Kungiyar Masariyya ta kaddamar da shugabannin ta a karamar hukumar Ingawa

Kungiyar Masariyya ta kaddamar da shugabannin ta a karamar hukumar Ingawa

Kungiyar Masariyya ta kaddamar da shugabannin ta a karamar hukumar Ingawa

0
1

Kungiyar nan mai rajin kare muradun gwamnatin APC a jihar Katsina karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari mai suna Masariyya wadda DG Abubakar Soja Tsanni ke shugabanta ta kaddamar da shugabannin ta a karamar hukumar Ingawa.

Taron kaddamarwar dai ya samu halartar dukkan masu fada aji na jam’iyyar ta APC a karamar hukumar wadanda suka yi fitowar farin dango zuwa sakatariyar karamar hukumar inda taron kaddamarwar ya wakana.

Da yake jawabin marabaga dumbin ‘ya’yan kungiyar, shugaban jam’iyyar APC a karamar hukumar, Alhaji Sule Aruwa ya tabbatar wa da kungiyar cikakken goyon bayan jam’iyya a karamar hukumar.

Shi ma da yake yin nasa jawabin, Alhaji Ya’u Sule dake zaman tsohon shugaban jam’iyyar a karamar hukumar kuma wakilin kwamishina Muhammad Kanti Bello ya zayyana wasu muhimman ayyukan da Gwamna Aminu Masari yayi a jihar Katsina inda kuma ya bayyana cikakkiyar kyamar su ga ‘yan APC Akida dake jihar.

Haka zalika shima sabon shugaban kungiyar da aka kaddamar a karamar hukumar, Sulaiman Ahmadu ya kara nuna jin dadin su tare da godiya ga irin salon mulkin gwamnan jihar Katsina.

Shi kuwa Alhaji Abdulaziz Abba Umar dake zaman shugaban kungiyar watau Coordinator na jiha baki daya a cikin bayanin na sa ya kalubalanci jama’ar karamar hukumar ta Ingawa da su tabbatar da sun baiwa Gwamnan jihar Katsina da kuma Shugaban kasa kuri’u akalla dubu 100 a zabe mai zuwa.

Daga karshe a jawabin shugaban tafiyar kuma jagoran kungiyar ta Masariyya, Alhaji Abubakar Soja Tsanni ya saka gasar kazar karfi ta Naira 1 miliyan ga dukkan karamar hukumar da take da rumfunan zabe 150 zuwa kasa da ta kuma bayar da yawan kuri’un da suka fi na karamar hukumar Batagarawa.

Haka zalika an rufe taro da addu’a bayan ya kaddamar da sabbin shugabannin kungiyar ta su tare da kuma raba masu form form kyauta.

Comment(1)

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *