Katsina: Rikici ya barke a tsakanin mawakan APC bayan karbar N13 miliyan daga Gwamna Masari

Katsina: Rikici ya barke a tsakanin mawakan APC bayan karbar N13 miliyan daga Gwamna Masari

Katsina: Rikici ya barke a tsakanin mawakan APC bayan karbar N13 miliyan daga Gwamna Masari

0
1

Daga ISAH BAWA DORO (Mujallar Fim)

Gwamnan Jihar Katsina Rt. Honourable Aminu Bello Masari ya ba wata kungiyar mawakan APC Naira Miliyan 5 a lokacin da suka kai masa ziyara. Kungiyar mai suna `Masari Modern Singers Association` sabuwar kungiya ce wadda wasu daga cikin mawakan APC na jihar Katsina suka kirkire ta wata uku da ya gabata.

‘Yan kungiyar sun ziyarci gwamnan jihar a daren ranar asabar, 28 ga watan satumba 2017 a gidan gwamnatin Jihar Katsina. Bayan sun gaisa, Kungiyar Mawakan sun bayyana wa gwamnan kudirin su na tafiya tare da gwamnatin sa da kuma bashi gudummuwa dari dari bisa dari. Inda nan take bayan sun gama ganawa da shi yasa aka basu Naira Miliyan biyar kafin su baro gidan gwamnatin.

Tun a cikin daren ba a kwana ba aka wuce gidan daya daga cikin ‘yan kungiyar Abdullahi Muhammad (Boda) wanda a cikin falon gidan sa ne aka raba kudin kowa ya kwashi rabon sa. Mawakan wadanda akalla za su kai su goma 15 ne kai masa ziyara, inda wajen raba kudin aka yi rabon zakkar baban gwari, ya yin da wasu suka tashi da Naira dubu dari uku da hamsin-hamsin, wasu kuma Naira dubu dari biyar-biyar suka kwasa, su kuma matan da aka tafi da su da yake mace biyu ce kowace an bata Naira dubu 100.

Mawakan da suka kai ziyarar sun hada da: Ukashat Ajuba, Salisu Arabi, Abdu Boda, Kabiru Siko, Lawal Usman, Adamu Ba burki, Ghali T. Yusuf, Ali Show, Shehu Opera, Musty Opera, Dahiru Asas, Zainab Asas, A’sha Funtua.

Tuni dai wasu daga cikin mawakan suka canza sabbin wayoyi, ya yin da wani daga cikin su ma ya sayi sabuwar wayar dubu 180, wani kuma dabara ya yi ya sayi fili a wani kauye a gefen Katsina, wasu kuma sun sayi Motoci, a gefe guda kuma wasu suka gyara motocin su da suka lalace. Wata majiya ma ta tabbatar mana wasu na da niyyar kara aure cikin kudin da suka samu.

Ba a fi wata daya da ba su kudin ba, Mawakan sun sake komawa wurin gwamnan na jihar Katsina cikin satin karshe na watan Nuwamba, inda gwamnan ya kara basu wasu kudin, wanda wata Majiya ta ce miliyan 8 ne gwamnan ya basu, da zummar za su bude sutudiyo na kungiyar, wanda tuni dai aiki ya kankama har sun sayo kayan sutudiyo inda suka kama wani shago a hanyar Nagogo Road, kusa da ofishin Human Right GRA Katsina su ka yi masa fentin APC.

Wakilin majiyar mu ya yi kokarin jin ta bakin shugaban kungiyar Ukashat Ajuba tun a lokacin da suka kai wa Gwamnan ziyarar farko, a kan ya yi masa karin bayani game da kungiyar da kuma manufofin ta, da abin da ta kunsa da kuma batun ziyarar su gidan gwamnati.

Sai dai ya ce masa shi bai da halin yin magana a kan wannan al’amari har sai ya tuntubi sakataren sa mai suna Salisu Arabi ka fin ya yi magana. Wakilin na mu ya yi iya bakin kokarin sa wajen tuntubar Salisu Arabi wanda shi ne sakatare na kungiyar, amma shi ma ya ce wa wakilin na mu a saurare shi zai neme shi nan bada dadewa ba. Saboda har yanzu ba su gama shirye-shirye game da kungiyar ba.

Kwatsam sai kuma mujallar fim ta samu labarin cewa kungiyar mawakan Gwamnan sun zauna wani taro, inda aka tashi baram-baram sakamakon musayar yawu da aka yi tsakanin Abdu Boda da kuma Sakataren kungiyar Salisu Arabi a wurin taron, Majiyar ta tabbatar mana cewa ana cikin taron ne akai ta hayaniya tsakanin Abdu Boda da Salisu Arabi kowa ya watse ba tare da an rufe taron da addu’a ba, Majiyar ta mu ta kara tabbatar mana da cewa tuni dai shuwagabannin kungiyar suka fitar da Abdu Boda da kuma wani mawaki mai suna Ghali T. Yusuf daga kungiyar, inda wasu suke ganin Musayar yawun da Boda ya yi da Salisu Arabi shi ne dalilin da yasa suka fitar da shi daga kungiyar.

inda kuma wasu ke cewa ai Abdu Boda da Ghali T. Yusuf su ‘yan tafiyar Atiku Abubakar ne duniya ma ta san haka, saboda har taro sun shirya a Katsina game da nuna goyon bayan su ga Atiku Abubakar, wanda kuma a yanzu Atiku din ya canza sheka daga jam’iyyar Apc zuwa jam’iyar PDP wanda ana ganin wannan dalilin ne yasa aka cire su tunda dai kungiyar mawakan Masari ce, shi kuma Masari dan APC ne.

Wakilin majiyar mu dai ya tuntubi Abdu Boda game da Cacar bakin da aka ce sun yi tsakanin sa da Salisu Arabi, da kuma batun fitar da shi daga kungiyar da aka ce an yi, sai Boda ya ce: ” Bari na gaya maka abin da ya faru, magana ce ake yi muna cikin meeting sai na ga an dauko maganar mawaka wadanda ba a ba wani abu ba a wancan lokacin.

Shi kuma Salisu Arabi ya ce sun kirashi suna ta zagin shi, na tambaye shi ba wannan maganar ta kawo mu ba, maganar an zage ka dole a zage ka, kuma ba kai ka bada kudin nan ba gwamna ya bada kuma ga wadanda ya ba. Kuma wannan ba wasu kudin kirki ba ne wadanda za a yi ta magana har wani ya bata rai. Na ce masa ka janye wannan maganar ka kawo abin da ya faru don mu gama meeting din nan mu yi tafiyar mu, ka ji abin da ya faru.

Sannan na biyu shi Salisu Arabi bai isa ya yi fada da ni ba, ba fada zai yi dani ba, ya ji haushin abin da na gaya ma shi, shi ne da ya tashi yake cewa bai kamata na yi masa haka ba, sai ya tashi aka d’aga meeting din daga wannan ranar, ka ji abin da ya faru”.

Game da batun fidda su kungiyar da aka ce an yi sai Boda ya ce: ” To, waye zai fidda mu? waye gwamnan a cikin su? wa ya hadani da gwamnan daga cikin su? wa ya san ina muka hadu? Abin da za ka duba kenan, ai kungiyar ba ta shi ba ce, kungiyar gwamna aka ce kai da kan ka sai ka yi wa kan ka hukunci.

Har zuwa kammala wannan rahoton Salisu Arabi bai tuntubi wakilin majiyar mu ba kamar yadda ya ce zai yi masa masa bayani  game da abin da ya shafi kungiyar, sannan ya kirashi ta waya don ji abin da ya hada su cacar baki tsakanin sa da Abdu Boda, amma bai dauki wayar sa ba.

Comment(1)

  1. Hmm gaskiya abun kunya baya karewa aduniya, mutane na fada saboda yan kudi kanana, domin mawaki kamar Audi boda da idon yayi wasa a kasar Niger zai iya samun wadannan kudin da aka basu, ni shaida ne kan irin samayyar da Audu ke samu, domin Audu yayi fim agidana ya Saida shi fiye da miliyan biyar, ni banga dalili Audu boda zai shiga wata kungiya ba da ta wuce kannywood, saboda haka ina ba alh Audu boda shawara yatsaya matsayinsa domin ya wuce shiga wata kungiya da bata wuce matakin jiha ba. domin kannywood ta fi matakin Nigeria ba dama Africa. Ina mai ba audu boda shawara da yabar zancen wata kungiya mai iya matakin jiha.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *