Aljanai sun watsa taron gayu masu party a Funtua

Aljanai sun watsa taron gayu masu party a Funtua

Aljanai sun watsa taron gayu masu party a Funtua

0
2

Mun samu rohoton cewa wasu jama’ar Aljanu wadanda muke kyautata zaton ‘Yan hisbah ne sun tarwatsa taron wasu gayu maza da ‘yanmata da suke taron “Night party” da daddare a GRA Funtua.

Al’amarin dai ya faru ne sakamakon gardama  da ta barke tsakaninsu bisa sha’anin wata budurwa wadda ta gaza rera waqar da aka bata su yi mamming ita da saurayinta.

Rigirmar dai ita ta kara barkewa da wasu gayu da suke ganin cewa kawai ta fita ta bada wuri tun da ta gaza, kuma tana ta kwafsawa, a daidai sadda wasu suke ganin a barta ta qara qoqartawa.

A taqaicce dai ‘Yan mata kusan goma sha daya ne suka yanke jiki suka fadi qasa warwas suna ihu da haure haure
sakamakon bugun Aljani!

Tuni su samarin suka ranta a na kare sai dai kuma wasu jami’an yan sanda  da suke akan aikinsu na sintiri (patrol) sune suka kai gudunmuwa inda aka zuba ‘yanmatan nan a Hilux
aka maidasu gidajen iyayensu kamar yadda Katsina Post ta samu labarin  daga  ‘daya daga wadanda labarin ya rutsa da su .

Comment(2)

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *