Matar aure da mijinta: ‘Juna biyun dake cikina ba naka bane’

Matar aure da mijinta: ‘Juna biyun dake cikina ba naka bane’

Daukar Nauyi: Funtua Mandate Promoters

Matar aure da mijinta: ‘Juna biyun dake cikina ba naka bane’

0
0

Wata karamar kotu dake Ake, Abeokuta cikin jihar Ogun na ci gaba da tafka shari’a tsakanin wasu ma’aurata , inda matar ta ce in ta haihu ba za ta ba mijin dan ba saboda ba nasa bane , kamar yadda Daily Trust ta rawaito.

Matar dai mai suna Kudirat Babatunde, ta ce sam cikin dake gare ta ba na tsohon mijinta da suka rabu Kamoru Babatunde ne ,don haka ko ta haihu ba za ta bashi dan cikin ba.

Mijin nata dai Kamoru ya maka matar tasa da suka rabu bayan sun sami yaya hudu da ita, Toheed mai shekaru 11; saiyYusuff mai shekaru 8; da Quyum mai shekaru 6; sai kuma Segun mai shekaru 4, tare da cikin wata uku a lokacin da suka rabu, yanzun kuma ya kai wata 7 amma matar ta kekeshe kasa ta ce sam ciki dai ba nashi bane kuma ba za ta bashi dan ba in ta haihu.

Ita kuwa a nata martanin a gaban kotu, matar ta ce mijin nata baya bata abincike da sauran abubuwan dawainiyar gida, ga dukanta da yake yi, bayan sun rabu ta yi kawance da wani saurayinta, kuma har ciki ya shiga tsakaninsu, saboda haka ita kadai ta san uban dan da za ta haifo amma ba na tsohon mijin nata bane.

Daga karshe dai Alkalin kotun Chief O.O. Akande, ya basu damar shirya kansu tare da gargadar matar a kan kar ta sake ta yanke wane mataki a kan cikin nata har sai kotu ta yi hukunci a kai, sannan ya dage shari’ar zuwa 7 ga watan Maris 2018.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *