Labari da duminsa: Kotun daukaka kara ta tabbatar da soke zaben Dan majalissar Mashi, Dutsi

Labari da duminsa: Kotun daukaka kara ta tabbatar da soke zaben Dan majalissar Mashi, Dutsi

Daukar Nauyi: Funtua Mandate Promoters

Labari da duminsa: Kotun daukaka kara ta tabbatar da soke zaben Dan majalissar Mashi, Dutsi

0
1

A yau Jumu’a kotun daukaka kara dake Kaduna ta tabbatar da soke zaben Dan majalissar tarayya dake wakiltar Mashi da Dutsi, Hon. Masur Ali Mashi, tare da bayar da umurnin nan da kwana 30 a sake sabon zabe.

Za a iya tuna cewa a ranar 15 ga watan Nuwamban 2017 Katsina Post ta kawo maku labarin soke zaben da kotun sauraron koken zabe ta jihar Katsina, ta yi a kan zaben cike gurbi na dan majalissar tarayya dake wakiltar Mashi da Dutsi, Mansur Ali Mashi, tare da bayar da umurnin sake sabon zabe cikin kwana 90.

A hukuncin da ya yanke shugaban kotun sauraron koken zaben Mr LM Boufini, ya ce zaben na cike da kurakurai, musamman a runfunan zabe 15 wadanda sune suka kawo nakasu ga zaben.

An dai gudanar da zaben cike gurbin ne a ranar 20 ga watan Mayun 2017 sakamakon rasuwar Dan majalissar yankin marigayi Sani Bello, inda hukumar zabe INEC ta bayyana dan takarar jam’iyyar APC Mansur Ali Mashi ya lashe zaben .

Sai dai abokin hamayyarsa na jam’iyyar PDP Nazifi Bello ya maka shi kotu inda yake kalubalantar sahihancin zaben

Sai dai yanzun abin da za mu zura ido mu gani, shi ne, ko jam’iyyar APC za ta yi aiki da hukuncin kotun daukaka karar ta bari a sake gudanar da sabon zaben, ko kuwa za ta sake daukaka kara zuwa kotun koli

Comment(1)

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *