Badakalar N300m: Kotu ta wanke SSG Mustapha Inuwa da Zakka

Badakalar N300m: Kotu ta wanke SSG Mustapha Inuwa da Zakka

Daukar Nauyi: Funtua Mandate Promoters

Badakalar N300m: Kotu ta wanke SSG Mustapha Inuwa da Zakka

0
0

Daga shafin Maiwada Dammallam

“A kwanakin baya wata jaridar wala-wala wadda wasu y’an kwanta-kwanta suka kafa mai suna “THE POLITY” ta shirga wata karya inda tace da Maigirma Gwamna Aminu Bello Masari da Sakataren Gwamnati, Alhaji Mustapha Inuwa tare da Kwamishinan Kananan Hukumomi, Alhaji Abdulkadir Zakka sunyi sama da fadi da har Naira Miliyan dari uku (N300) kudaden Jihar Katsina ba bisa ka’ida ba.

Rashin Jin dadin kazafin yasa shugabannin 3 suka runtuma kotu dan neman kotu tayi bincike dan ta wankesu kan zargin da baida makama balle tushe. Kotu ta nemi jami’an The Polity dan basu sammace suzo su kare zargin amma sai suka cika wando da iska sukayi batan dabo. Alhamdulillah yau Mai Shari’a, Maikaita Bako, ya yanke hukunci kuma yayi watsi da zargin a matsayin karya mara tushe ballantana makama. Akan haka yaba Gwamna Masari da Alhaji Mustapha Inuwa da Kwamishina Zakka ladar Naira Miliyan 50 (N50m) dan yazama ladabtarwa ga jaridar The Polity, ya kuma zama Jan kunne ga masu yada karya dan suyi batanci.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *