Katsina: Yadda ‘yan sanda suka cafke wata mata tana kokarin sayar da ‘ya’yan ta Naira 350,000

Katsina: Yadda ‘yan sanda suka cafke wata mata tana kokarin sayar da ‘ya’yan ta Naira 350,000

Daukar Nauyi: Funtua Mandate Promoters

Katsina: Yadda ‘yan sanda suka cafke wata mata tana kokarin sayar da ‘ya’yan ta Naira 350,000

0
0

Wata mata mai suna Salima Lawal yar shekaru 30 a duniya ta shiga hannun jami’an rundunar ‘yan sandan Najeriya a garin Marabar Kankara da ke karamar hukumar Malumfashi, Jihar Katsina a yayinda take yunkurin siyar da tagwayen yaran ta a kan kudi naira 350,000.

Kwamishinan rundunar ‘yan sanda na Jihar ta Katsina, Been Gwana ne ya tabbatar da afkuwar lamarin a lokacin da yake jawabi ga manema labarai a ranar Laraba a garin Katsina.

Benson Gwana din haka zalika ya bayyana cewa Uwar jariran ta kammala cinikin yadda zata sayar da tagwayen ga wani bawan Allah a garin Ruwan Godiya da ke karamar hukumar Faskari a ranar 2 ga watan Disamba yayinda jam’an ‘yan sanda suka samu nasarar kamata.

Kwamishinan dai ya bayyana cewa dukkan tagwayen jinsin mata ne sannan kuma duka-duka kwanan su 30 a duniya sannan kuma yace rundunar tana cigaba da gudanar da bincike a kan lamarin kana daga baya za’a gurfanar da Salima Lawal gaban kotu domin ta fuskanci shari’ah.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *