Kannywood Post: “Ni ba cikakkiyar budurwa ba ce amma ban taba aure ba” – Rahama Sadau

Kannywood Post: “Ni ba cikakkiyar budurwa ba ce amma ban taba aure ba” – Rahama Sadau

Kannywood Post: “Ni ba cikakkiyar budurwa ba ce amma ban taba aure ba” – Rahama Sadau

0
3

Rahotanni sun kawo cewa korarriyar jarumar kamfanin shirya fina-fina hausa na Kannywood, Rahama Sadau ta bai wa masoyanta damar yi mata tambaya a shafinta na Instagram.

Wannan dama da jarumar ta bayar ya sa masoya na ta tururuwa wajen yi mata wasu tambayoyi da suka shafi rayuwarta.

Duk da cewa wasu daga cikin tambayoyin sun kasance masu nauyi jarumar tayi kokarin baar da amshoshin day a gamsar da masu yin tambayar ba tare da ta nuna bacin rai kan tambayar ba.

“Ni ba cikakkiyar budurwa ba ce amma ban taba aure ba” – Rahama Sadau

Shafin al’ummata ta wallafa tambayoyin da akayi wa jarumar da amshoshin da ta bayar kamar haka:

An tambayi jaruma Rahama ko ita budurwa ce gangariya: Ga amsar da ta bayar “Ni budurwace, amma ba budurwa fil a leda ba, domin na rasa budurcina.”

KU KARANTA: Kannywood Post: Yan sanda sun dirar ma Nafisa Abdullahi a Otel din Katsina da tsakar dare

An tambayeta wanda ya koyamata rawa? Ta amsa cewa “Ali Nuhu.” Me ta fi jin tsoro a duniya? Ta ce “mutuwa.” Yaushe za ta yi aure? Ta ce “kwanannan,” amma bata bayyana ko wanene saurayin nata ba.

Shin za ta iya daina fim? Ta ce “a’a.” Dan wasan da ya fi birgeta a masana’antar fina-finan Hausa Ta ce “Sadiq Sani Sadiq.” Fim din da ta yi wanda ta fi so, ya fi birgeta Ta ce fim din turanci na “Sons of the Caliphate” An tambayeta ko shekarunta nawa? Ta ce, “24.”

Comment(3)

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *