Masari zai gina irin makarantar da ‘ya’yansa ke karatu a Funtua

Masari zai gina irin makarantar da ‘ya’yansa ke karatu a Funtua

Daukar Nauyi: Funtua Mandate Promoters

Masari zai gina irin makarantar da ‘ya’yansa ke karatu a Funtua

0
0

Gwamnan jihar katsina Aminu bello masari ya amince da gina sabuwar makarantar Family Support irin wadda ya’yansa ke karatu a cikin garin Katsina, zai gina wata a yankin Funtua  zone.

Gwamnan ya fadi hakane alokacin da shuwagabannin uwayen dalibai tare da malaman na Family  Support da suka kawo mashi ziyara a gidan gwamnatin jihar katsina.

Alhaji Salisu Isiyaku shi ne ya jagoranci wannan tawaga a gidan gwamnatin inda ya yabi gwamnatin APC da cewa tun bayan kafuwar makarantar nan shekara 17 data wuce lokacin da marganyi colonel chamah ya assasa makarantar babu wata gwamnati da ta kula da harkar makarantar sai wannan gwamnati.

Gwamna masari yatabbatar masu da cewa tuni gwamnati tasama makarantar fili a funtuwar, inda kuma yace tunda akwai makarantar a katsina dakuma Daura itama funtua yakamata asamamata.

Gwamnan yace aikin zai kunshi gina katafaran azuzuwa guda 8, sannan da gina manyan dakunan karatu na physic, chemistry dakuma biology.

Gwamanan yakara dacewa zasu gina da za’a ajiye na’ura mai kwakwalwa tare da sa abun zama guda 50.

Haka zalika gwamnan yakara dacewa gwamnatin zata gina dakin karatu Wanda za’a sa na’urori masu kwakwala.

Sauran sun hada da sayen mota Mai kujera 18 tare da Samar da ingattacciyar hanyar da zata kaika makarantar, dakuma gina dakunan kwana na masu bautar kasa.

Abu Aminu, Katsina Post.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *