CANJIN RAYUWA [Kashi na Hudu] Tare da Halima K. Mashi (Shafi na 66 – 70)

CANJIN RAYUWA [Kashi na Hudu] Tare da Halima K. Mashi (Shafi na 66 – 70)

CANJIN RAYUWA [Kashi na Hudu] Tare da Halima K. Mashi (Shafi na 66 – 70)

0
1

Hasana da usaina suna zaune suna kallon rufe tafsir din Ismail, Hasana tace, kai Malam yayi wlh! Na qosa daddy yayi mana izinin zuwa muga sis Mimi. Itama nasan ynxun ta hadu.

Usaina tace, ai na dauki number din da ya bada wadda yace mutane suyi message kawai banda kira in sunada tambaya, so muyi masa text cewa, mune. Sainya fada mana gidansu, sai muje muga sis Mimi. Muryar Hajiya sauda ta katsesu da cewa, Allah yasa in samu labari. Wai ba ku nace ma tana lfy bane. Kuma fa na fada muku cewa, akwai matsala in munyi yunqurin zuwa gurinta zata sake guduwa. Karku damu tunda muna samun labarinta. Muyi ta Addu’a komai zai wuce.

Hasana tace, Hajiya shi Malam a matsayinsa na Malami ba sai ya nemi lambarki ba kiji komai daga bakinsa? Usaina tace, ya fa san nan gidan meyasa ma ba zaizo ba? Hajiya sauda tace, Nice da laifi, don na tura masa saqo cewa, naji dalilan mahaifin Mimi, kuma na gamsu dashi. Don haka nima zaka jini shiru. Kaima kayi haquri karka sake nemana ko a waya. Ina mai sake baka amanarta. Lokaci yana zuwa da zamu nemeka da kanmu. Kunji tun daga lokacin ban sake nemanshi ba, shima bai sake ji daga gareni ba.

Hasana tace, to sai zuwa yaushe ne sannan za’aje gurinta? Usaina tace, ke kam kamar bada hausa Hajiya tayi magana ba? Hajiya sauda tace, zaku soma musunku ko? To ni nayi nan! Ta nufi kicin. Ranar sallah, Ismail ya matsawa Mimi wai ta shirya suje masallaci. Da ma tun ranar jajibiri yake fada mata lokacin da yazo ya kawo mata dinkinta. Tace, ba zataje ba, qila ‘yan gidansu zasuje.

Yace, ba ga niqabinki ba, sai ki 6oye fuskarki, dama amfaninsa kenan. Zama haka ba ya yiwuwa Mimi, dole sai da dan fita ana dan motsa jiki. Balle sallar idi wadda daga shekara sai shekara. Ba tada za6i dole ta shirya cikin leshinta, yayi mata kyau matuqa, tayi alwalla, sannan ta shafa hodarta da jan baki, ta saka hijabin da niqabi. Suka fito tace, yiwa yaya sallama. Ummi ma da take ta rabon abinci gidajen maqota tayi kyau cikin kayan sallarta. Su kuwa su saddam dama sun tafi da abbansu a mashin.

Ismail yayi kyau cikin wani tsadadden yadi, mai ruwan madara, malum-malum ce ta dauki aiki. Hularsa da takalminsa sun dace da kayansa. Yayi kyau matuqa.

Ita kanta Mimi lokacin da ya shigo Gidan, sai da Zuciyarta ta buga. Daga lokacin da Ismail ya soma tafsir zuwa ranar sallah, yayi abokai kala-kala, kowa yanason ace suna hulda, masu da kuma talakawa. Daga cikinsu ne wani yazo har gida ya daukeshi, shine yace, su biyo ya dauki matarsa. Mutane sukanyi mamakin ganin Ismail a wani guri daban. Duk wanda ya tambayeshi yakan ce masa, shi ba lazauni bane. Matarsa kuma ba tada isasshiyar lfy, shiyasa ya barta gidan yayarsa. Bayan sun dawo sallah ne Ismail yaci abinci anan gidan, sannan ya miqe zai fita. Sai Mimi taji sam batason ya fita. Amma ba tada ikon hanashi, wani sonshi ne taji a cikin Zuciyarta. Tana kallonshi ya fice.

Bayan sallah da kwana tara Ismail suka shirya nasu-yanasu sai makaranta. A ranar ne Mimi taji inama itace, Rabi’a. Ranar ce, tayi kuka sosai, wanda batasan ko na menene ba. Ismail yayi zaton ko tana yi ne don bai saketa ba. Sai yace, karki damu khadija, shekara kamar kwana ce, in na dawo komai zaizo qarshe, kinji? Bayan tafiyarsu tayi ta dana sanin qin yarda da tayi ya sai mata waya. Amma tace, bataso. A fili tace, kashh! Menene ma zai sa ince ban son waya? Tsaki taja, tare dayin tagumi.

Ynxun kam ta gama fahimtar cewa, Zuciyarta tana matuqar son Ismail, sai dai tsoronta daya shine, shi baya sonta. In ba zata manta ba ya sha fadin cewa, shi mace mai kyau yakeso ya aura. Tuna hakan sai taji jikinta ya mutu. Ta kalli kudin daya bata kafin ya tafi. A fili tace, dole ne in nemi wanda zai siyomin waya ko don in hada hulda dashi. Tsaki taja, a ranta tace, ta yarda jama’a rahama ne, inda tana hulda dasu da ynxun ta samu mai siyo mata. Dakin yaya Amina taje, tace yaya inason a siyomin waya ne.

Yaya Amina tasha mamaki, “ke kuwa meya hanaki yarda Ismail ya siya miki? Don nasan babba zai sai miki. Tace, lokacin banason wayarne, amma inasonta ko don inji Rediyo. Amma fa karki fadama kawun su Ummi. Tace,  shikenan ki kawo sai qanin abban su saddam ya siyo miki. Ta dauko dubu bakwai, cikin dubu ashirin din da Ismail ya bata kafin ya tafi.

Zainabu kuwa tunda taga Ismail a TV, hankalinta yayi matuqar tashi. A fili tace, Ismail yafi qarfi na ynxun. Ta saka kukan takaici, tayi har ta gode ma Allah. Innarta cikin tsantan nadama tace, zainabu kiyi haquri, qila zaku hadu ne ko anan gaba.

Tunda yana sonki, na san ma zai dawo gareki. Zainabu dai bata tanka ba. Innar ce da kanta ta fita neman labarin Ismail, har gidan mahaifinsa gurin su fatu. Anan ne fatu take fada mata cewa, Ismail yana madina garin manzo, dama zuwa yayi don can yake karatu. Ta qara da cewa, Ismail fa ya wuce da tunaninki, mu kanmu mun dangana bare ke. Dole mu dangana ko don alherin da yakeyi mana.

Azumin nan shine geron kununmu, shine waken qosanmu. Da sallah tazo kuwa, zo kiyi kallon hidimar, dinkunanmu da yara, ke har cefanen sallah. Innar zainabu tace nima ai nadamar ta kawoni, ban san yaya zanyi da zainabu ba, taqi sauraron kowa. Fatu tace, dama ta saurari kowa, sbd Ismail da ya yafe tunaninta. jiki babu qarfi ta koma Gida.

Ya zuwa wannan lokacin, rikicin su Na’ima ya kai su ga zuwa kotu, inda shi Abbas ke qarar Na’ima, akan ta bashi dansa. Ita kuma Na’ima tace, ba zata bada shi ba. Duka 6angaren guda biyu sun dauki lauyoyi. Inda ake fafatawa tare da dage zaman sauraron shari’ar.

Nadama kuwa, Momy Nafisa tayi akan auren nan yafi cikin buhu. Ita kuwa Na’ima nata ganin alhakin Mimi ne. Duk lokacin da tace haka, sai momy Nafisa tace, ki daina wannan maganar, ai komai muqaddari ne. Na’ima tace, qaddarar da mutum yake qadddara ma kansa ba. Da mun bar Mimi ta aure shi, na tabbata hakan ba zai faru ba. Haka Allah yake ikonsa, sau da yawa sai mutum yayi ha’inci, sai kuma kaga ya dawo yana nadama. Kukan Na’ima da yawa, ita ba a karatunba, ita ba ga auren ba.

Ynxun ne take burin in ya saketa, ta koma makaranta. Shi kuma yace, tana bashi dansa zai sake ta. Lauyoyinta suna ta zuba hujjojinsu kan cewa, dole ne ya saketa tare kuma da bar mata danta don itace tafi dacewa ta kula dashi. Su ma nasa lauyoyin hujjojinsu suke bajewa akan cewa shine yafi dacewa ya riqe dansa a matsayin sa na uba. Nidai nace, ku kuka sani, mu dai ‘yan kallo ne.

Lokacin da aka kawo wa Mimi wayarta, ta hada ta tasa aka sai mata layi ta saka aciki. Number Ismail kawai ta dauka a cikin wayar yaya Amina. Wtsapp Mimi ta bude, cikin sa’a kuwa da lambar yakeyi, hotonsa ne ma yasa a D.P dinsa,yana sanye da farar jallabiya. A saudiyya ya dauki hoton daga gani. Wannan lokacin ma yana online. Mimi tayi murmushi sannan tayi masa sallama. Sam bai kula sallamarta ba, duk da tayi ta kusan sau goma. Tace, nasan yaya zanyi.

Ta sauka daga kan wtsapp din ta tura masa message, da cewa. Dama haka malaman suke basa son sauraron al’ummarsu, balle su basu fatawa akan matsalolinsu? To, ka sani bin Abdurrahaman, in har na mutu ban samu mafita a matsalar da nake ciki ba, to ka sani har da kai zunubin, domin na kira baka daga ba. Kuma nayi maka magana ta wtsapp baka kula ni ba. To ynxun ga message dina nan. Tana turawa tayi murmushi, sai ta kashe wayar ta a je.

Bata sake kunnawa ba sai bayan kwana uku. Tana kunnawa saqonni guda uku suka shigo, data duba daya na MTN, biyu na Ismail dama da Malam tayi saving. Murmushi tayi, sannan ta bude saqon. Gajerrn saqo ne, kawai cewa yayi, ki fadi matsalarki. ‘yar dariya tayi don ganin cewa zatayi wasa da hankalinsa.

Ta hau wtsapp nan ma saqon iri daya ne. Ta soma tunanin me zata rubuta masa, wanda zaija hankalinsa, ya saurareta? Sai ta soma rubuta cewa, Malam Allah ya sani tunda nake ban ta6a ji ko ganin matsala irin tawa ba, ko da a film ko kuma labarin qirqira. Sai ta tura masa. Daga nan sai ta kashe wayar. Washegari data hau wtsapp sai taga yace, ki fadi matsalarki kai tsaye ba tare da kin gutsutsura batun ba. Ke nake sauraro.

Dariya tayi, sosai sannan ta tura masa cewa, roqo na da kai, shine in kaji wannan matsalar tawa ka taimakamin, kuma ko da kisan kai ne ya kasance hukunci na to zan dauka. Ta tura masa. Haka tayi ta tura masa wadannan saqonni na wasa da hankali, tun yana nuna mata yanason jin ko wace matsala ce, ta daina jin tsoronsa ta fada masa, har ya gaji yayi banza da ita. Tare da haka, in ya kira yaya Amina yakance, a bashi Mimi su gaisa. Cikin ja masa ajin data saba yi take amsa su gaisa. Inya tambayi matsala, sai tace babu.

Kwancitashi su Ismail sun kammala karatu na digiri, tare da sakamako mai kyau. Hukumar qasar ta tuntu6i daliban da aka yaye a wannan shekarar, ko akwai wanda yakeson yin aiki tare da su bisa ga albashi mai tsoka? Su Ismail kam cewa sukayi sunfi son suzo su amfanar da ilimin da suka samo ga al’ummar qasarsu. Sannan Ismail yanason samun nasa iyalin, ya gaji haka.

Mimi bata ta6a yin murnar dawowar Ismail ba kamar wannan karon. Domin gsky tayi kewarsa, tanason ganinsa, sosai matuqa. Wani abu da ya sake burge ta shine tasha gwada Ismail da sim kala-kala, don taga ko yana hulda da mata, amma sai ta sameshi a natsattse wanda bashi da lokacin shashanci.

Sun iso gida cike da murna da doki. saidai Ismail ya baro madina cike da burin komawa don samun digirinsa na biyu, in komai ya tafi masa daidai. Dakinsa ya sauka, wannan karon zai kama masauki amma sai ya saita lamuransa.

Comment(1)

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *