Ku kalli hotunan wanda ya lashe kyautar mafi muni a duniya karo na 5

Ku kalli hotunan wanda ya lashe kyautar mafi muni a duniya karo na 5

Daukar Nauyi: Funtua Mandate Promoters

Ku kalli hotunan wanda ya lashe kyautar mafi muni a duniya karo na 5

0
0
Wani mutum mai suna William Masvinu dan asalin kasar Zimbabwe ya sake lashe kambun wanda yafi kowa muni a karo na biyar a cikin karshen satin da ya gabata a yayin wani gagarumin taro da aka gudanar a can kasar dake cikin Afrika.
Shi dai William ya yi rashin sa’a a shekarar da ta gabata ne inda wani wanda ake kira Maison Sere ya kada shi a cikin wata gasar mai cike da sarkakkiya.
NAIJcom dai ta samu cewa a wannan karon dai kuma sai shi William din ya sake shiri inda ya lashe kyautar ya kuma samu kyautar kudin da suka kai dala dari 500 yayin da shi kuma wanda ya zo na biyu aka bashi dala dari 200.
Da yake zantawa da manema labarai kuma, Masvinu ya bayyana matukar jin dadin sa da ya lashe gasar a wannan karon inda kuma ya godewa dangin sa da mahaifan sa da ma dukkan masoyan sa.
Haka ma kuma ya bayyana kudurin sa ga yadda ake so ya shiga gasar wanda yafi muni a duniya sannan ya kuma bada tabbacin cewa zai lashe kambun.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *