Duk dan PDP a Katsina barawo ne banda wanda ya dawo APC – Shugaban jam’iyyar APC

Duk dan PDP a Katsina barawo ne banda wanda ya dawo APC – Shugaban jam’iyyar APC

Daukar Nauyi: Funtua Mandate Promoters

Duk dan PDP a Katsina barawo ne banda wanda ya dawo APC – Shugaban jam’iyyar APC

0
0

Jam’iyyar APC a jihar Katsina ta bayyana cewa duk ‘yan PDP barayi ne amma banda wadanda suka sauya sheka daga PDP zuwa jam’iyyarsu ta APC saboda har yanzu ba a kama su da laifin sata ba, kamar dai yadda jaridar Leadership A Yau ta ruwaito.

Alhaji Shitu S. Shitu ya bayyana haka a wani mataki na maida martani ga shugaban jam’iyyar adawa ta PDP, Alhaji Salisu Yusuf Majigiri bisa zargin da ya yi na cewa gwamnatin APC karkashin jagorancin Aminu Bello Masari ta yi wa Naira Biliyan 400 hadiyar kwafino a cikin watanni talatin da hawa mulki.

Shugaban wanda maitamakinsa na shiryar Funtua ya wakilta, Bala Abu Musawa ya ce lallai Majigiri ya gigice so sai, tunda ya kasa gane inda aka nufa a wannan gwamnati da take abubuwa a bude, ba kamar yadda suka gudanar da ta so ba. Ya kara da cewa, ada lafiyar lau suka tare da shugaban jam’iyyar na PDP amma komawar da wasu jiga-jigar jam’iyyar PDP suka yi zuwa jam’iyyar APC ya sa Majigiri zautuwa inda ya fara wadanda soki burutsu.

Alhaji Shitu S. Shitu ya ce har gobe sun zuba ido suna sauraran dawowa shugaban jam’iyyar PDP Honarabul Salisu Yusuf Majigiri zuwa jam’iyyar APC adalci da iya mulki domin ya bada tasa gudunmawa a ciyar da jihar Katsina gaba.

“Kun ce ‘yan PDP barayi ne kuma kullin sai kun amshe su zuwa jam’iyyarku ta APC shin an yafe masu ne  ko an tsarkakesu daga zunubansu sannan za su dawo wannan jam’iyyar ta ku?” Tambayar da ake yi wa shugaban jam’iyyar APC ke nan.

“Sai ya ce duk barawon da baka kama ya ya sunanshi? Duk wadanda suka dawo wannan jam’iyya babu wanda kotu ta ce mashi barawo ne saboda haka babu laifi idan suka dawo cikin wannan jam’iyya ta APC inji shi.”

Daga cikin irin kalubalantar da jam’iyyar PDP ta yi wa gwamnatin APC har da cewa idan Masari isa ya fito ayi tattaunawa keke-da-keke da shi akan kudadan da ya karba amma har yanzu babu aiki na biliyan daya da za a nuna a jihar Katsina baki daya ina kudadan suka makale ?

Da yake maida martani shugaban na APC ya ce gwamna Masari ba tsaran Majigiri bane, idan jam’iyyar PDP ta shirya ta tuntubi jam’iyyar APC amma ba gwamna Masari ba, tsohun Gwamnan jihar Katsina Ibrahim Shehu Shema shi ne tsaran Masari amma ba jam’iyya  PDP ba.

Kazalika jam’iyyar ta PDP ta zargin APC da zama Iliya dan mai karfi akan sauran jama’a na hanasu damar tsayawa takarar gwamna a karkashin jam’iyyar APC inda shugaban jam’iyyar ya ce ba su da dan takara a shekarar ta 2019 daga Masari sai Buhari kuma har yanzu suna kan bakan su.

Sai dai kuma jam’iyyar APC ta ce, a je a duba kundin tarihi a gani, wanene ya zama Iliya dan Mai karfi tsakanin jam’iyyar APC da PDP? Wanda acewar shugaban APC rashin adalci yasa duk wani mai karfin fada aji ya bar jam’iyyar PDP ya dawo APC.

Ya kuma kalubalanci jam’iyyar PDP da ta fadi koda mutun daya mai tasiri a siyasar jihar Katsina da ya sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa PDP amma su ko kwananan sun karbi tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Katsina tare da tsohun matamakin kakakin majalisar, Honarabul Ya’u Umar gwajo-gwajo da kuma kwamared Bilyaminu Mohammaed Rimi zuwa jam’iyyarsu ta APC adalci.

Haka kuma jam’iyya ta APC ta yi bayani dalla-dalla akan irin kudadan da ta amsa tun daga lokacin da ta hau karagar mulki da kuma bayanin yadda suka kashe su a fannoni daban-daban da suka hada da bangaran Ilimi da kiwon lafiya da tsaro da Noma da samar da aikin yi da sana’o’I da samar da ruwan sha da dai sauransu.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *