Kannywood Post : Ko na sake yin aure ba zan dena harkar fim ba – Khadija Mustapha

Kannywood Post : Ko na sake yin aure ba zan dena harkar fim ba – Khadija Mustapha

Kannywood Post : Ko na sake yin aure ba zan dena harkar fim ba – Khadija Mustapha

0
0

Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Hausa a masana’antar Kannywood watau Khadija Mustapha ta bayyana cewa tana da burin cigaba da harkar fim ko da tayi aure a nan gaba.
Jarumar dai ta bayyana hakan ne a cikin wata fira da tayi da wata mujallar dake buga labaran masana’antar fina-finan Hausa inda tace tana da burin cigaba da shiryawa tare kuma da daukar nauyin fina-finai koda ta yi aure.
Katsina Post HAUSA dai ta samu cewa jarumar ta kuma zayyana yadda ta dade tana sha’awar yin fim tun tana yarinya karama kafin daga bisani ta tsunduma cikin fim din gadan-gadan da kanta.

Dandalin Kannywood: Dalilin da yasa nayi ma Umma Shehu Tambaya akan addini – Aminu Momo

Tun da farkon tattaunawar dai jarumar ta labarta cewa ita shekarun ta 27 a duniya sannan kuma ta taba yin aure har ma ta haifi ‘ya daya kafin auren nata ya mutu.
Haka zalika jarumar ta bayyana fim din ‘Matar Hamza’ a matsayin wanda yafi kwanta mata a rai saboda yadda ta fita daga Kano zuwa Zamfara domin yin sa.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *