Komawar Musa Adamu APC babban cigaba ne – Inji Karaduwa Media Congress 

Komawar Musa Adamu APC babban cigaba ne – Inji Karaduwa Media Congress 

Komawar Musa Adamu APC babban cigaba ne – Inji Karaduwa Media Congress 

0
0

A wata sanarwa da ta fitar ga manema labarai ta hannun Shugaban ta Teacher Salisu Nasiru Funtua, Kungiyar Karadua Media Congress ta bayyana komawar Hon. Musa Adamu Funtua jam’iyar APC babban cigaba ne ga jam’iyar kuma alama ce da ke tabbatar da cewar jam’iyar na kan turba tagari a kokarin ta na samar da ingantaccen shugabanci a jihar Karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari.

Kungiyar ta bayyana Hon. Musa Adamu Funtua a matsayin gogaggen Dan siyasa da ke son cigaban al’umma da jihar Katsina kuma mutum ne mai dumbin magoya baya a ko’ina cikin jihar  dalilin kyautatawar sa gare su.

“Ba shakka jam’iyar APC na bukatar gogaggun mutane irin su Hon.Musa Adamu Funtua (Dan Kafin Katsina) don taimakawa gwamna Masari tsallakar da jihar tudun mun tsira kamar yadda ya sa gaba.” – Cewar sa.

Ya kara da cewa al’ummar Katsina da cigaban jihar su ne a gaban Hon. Musa Adamu wanda hakan ya yi daidai da Manufofin Gwamna Aminu Bello Masari.

Daga karshe kungiyar ta kira ga daukacin al’ummar jihar da su cigaba da bada goyan baya ga Gwamna Masari da Jam’iyar APC don tabbatuwar canji mai dorewa.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *