Matashi ya rasa ransa wajen gwajin maganin bindiga a Katsina

Matashi ya rasa ransa wajen gwajin maganin bindiga a Katsina

Daukar Nauyi: Funtua Mandate Promoters

Matashi ya rasa ransa wajen gwajin maganin bindiga a Katsina

0
0

Hukuma ta damke wani mai sayar da maganin gargajiya, Usman Saidu, bisa laifin salwantar da rayuwar wani matashi dan shekara 27 mai suna Aliyu Yahuza a jihar Katsina.

An gano cewa marigayin ya mutu ne bayan ya saya maganin bindiga daga hannun Usman Saidu wanda ya tabbatar masa cewa babu wani harsashi da zai iya ratsa jikin sa idan ya sha. Matashi ya rasa ransa wajen gwajin maganin bindiga.

Domin gwada ingancin maganin, Yahuza ya bayar da umurnin a harbe shi a kirji da bindigar farauta sai dai harsashin ya ratsa shi kuma hakan yayi sanadiyar mutuwar sa nan take. Hakan yasa hukuma ke tuhumar Saidu da laifin cin amana da kisan kai.

Mai maganin gargajiyar mai shekaru 42 a duniya zai cigaba da zama a tsare har zuwa ranar 22 ga watan Febrairu inda babban Majistare Hajiya Fadila Dikko za ta saurara karar sa.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *