Buhari ya ‘yantar da fursunoni 500 tare da basu makudan kudade a Kano

Buhari ya ‘yantar da fursunoni 500 tare da basu makudan kudade a Kano

Daukar Nauyi: Funtua Mandate Promoters

Buhari ya ‘yantar da fursunoni 500 tare da basu makudan kudade a Kano

0
1

 

A ziyarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke yi yau a Kano, ya ‘tartar da wasu fursunoni 500 tare da basu kyautar kudi su kama sana’a

Fussunonin sun hada da maza da mata dake gidan kaso na Kurmawa dake cikin birnin Kano

Wannan matakin rage yan gidan Yari a gidan kaso na daya daga cikin muhimman gwamnatin Buhari wajen rage wadanda ake tsare da su a gidan Yarin

A ziyarar sa ta ya kai fadar Sarkin Kano, shugaban kasar ya ce tun shigowarsa siyasa a 2003 ya ga abubuwa da dama a rayuwarsa

A lokacin da ya kai wa Sarkin Kano caffa a fadar tasa, Buhari ya ce akwai bambamnce-bambance masu dumbin yawa tsakanin mulkin soji da na farar hula.

Ya ce ” A lokacin da ina shugaban kasa a mulkin soji, na kama mutane da dama na kuma tsare mutane da dama da aka kama da cin hanci da rashawa, amma daga karshe nima kaina na kare a gidan yarin.

Ya kuma koka a kan yadda Nijeriya ta samu makudan kudade tun daga 1999 zuwa 2014 , amma abin takaici ba wanda zai iya nuna inda kudaden suka yi layar zana.

Comment(1)

  1. Masha Allah, Allah ya sa kwalliya ta biya kudin sabilu. Allah ya bashi ikon sauke nauyin da Allah ya dora masa ameen.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *