuciyarta kuwa tambayar kanta takeyi menene dalilinsa na share zancen rabuwarsu? Yace, ba zanci bread ba. Na saba dana can da mukeci bashi da suga.

Ya miqe ya janyo jakarsa, ya zuba wani ganyen tea, ya zauna yana sha. Duk sukayi shiru, kowa da kalar tunaninsa.

Shi ba wai ba zai iya sakinta bane, amma tsoron sa kar ya saketa, ta sake guduwa. Ta katse masa tunani, “Wai meyasa ka share batun da kawo? Ya kalleta, “ba sharewa nayi ba. Khadija muna buqatar qarin lokaci ne. Kiyi haquri har in kammala karatu na.” Tace, zuwa yaushe? Ya dubeta da sauri, “kin samu wanda kk so ne? Itama cikin sauri ta kalleshi, “Allah ya kiyaye min, ni kam banason kowa. Nauyin ne nikeson a sauke min. Yayi murmushi baice komaiba. Sati biyun da Ismail sukayi a Nigeria sunyisu ne a cikin hidimar bikin Mahmud.

Babu yadda baiyi da Mimi ba akan taje gurin walimar bikin, amma taqi, dolensa ya haqura ya barta. Bayan kwana biyu da kammala bikin, suka soma shirin komawa madina. Ango da Amarya cikin dokin juna a ranar tafiyar, ko cikin jirgi tamkar su hadiye juna suna ta birge Ismail, wanda ya lumshe ido yana tuno hawayen Mimi da suke zuba lokacin da sukeyin sallama. Ya tuna tambayar da yayi mata. Khadija wannan kukan kuma na menene?

Ta girgiza kai, “nila ban san ko na menene ba. Ya ciro kyakkyawan hankici daga aljihunsa, sai qamshi yakeyi. “share hawayenki da wannan, sai in munyi waya kenan ko? Ya sauke ajiyar zuciya, tare da furzar da wani huci mai zafi. Yana kewar rabuwa da yarinyar. Yayi ta tuna huldarsuda kuma irin CANJIN RAYUWAR da Allah ya saukar mata. Allah yasa ya zama sanadin shiriyarta kenan.

Labarin data bashi na tsohon saurayinta, abinda ya fahimta da Mimi, ita mutum ce maison aso ta, aji da ita, a nuna mata tsantsan so a fili, sannan a fada mata kalaman tada hankali. A fili ya furta cewa ban iya wannan ba. Sai kuma Zainabu ta fado masa, ya tuna da zancan su da yaya Amina bisa ganin da yayi mata. Yaya tace, masa tana gidan mijinta, qila dai tazo duba su ne. Haka yayi ta tunane-tunane har Allah ya kaisu lfy.

Satin su Ismail daya da tafiya, yaya Amina ta haifi ‘yarta mace, aka sa mata Aishatu. Yaya tasha mamakin ganin ‘yan uwanta mata yadda suka zo mata barka harda suna, sa6anin da ba kowa ke zuwa mata barka ba bare suna. Inna kuwa zuwanta uku. Mimi kam ta takura sosai ranar suna, domin sam batason jama’a, kamar ta bar gidan  amma ba yadda zatayi, dole ta haqura.

Lokaci yana qhudewa kwanaki quna qarewa, yau gashi su Na’ima anyi arba’in. Ta matsu qwarai tabar gidan minister, domin ko abincin da zataci sai taje kicin da kanta ta kar6a. Hatta ‘yan aikin gidan sunsan batada wata kima, tunda a gabansu za’a zage ta tass. Don haka ko aiki tasa su basa yi mata.

Sannan ga gadara da yaron, kullum akayi masa wankan safe, za’a tafi dashi gefen kakarsa, sai yamma ko in ya buqaci Nono. Da ma mai wanka da shirya shi musamman aka dauko. Shi kuwa Abbas sai dai ta jiyo muryarsa daga can sasan. Bata damu ba don ita ynxun ya gama sire mata. Kwana arba’in da bakwai suka maida ta gidanta bayan an kafa mata dokoki da sharudda akan yaron, sai kace ba itace ta haifeshi ba. Lokacin ne ma ta samu zuwa gidansu yini. Kuka momy Nafisa ta tasa Na’ima tayi tayi, sbd baqi data qara akan nata, gashi duk tayi zuru-zuru, idanu sun shige.

Lokacin Alhaji bayanan Abuja, tace, bari dai yau dadynku ya dawo zan fada masa komai game da halin da kk ciki. Na gaji, gara komai zai faru, ya faru. Na’ima tace, yauwa momy don Allah  ki taimaka min. In ba haka ba, wata rana zakije ki dauko gawata a gidan Abbas. Har dare Na’ima tananan tana jiran dawowarsa. Sun zauna sun karanto masa komai game da halinda Na’ima take ciki. Yace sam qarya ne, domin ta jima tanason kashema Na’imar aurenta.

Su tashi su bashi guri. Ya kalli Na’ima, “karki daka ta mahaifiyarki, ki zauna dakinki shine cikar mutuncinki. Na’ima tace, Allah dady duk abinda kaji dinnan shine yake faruwa, yace kije zan bincika. Fitarta keda wuya, Alhaji Bashir ya kira layin Abbas. A tunanin Alhaji Bashir, Abbas da Na’ima duk daya ne agurinsa. Bayan sun gaisa, sai Alhaji Bashir yace, zantuka nakeji marasa dadi abakin Na’ima, tana fadamin wai bakwa zaman lfy tunda taje gidan.

Shine na kira ka inji menene gskyr zancen? Abbas yace e.. to kusan akwai hakan daddy. Alhaji Bashir yace, to menene dalilin hakan Abbas? Abbas babu kunya ko shayi, yace, gsky daddy ina matuqar qoqari gurin zama da Na’ima, sbd gsky ni na wai ina sonta bane sam, Mimi nake so. “kalaman sukazo ma Alhaji Bashir a bazata, ya kuma fassarasu da cin fuska.

Amma sai ya danne, yace, in banda abin Abbas abinda yayi Mimi aishi yayi Na’ima, dukkansu ‘ya’yana ne. Abbas yace, daddy Mimi fara ce mai aji. Na’ima baqa ce mai naci, amma aka dauki dauki Mimi aka ba wanda baisan darajata ba… “Dakata Abbas!

Alhaji ya katseshi, cikin zafin zuciya. Yaya inayi maka magana kanayi min wani shirme? Zancen Mimi ba naka bane, qanwarta ce matarka, kuma a kanta muke yin magana. Bakason ta shine baka fada ba tuntuni, sai ynxun da kuka soma samun qaruwa? Ynxun dai abinda nakeso dakai, in tana yi maka wani laifi ne to sanar dani, sai in tsawata mata ta daina. Abbas yace, nidai son da banayi mata shine kawai matsalarmu.

Alhaji Bashir yayi shiru, cikin Mamaki ya rasa me zaice, sai kawai yace, shikenan in ka samu lokaci kazo ina nemanka. Mamakin Abbas ne ya cika Alhajin, yadda yake magana cike da rashin ladabi. Kar dai ace yaronnan bashida tarbiyya. Sai kuma ya canza kiran wayarsa zuwa ga minista. Bayan sun gaisa, sai yace, ashe dama yaran nan zaman rashin jituwa sukeyi tun tuni? Minister yace, kamar yaya? Nan Alhaji ya kwashe komai ya fadawa minister har yadda suka yi ynxunnan.

Sai kawai yaji minister yasa dariya, tare da fadin, karka shiga zancen yarannan. Baya sonta, yaya akayi ta haihu? Ya kamata da kayi masa wannan tambayar, lokacin daya ke fada maka cewa baya sonta. Alhaji Bashir yace, neman mata da tace yanayi shine matsalar ai. Minister yasa wata dariyar. “kar ta damu da wannan, in dai ya sauke mata nata haqqin. Kasan yarannan ba’a rabasu da son nishadi.

Su kuwa mata, ai sune nishadin rayuwa. Kan Alhaji Bashir ya kulle, kenan ya daure ma dansa gindi yayi duk abinda yakeso, kuma bazai iya hanashi sa6ama Allah ba kenan? Minister ya katseshi da cewa, nayi zaton zakayi min magana akan hauhawar farashin man fetur ne? Alhaji Bashir yace, a’a ba wannan bane. Shi kenen saida safe mayi maganar kasuwanci, in Allah ya tashemu lfy, minister yace, Allah ya kaimu. Kada kasa kanka a damuwa game da batun wadannan yaran.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *