2017: Yan sandan Katsina sun cafke wadanda ake zargi da fyade su 210

2017: Yan sandan Katsina sun cafke wadanda ake zargi da fyade su 210

Daukar Nauyi: Funtua Mandate Promoters

2017: Yan sandan Katsina sun cafke wadanda ake zargi da fyade su 210

0
0

Rundunar ’Yan sandan Jihar Katsina ta bayyana cewa ta samu rahoton aikata fyade a jihar har sau 210 a cikin 2017.

Kakakin rundunar, Isa Gambo ne ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN a Katsina cewa an kama mutane har 275 da ake zargi da fyade a cikin 2017.

Gambo ya kara da cewa yanzu haka akwai kararraki har 2017 a gaban alkalai da ke kotuna daban-daban, masu alaka da aikata fyade. Ya ce sauran uku kuma ana kan binciken su.

Kakakin ya ce a cikin 2017, an kama wadanda ake zargi da aikaya fashi da makami har mutum 320, yayin da aka samu rahotannin fashi da makami har a wurare 204 duk a cikin 2017.

Gambo ya ci gaba da cewa ana kan gurfanar da rahotannin fashi har 155, yayin da ake kan binciken sauran.

An kuma samu rahotannin kisa a wurare 150, inda aka kama mutane 319 dangane da hannu a zargin kisa duk a cikin 2017.

Da ya ke magana a kan satar shanu kuwa, Gambo ya ce an kwato shanu 313, tumaki 24 daga barayin shanu 29 a cikin 2017.

Ya kuma yi magana a kan yawan kudade da bindigogin da aka samu a hannun ‘yan fashi da makami. Sannan kuma ya koka da matsalar kayan aiki, kamar yadda Katsina Post ta samo daga jaridar Premium Times

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *