Kul kukaje tarbar Buhari a Kano – Kwankwaso ya gargadi magoya bayan sa

Kul kukaje tarbar Buhari a Kano – Kwankwaso ya gargadi magoya bayan sa

Daukar Nauyi: Funtua Mandate Promoters

Kul kukaje tarbar Buhari a Kano – Kwankwaso ya gargadi magoya bayan sa

0
0
Labaran dake yawo a yanzu haka a kafafen sadarwa na zamani musamman ma a arewacin Najeriya na nuni ne da cewa tsohon Gwamnan jihar Kano kuma Sanata a yanzu, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya bukaci daukacin magoya bayan sa da su kauracewa dukkan inda shugaba Buhari zai je a yayin ziyarar sa zuwa Kano.
Sanarwar dai da ake zargin cewa ta fito ne daga wasu makusantan tsohon Gwamnan ta bayar da dalilin daukar wannan matakin ne da cewa wasu bata-gari suna nan suna shirin tayar da tarzoma a wuraren da nufin batawa jagoran tafiyar suna.
Mun samu daga NAIJcom dai cewa haka ma kuma sanarwar ta bayar da hakuri ga daukacin mabiyan nata musamman ma wadanda wannan umurnin ba zai yi wa dadi ba da su zauna a gida kasantuwar anyi hakan ne domin tsaron lafiyar su da mutunci.
Mai karatu zai iya tuna cewa shugaba Buhari ya shirya zuwa jihar ta Kano a wata ziyarar kwana biyu tun daga yau Laraba har zuwa Juma’a na wannan satin da muke ciki.
A yayin ziyarar ta sa dai ana sa ran shugaban kasar zai kaddamar da wasu muhimman manyan ayyukan da gwamanan jihar ya aiwatar.

 

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *