Sakataren kasa na PDP: Zamfarawa ma sun ce sai Sanata Tsauri 

Sakataren kasa na PDP: Zamfarawa ma sun ce sai Sanata Tsauri 

Daukar Nauyi: Funtua Mandate Promoters

Sakataren kasa na PDP: Zamfarawa ma sun ce sai Sanata Tsauri 

0
0

Jim kadan da gama ganawa da yayan PDP na jahar Sokoto da jahar Kebbi sai tawagar dan takarar kujerar sakataran jam’iyyar adawa ta PDP na kasa baki daya Senata Umar Tsauri ta shilla zuwa Jihar Zamfara domin cigaba da sada zumunta tare da neman goyan bayan dukqnin mai alhakin jefa guria a matakin kasa baki dayq NATIONAL DELEGATE  da masu ruwa da tsaki kai uwa uba kuma sauran alumma magoya bayan babbar jamiyyar adawa mai dawa ta PDP na jahar Zamfara din a garin Gusau. 

Idan bamu mantaba uwar jamiyyar PDP ta shiyyar Arewa maso yammacin kasar nan sun tatauna akan mukaman da shiyar ta samu inda suka rabasu zuwa tsohuwar Kano, tsohuwar Kaduna da tsohuwar Sokoto.

Cikin ikon Allah sai tsohuwar Kaduna ta samu kujerar sakataran PDP ta kasa inda aka barma jahar Katsina ta duba da wata yarjejeniya dake tsakanin Katsina da Kaduna nayin karba karba, idan wannan jaha tayi tabama wannan Jaha, wanda jahar Kaduna ce tagama kujerar sakataran shirye shirye na kasa a yanzu .

Duk da haka wasu sun fito takara amma ba da yawun iyaye da masu fada aji na shiyar north west zone suke takarar ba.

Jahar Zamfara itama takara jadada cewa su basu karya alakawarin da’akayi na barma Sen Umar Ibrahim Tsauri CON, daga jahar Katsina takarar kamar yanda sauran jahohi suma suka aminta.

Shuwagaban PDP kuma jagoran tafiyar HON. Salisu Yusuf Majigiri addua yafara mikawa ammadadin tawagar akan hadarin da shugaban babbar jam’iyyar adawa ta PDP na kasa reshen jahar Zamfara yayi a yau. 

Inda yacigaba da nuna farin ciki da godiya abisa yanda aka tarbe su kuma aka nuna masu karamci na musamman tare da kara hasakaka waye Sen. Umar Ibrahim Tsauri a matsayin dan takarar da ake son yazama zababen sakataran pdp na kasa.

Haka kuma yayi karin bayani akan yanda takarar ta kasance tare da samuwar kujerar a jahar katsina har katsinawa suka taso gwanin su gaba domin sun san bazaya basu kunya ba inda ya rufe da cewa sunada tabacin sen tsauri zayayi aiki da jahar zamfara kafada da kafada kamar jahar shi ta katsina ba tare da nuna banbanci ba saboda haka su zabi sen tsauri domin ciyar da PDP Najeriya gaba .

Anashi jawabin shugaban babbar jqm’iyyar PDP na kasa reshen jahar Zamfara Hassan Nasiha wanda yasamu wakilcin sakaranshi sunce su masu biyaya ne. 

Sen. Umar Ibrahim Tsauri CON, galadima yandakan Katsina kuma dan takarar kujerar sakataran PDP na kasa kuma sakataran PDP na kasa da yardar alla godiya yakarayi a bisa karamaci da tarbar daakai mashi da tawagarshi hqnu biyu  inda yayi alkawarin mudun allah yakaishi gaci  to zaya kasance mai biyaya da daa ga  dukanin daftarin tsarin mulkin PDP sanan bazaya bada kunya ba zayayi aiki tukuru domin ciyar da jam’iyyar PDP gaba da tarayar Najeriya  gaba .

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *