MATASAN  YANKIN KARADUWA SUN ZABI ENGR.NURA KHALIL A MATSAYIN WAKILIN SU.

MATASAN YANKIN KARADUWA SUN ZABI ENGR.NURA KHALIL A MATSAYIN WAKILIN SU.

Daukar Nauyi: Funtua Mandate Promoters

MATASAN YANKIN KARADUWA SUN ZABI ENGR.NURA KHALIL A MATSAYIN WAKILIN SU.

0
0

A jiya ne,wata kungiya da ke Funtua watau Nura Khalil Youth Consultative Forum suka yi taro na musamman domin ganin sun tsaida dan takarar su watau Engr.Muhammad Nura Khalil a matsayin dan takarar su wanda zai wakilce su a  kujerar Sanata na Funtua a za6e mai zuwa 2019.

Haka kuma Matasan sun tuntu6i bangaren ‘yankin karaduwa domin neman goyon bayan su,wanda haka yasa wadansu matasan suka amince da wannan kudiri nasu.

Wannan tafiya dai tana karkashin jagorancin Abubakar  Bala Funtua da kuma Aminu Gide Funtua Kamar yadda suka wallafa a shafin su na sada zumunta watau(Facebook).

Matasa dai a bangarori daban-daban na jihar Katsina suna ta kokarin kafa irin wadannan kungiyoyi domin ganin sun fiddo dan takar da zai wakilce su,bisa la’akari da yadda guguwar zabe take kara tahowa.

Engr.Muhammad Nura khalil dai ya dade yana neman kujerar gwamna a jahar Katsina.A yanzu ne  dai wadansu suke ganin cewa ya dace ya fito ya nemi kujerar Sanata.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *