Ra’ayi: Budaddiyar wasika zuwa ga Ya’u Umar Gwajogwajo – Daga Nuraddeeni Adam Tina

Ra’ayi: Budaddiyar wasika zuwa ga Ya’u Umar Gwajogwajo – Daga Nuraddeeni Adam Tina

Ra’ayi: Budaddiyar wasika zuwa ga Ya’u Umar Gwajogwajo – Daga Nuraddeeni Adam Tina

0
1

AIKIN DA JAM’IYYAR APC TAYI YASA NA KOMA APC INJI BABA YA’U UMAR GWAJO GWAJO.

A jiya wajen taron amsar mai girma tsohon Speaker na jahar Katsina, Ya Bayyana Cewa aikin da jam’iyyar APC tayi shine Dalilin shi na Komawa APC .

Mai girma tsohon Speaker Akwai Kuskure Wajen wannan maganar domin da kai akayi mulki tsawon Shekaru 16 a jahar Katsina.

Aikin da PDP Tayi a garin gwajo gwajo shi Kanshi aiki ne Na Gani na Fada domin ni Nasan APC bata iya aikin PDP koda Zata share Shekaru 50.

Mai Girma Tsohon Speaker kada Kamanta Matsayin da Kataba Rikewa A PDP wanda Rawar da jam’iyyar PDP ta taka yasa aka Zaɓe ka chairman Har sau Biyu, aka zaɓe ka dan majalisar dokokin jahar Katsina har Sau Biyu kuma aka Zaɓe ka Matsayin Speaker na majalisar dokokin jahar Katsina Shekaru 8.

Mai Girma Baba Speaker Nasan dukkanin aikin Matsayin da ka taba Rikewa idan Kaje neman tazarce da aikin PDP kake neman Kuri’ar al’umma.

Babu Shakka Baba Ya’u Gwajo Gwajo, Fadin Cewa aikin APC ne yaja Hankalinka ka Koma APC Tamkar da Sokawa kai wuƙa ne, domin da kai aka shirya  aka kai aka aiwatar aka kuma Gudanar da Yawunka domin Takobin daka rike mai kaifi biyu ce.

Zan so Baba Gwajo Gwajo ya fadi Gaskiyar abunda yaja Ra’ayin Shi zuwa APC banda abubuwa Guda Uku ne kuma Kowa Yasan su a jahar Katsina, wato 1 Masari, 2 Masara, 3 Masassara .

Zata iya Yiyuwa Wadanda Kaba Kwangila su zage mu, To mu bamu Shakkar haka ita gaskiya daya ce Daga kin ta sai bata.

Daga Karshe muna maka Fatan Alkhairi amma idan za’a hau kuka a Cire Takalmi baba, domin dukkanin abunda Akayi cikin Duhu to Haske zaya Kore shi.

Talakka shine Wuka shine naman shine zaya Yanke hukunci idan lokaci yayi, idan bamu Manta ba haka PDP ta rinka bin yan adawa Tana Maido su PDP cikin su Harda Yan TAKARKARU DABAN DABAN A JAM’IYYAR adawa amma da lokaci Yazo Sai Gashi an Zabi APC, wanda Baba Kaima Sheda ne akan haka domin ka nemi SENATOR Kafadi. Wannan Shine zaya kara maimaita kanshi A Zaɓe mai zuwa 2019 da yardar Allah, domin al’umma. Ba Suga aikin da Akayi Masu ba a jahar Katsina da har zasu kara Zabar APC saboda haka mun aje ma Baba gurin shi Kamun ya Dawo Gida kamar yanda HON. KOFA ya tafi ya gani duk karya ce ya dawo PDP.

Allah Ya bamu Sa’a ya bamu Shugabanni nagari ya kara bamu Damar rike amana ameen.

Comrad Nuraddeen Adam Kankara Tina (Chairman) Katsina State PDP Social Media Organization.

Comment(1)

  1. Kai nuraddenn bantaba ganin sakaranmutum irinkaba wlh inaruwanka kuma wata fadama haka akesiyasa kawai Dan jahilchi Yakima yawa cikin kai saikaita hauka yakamata kakoma makaranta domin cikikanka duk jahilchine banza wawa sakarai dabba marar aikinyi daga ni SALISU sani dori

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *