CANJIN RAYUWA [Kashi na Hudu] Tare da Halima K. Mashi (Shafi na 71 – 80)

CANJIN RAYUWA [Kashi na Hudu] Tare da Halima K. Mashi (Shafi na 71 – 80)

CANJIN RAYUWA [Kashi na Hudu] Tare da Halima K. Mashi (Shafi na 71 – 80)

0
0

Shi mahmud bashi da wannan matsalar ta gurin zama, domin suna da mazauninsu, daya daga cikin gidajen mahaifinsa. Sunyi isowar dare ne wannan dawowar. Kusan qarfe biyun dare suka shigo katsina. Kai tsaye gidansu ya wuce, ya sauna da kayansa. Su kuma su Mahmud da Rabi’a da dansu mus’ab yayi wayo sosai, suka wuce nasu gidan. Ismail ya buga gidan. Yayyinsa maza guda biyu sukazo sun a tambayar ko wanene? Ismail yace nine Ismail. Da sukazo suka buds mass, suna yi masa sannu da zuwa. Sun yi sallama Sai da safe, suka nufi ciki. Shikam bai kwanta back Sai daya share dakin.

Want Abu daya bawa Ismail mamaki, bayan yay sallar asubahi ya dawo, ya kwanta don ya huta, bai yi niyyar fita ba don yana tsammanin babu Wanda yasan ya dawo, gurin qarfe goma yaji sallama a qofarsa. Barcin nasa sama-sama ne. Don haka Sai ya tashi ya suka jallabiyarsa ya fito, ya baqon nasa, Sam bai sanshi ba, amma ya miqa masa hannu, suka gaisa. Mutumin ya Ciro wasu takardu ya miqa masa, game saqo daga wani bawan Allah, yace in Baka tun kusan wata uku da suka wuce. Ismail ya kalleshi cikin rashin fahimta, saqon menene? Yace mai gidana be, inayi masa aikin sama. Ni kafintan same ne. Duk wani aikin gidajensa ni keyi masa daya shafi Sana.

To shine ya tambayeni ko ma sanka? Nace unguwarmu daya. Ta yiwu Baka sanni ba, ina  can bayan mayo be, gidan malam kadi. Ismail ya kalleshi. Gidan su hashimu? Baqon yace, yauwa, to ni wansu hashimu be. Zakkar gida be, ko ince kyautar gida yace in Baka. Wadannan takardun gidan be. A can unguwar GRA be gidan take. in ka shirya Sai mine in Nina mama.

Cikin mamaki, Ismael yace a ina wannan mai gidan naka yake, kuma yaya sunansa? Baqo yace nidai sunana Nasiru amma shi mai gidana ya hana ni in fadi sunansa ko unguwarsa. Yace, shi yayi ne don Allah, kuma malam ya sakashi a cikin addu’ar Allah ya biya masa buqatunsa na alheri. Ismail yace jirani ina zuwa. Ya koma daki ya canza kaya, ya fito yace, zo muje gurin malam. Sun samu malam Aminu, inda dan aike yayi masa bayanin kimai. Bada 6ata lokaci ba, suka nufi gidan, harda mahmud, wanda ismail yayi masa waya, shima yazo ya samesu.

Sun samu mai gadin gidan ya bude musu suka shiga. Mai gadi yazo ya gaishesu tare da tambayar su ko wanene mai gidan cikinsu? Mahmud yace, wa yasa ka gadin gidan? Yace ‘yalla6ai ne. Yace min duk randa wanda yaba gidan yazo, shi aikinsa ya qare. Mahmud yace, to ya sunan shi ‘yalla6ai din? Tsoho maigadi yace, ya hanani in fadi sunansa.

Sun zaga gidan qato ne sosai. Ginin na gefe hawa daya. Mai gadin ne yabasu makullan ciki tare da  nuna musu ko ina na gidan. Shikam ismail filin gidan ne yafi burgeshi, domin har ya hango yadda zaiyi makaranta a gurin, harda masallaci.

Take ya sanar da su malam Aminu sha’awarsa da gurin, suka ce tabbas bakan yayi. Sun yi bankwana da maigadi bayan ismail ya bashi dan abinda ke hannunsa tare da bashi baquri kan cewa bai fito da kudi ba. Suka fito suka kulle gidan suka tafi da makulli. Babu abinda gidan ke buqata saidai kayan da za’a zuba na amfani. Sun koma gida, inda Ismail ya kawo dubu biyar tare da sabbin jallabiyu a cikin kayansa yaba dan aike tare da bashi haquri, kan cewa dawowarsa kenan daga karatu bashida kudi.

shi  kuwa dan aike godia yayi, tare da cewa, ni ai babu abinda yafi faranta mun rai kamar sada ka da saqonka da nayi. Domin tun shekaran jiya yake cemin cikin satinnan zaku dawo. Ismail yace, wato harma ya san lokacin da zan dawo. Dan aike yace gsky ya sanin kenan. Sukayi bankwana, ismail ya rakashi tare da yi masa godiya mai yawa. Ko daya dawo daki, yayi iyakacin qoqarinsa don ya gane ko wanene. Amma hakan yaci tura. Sai kurum yayi masa addu’ar Allah ya cika masa burinsa, duniya da lahira.

Mimi suna da labarin dawowar ismail amma basu ganshi ba. Mimi bataji dadin hakan ba, domin sai taga kamar bai damu da ita ba. Sai washe gari bayan la’asar, yinin ranar Mimi tayishi ne cikin qunci da rashin walwala. Har yaya ta nemi dalili, amma sai Mimi tace, kanta keyi mata ciwo. Tana zaune a tsakar dakinta tana yanke qumba, kanta babu dankwali ta kama gashinta a tsakiya, kamar yadda ta saba tun tana ‘yar gayunta, muryarsa ta jiyo yayi sallama, sai sowar yara ta jiyo suna yi masa sannu da zuwa. kamar ta tashi ta fita sai kuma ta fasa, ta kalli jikinta, riga da wando ne wadanda shine ya sai mata su. Taje madubi ta kalli fuskarta.

Sai ta samu kanta da zazzaga hoda a tafin hannunta ta hure, sannan ta shafa ta hau tsakiyar gadonta ta zauna, ta kunna TV. Catoon sukeyi. Kusan minti ashirin da tara, sannan ya kalli dakinta, ita wannan bata nan ne? Yaya tace, tananan. Dazun dai tayi fama da ciwon kai, amma yayi sauqi. Da sallama ya shigo. Ta dago tamkar lokacin taji shigowarsa. Qwarjinin dake kan fuskarsa ya doketa, tayi saurin sunkuyar da kai, sannu da zuwa. Yace, sannunki, in zauna bakin gado? Ta dago ta dubeshi, yaune zaka nemi izinina? Yayi murmushi, ai na qara wayau ne ynxun. Da kinsan yaro ne. Tayi dariya, to ka zauna.

Ya tsura mata ido, “kinci naman hawainiya ne? Yayi tambayar cikin tsokana. Ta zaro ido, meka gani? Duk lokacin da na tafi na dawo, sai inga kin canza kala. Gabanta ga fadi, tsoronta kar ya kusheta, ta kalleshi, duk nayi muni ko? Yayi dan murmushi, nidai ban fada ba. Tace to fadamin me nayi? Da ya fahimci tanason jin ta bakinsa game da yabon da yayi niyyar yi mata, sai ya canza da cewa, wai don Allah meyasa in na dawo baki doki na? Tayi masa kallon gefen ido, injiwa? Yace injini mana. In ana dokin mutum ai anayi masa tarba ta musamman da girke-girke.

Ta ta6a baki, ai muma bakayi dokin ganinmu ba. Sai fa da kayi kwanaki, mutane suka gama ganinka, sannan kake zuwa mana nan. Yayi murmushi, amma zuwana na farko nan na fara sauka. Mimi tace, wannan ne kawai. Ta sake maido da wancan zancen. Baka fa bani a msa ba. Tame? Ya fada tare da kanne mata idonsa daya. Canzawar daka ce inayi. Shine nace muni na qara ko? Yayi ‘yar dariya nidai bance ba. Ki kawomin ruwa mai sanyi insha, ya sake kauda zancen.

Ta sauka sannan ta dauki qaramin hijabi tasa. Yasan sbd kayan jikinta ne don sun kama fa tsam, duk motsin da tayi jikinta yana rawa. A zuciyarsa yace, lallai! Yau Mimi ce da rufe tsiraici? A fili yace Albmdlh. Ta kawo masa ruwa da kofi, ya kalli goran ruwan, lallai ‘yan gayu, swan kuke sha?

Tayi masa hararar wasa, wa zai bamu ruwan swan? Na fanfo ne muke sawa yayi sanyi. Ya tsiyaya ya sha. Cikin son jin me yayi niyyar cewa yaqi fada, tace ai kaima ka canza. Ya dubeta don ya riga ya dago ta. Yace, eh nima nasan na canza, na qara kyau sosai haka? Ta harareshi, ka cika son kanka da yawa. Yace inba gaky na fada ba sanar dani kawai. Tayi shiru. Yace shiru yana nufin eh ne. Ni nasan inada kyau. Ta 6ata rai, kai kyau ya dama. Ni ynxu nafison kyan hali. da ne nake kallon kyau wata tsiya. Yayi dariya shima inada shi, don naji mutane suna fada.

Ranta ya sake 6aci. Da gske batasan shi zolayarta yake ba tace, ka cika wasa kanka. Kuma ance duk wanda yace shine, to ba shi bane. Yace nidai nine ismail bin Abdurrahaman. A ranta tace, karma yaga cewa na wani damu dashi ne ma, bari in masa zancen rabuwarmu. Tace gashi dai karatu ya qare, yaushe zamu warware maganarmu? Gabansa ya fadi. Nasa zaton ta dangana da wannan maganar. Maimakon yabata amsa, sai yace, ni na manta ma munyi gida fa. Ya miqe bari in sanar da yaya Amina. Itama ta miqe ta biyoshi. Nan ya labarta musu komai. Suka yi murna sosai.

Yaya tace, kuma takardun da sunanka da komai? Yace cikakken sunana kuwa. Tace ko wanene wannan, Allah ya saka masa da alheri. Yace Ameen, gurina da akwai wasu kudi, zan gani ko zasu sai mana kayan gado dana girki. Ba sune dai akafi buqata ba? Yaya tace sune mana. In ma na gado ko katifa ce zatayi muku. Kayan kicin shine yafi zama dole. Yace hakane mu shirya gobe zanzo in kaiku gidan.

Haka kuwa washegari yazo ya kwashesu. Gidan ya burgesu sosai. Mimi ta shiga fargaba, tana tambayar kanta wa zaisa a gidan? Bata san lokacin da tace to kawunsu ummi yaushe zaka dawo nan gidan? Ya kalli cikin idonta, ya karanci wani abu. Don haka sai yace, bari mu koma gida, zaki bani shawara ko? Ta daga gira, alamun eh. Yayi murmushi.

Ismail tunda ya dawo bai zauna ba, abubuwa zunyi masa yawa. Sun raba takardun neman aiki a jami’o’i kamar su A.B.U da B.U.K, har Abuja. Sannan qungiyarsu ta da’awa, suna ta gudanar da aikace-aikace, musamman na gidan marayun da suke ginawa. Sannan ga gayyata da yake samu gidajen rediyo, da talabijin da gabatar da filaye na addini irinsu tambayoyin addinin musulunci, Filin fatawa, da dai sauransu. Haka sauran jihohi irinsu kaduna, kano, sakoto, suna gayyatarsa don yin majalisi dashi. Hakan yasa ismail ya zama kullum yi nan, yi can. Ga shi har ynxun bai daina zama gaban malamai ba don neman qarin ilimi.

Daukaka ta Allah, lokaci qanqani sunansa ya karade jihohin Arewa. Wannan yasa mahmud ya matsa masa. Wai ya tare a gidansa. Yaso su tare da mahmud din tunda sama ne da qasa, amma sai mahmud yace, in har ya sake ya tare a gidan ismail din, ba zai maida hankali a nasa ginin ba, wanda yayi nisa da farawa. Ranar wata lahadi misalin qarfe takwas da wani abu na dare, ismail ya shigo gurin su mimi, lokacin babu wutar NEPA ta kwanta a tsakar daki akan tabarma, tana dannan wayarta.

Sallamarsa ta jiyo yasa ta kashe tocilar wayar, sannan ta kashe ta gaba daya, ta tura a qasan gado. Lokacin daya iso dakin da sallama, ta amsa. Yace farko dana shigo, sai naga kamar dakinnan da haske. Tace, idonka ne yaga haka. Ya ciro qaramar wayarsa daga aljihu, ya haska dakin. Kafin ya zauna yace, me kuke dashi na ci? Tace shinkafa mukayi da wake, sai mai da yaji. Jiya ne yaya tace, muyi alala, qila kozo, tunda ka kwana biyu baka zo ba. Amma sai kaqi zuwa.

Yace ba zaki gane bane khadija. In  a lissafa maki lamurran dake gabana, zaki sha mamaki. Karku damu da yin abinci dani. In nazo kamar haka in na samu zanci. Ban cika son cin yaji ba, shirya ki rakani muci abinci. Ko kuma ke kici kifinki. Tace kana son jana yawo, ni kuma banason fita. Yace shikenan ba zan matsa miki ba. Tace to bari in shirya muje. Ya ciro wayoyinsa banda wadda ya haska. Kamar ana jira sai ga kira, tamkar kar ya daga, sai kuma ya daga don ya lura da lambar anata kiransa da ita bai ta6a dagawa ba.

Kamar yadda ya zata kuwa mace ce, ya amsa suka gaisa. Yanason tuna inda yasan mai muryar.Ta katse masa tunani da cewa, baka ganeni ba ko? Yace cikin qosawa eh. Tace zainabu ce. Sai kuwa Mimi taga ya miqe da sauri tare da fadin zainabu?! Tace eh nice, malam.

Zuciyarsa ta shiga bugawa da sauri. Yayi ta maza , yaya gida da mai gida da kuma yara? Tayi ‘yar dariya, gida dai lfy mai gida kuwa bama tare. Munfi shekara biyu da rabuwa. Da kuwa qwara daya ne, ya dauki kayansa. Yace, subhanallahi, to Allah yayi miki za6i na alheri.

Tace Ameen nagode, na gaisheka. Wannan kuma number ta ce. In ba laifi adan ajeta, don nayi ga kira baka daga ba, qila don bakasan lambar bane. Ban sani ba ko zan kira neman fatawa. Cikin wani shirinka na samu number lokacin daka bada. Yayi ‘yar dariya, karki damu zanyi saving dinta, nagode. Kasa kashe wayar yayi, sai itace, ta kashe. Ya zauna bakin gado tare da cewa, auren zainabu ya mutu tun shekara biyu? Kenan ma tun ganin da nayi mata.

Yaya tace min tanada aurenta, ashe ba tada shi. Sam ya manta da wata Mimi tana dakin. Ita kam tana zaune hankalinta tashe. Tambayar kanta kawai takeyi wacece kuma Zainabu? Batasan tambayar ta fito fili ba, saida taga ya tsaya cak, daga rawar jikin saving din lambar Zainabu wanda yakeyi. Shi sam ya manta a ina yake ma. Yace, am.. Wata yarinya ce. Ya miqe, ba zaki santa ba. Ya kalleta, ni bari in tafi. Tace zuwa gurin cin abincin fa? Yace mu barshi sai zuwa wani lokaci, zan sha tea in naje gida.

Hankalin Mimi yayi qololuwar tashi, tace, ynxun fa kazo amma har zaka tafi? Yace inada wani uzuri ne, karki damu zan dawo da safe. Bata iya amsa shi ba ya fice. Kai kawo ta dinga yi a dakin. Ta gama yarda cewa tanayi ma ismail wani mugun so, shi yanason wata kenan. Ta fita zuwa dakin yaya Amina ta zauna. Yaya tace yau naga malam ya fita da wuri. Mimi tace, yaya in tambayeki mana? Yaya tace ina jinki.

Mimi ta tsura ma yaya ido, wai wacece Zainabu? Yaya tace Zainabu? Kinsan tane? Mimi ta sake tambaya. Tace umm, wata yarinya ce da ismail yayi mata wani mahaukacin So, shine iyayenta suka yaudareshi, suka bada ta ga wani mai kudi. Zufa ta karyo wa Mimi, ta miqe. Yaya tace, yayi miki zancenta ne? Mimi tace kawunsu ummi ne naji suna waya, ta fada masa aurenta ya mutu shine fa ya fita jiki yana 6ari.

Yaya Amina ta miqe tsaye tabdi! Ai ko duk nacinsa ba zai aureta ba! Shegiya, ko wa ya bata lambarsa? Tuni nasan aurenta ga mutu, amma na share ban fada masa ba. Saboda kar ya koma mata. Mimi cikin fargaba ta miqe tare da fadin saida safe. Yadda yaya taga hankalin Mimi ya tashi ne ya bata mamaki. Har ta miqe da nufin zuwa ta bawa Mimi shawara, sai kuma ta fasa, tace bari in barta ta fara yin shawara da kanta tukunna.

Yarinya kinada miji tun tsawon lokaci, amma me kin dage sai an rabu dake. Daga ganin ta kasan kishi ne can qasan ranga. Ta koma ta zauna. Mimi kuwa tana shiga dakinta ana kawo wuta. Sam bata damu da wutarba, duk da cewa fankar data soma kadawa tana kai mata iska. Sitiri kawai takeyi tsakar daki. Ta rasa wane irin tunani zatayi, ta rasa wa zai bata shawara. Ta zauna bakin gado. Na shiga uku na, ni khadija wa zai bani shawara ynxun? Kalaman yaya Amina ke mata yawo cikin kai, “wata yarinya ce da ismail yayi wa mahaukacin so.

Ta maimaita sunan wai Zainabu. Ta tuna yadda ya miqe zumbur lokacin da ta ambaci sunanta. Ta tuna yadda ya manta da ita a dakin sbd zainabu. A fili tace, lallai za’ayi tan kuwa. Wani tuquqi ne ke taso mata daga qirji, tace, qila ma suna can tare. Ranar dai su Mimi ba’a runtsa ba, sannan bata qulla ma kanta mafita ba. Barci sama-sama tayi shi har asubahi. Sai da tayi sallah sannan varci ya dauketa.

Ta kai kusan tara na safe sannan ta farka. Ta fito da nufin gaida yaya, sannan tayi wanka, sai kuma taga yayar sanye da hijabi zata fita. Tace ina kuma zakije yaya? Tace nan maqota zan shiga aikin biki, wannan gidan da sukace muje muga lefe. Kinsan yau ne daurin auren. Mimi tace, wai dole ne jn mutum yananan garin sai ya shiga aiki kenan? Ban saba ganin haka ba.

Mu in zamuyi biki, ko suna sai akai gurin yin abincj ayi a kawo. Yaya tace, sha’anin masu kudi kenan. Mu nan in baka zuwa, wa zaizo maka? Bakiga sunan Aishatu ba, gidannan cika yayi? Kinsan dai in bana zuwa ba za’a zomin don tsorona ba. Mimi tace, sai kin dawo. Ni dai bana ra’ayin haka. Tayi ‘yar dariya. Aishatu tananan tana varci a uwar daki. Mimi tace to. Ta dauki ruwan wankanta wanda ummi ta zuba mata, kamar kullum tunda bata iya jan ruwa.

Tana  wanka taji shigowar ismail, yana ta sallama ba a amsa. Tana jinshi yana cewa, inma dai yaya Amina batanan, yasan babu inda Mimi zataje, qila tana bandaki. Saida Mimi ta gama ta fito, sannan ta dauki Hijabin Ummi dake kan igiya ta saka.

Ta shiga dakin. Yi tayi tamkar bata ganshi ba. Ta wuce, kan madubi ta zauna tana shafa mai. Ta zame hijabin, ya sauka a wuyanta, dogon gashinta ya bayyana. Ta dauki mataji tana tajeshi. Baqi sidik. Ta lakuto manta na gashi tana kallon gashin cikin madubi. A ranta tana cewa, inda nagode ma Allah, duk lalacewar da nayi gashina bai zube ba. Ta kalli fuskarta a madubin, tace wai wane irin kyau mutuminnan yake buqata wanda yafi nawa? Sai dai ko in balarabiya yake son ya aura. A fili tace, zan so ni kuwa inga zainabun nan wace iri ce ita? Kyanta yaya yake? Yace me kk ce? Cikin sauri ta waiwaya, ta dubesbi.

Yace yau ‘yan miskilancin ne ko? Kin shigo kinyi kamar baki ganni ba. Shiru tayi, sam ta manta yana dakin, tayi zancen zucinta a fili, fatanta Allah yasa baiji taba. Tace kaji abinda nace ne? Yace a’a me kk ce? Ta sauke ajiyar zuciya, sannan ta maida hankali gurin abinda takeyi. Yace, ki fada min me kk ce mana? Sai naji kamar dai kin ambaci zainabu. Ta danyi dim, sannan tace, wai kai ka damu da wata zainabu, tunda ta kiraka jiya, ka fita hankalinka, harma takai ynxun kunnenka yanayi maka gizo ko? Magana mutane sukayi, sai ka zata sunce zainabu ko? Yace ni bance ba ranki ya dade.

Ta zauna tana shafa hoda. Ta gama, taja durowar madubi, ta ciro abin daure gashin ta kamashi a tsakiya. Ta fesa turare sanna ta ciro daguwar rigarta leshi ta saka. Ba tare da ta daura dankwali ba ta nufi kicin. Shi dai yana binta da kallo. Tayi masa kyau a idanunsa. Ta dauko biredinta da ruwan shayi mara madara ta zauna, amma sai damuwa ta hanata cin biredin, sai ruwan shayin take kur6a.

Yace nima zansha. Ta miqa masa na hannunta, kar6a. Yace, ki hadamin wani mana. Ta kalleshi, munin nawa har ya kai cikin kofin shayin ne, shiyasa ba zaka iya sha ba? Yace bance ba naga kamar baki qoshi bane, tunda ko biredin bakici ba. Ta daure fuska, nina qoshi. Yace shikenan bani. Ta miqa masa. Kan gado ta koma ta kwanta, fuskarta tana kallon gefe, tana tunanin nafita. Ya kalleta, baisan me take yiwa fushi ba. Sai ya samu kansa da shiga damuwa.

Yace ki tashi khadija, magana zamuyi, duk da naga yau kina fushi dani.Ta tashi amma taqi kallonsa, kanta yana qasa, tana wasa da yatsun hannunta, fuskarta a daure tam. Yace, to inason zan tare a gidana. Kina ganin ya kamata mu koma tare ne ko kuwa zaki zauna anan? Mimi tayi shiru cikin nazari, sai taga ya kamata ta gwadashi. Tace, kai me ka gani yafi? Ni ko ina daya ne a gurina.

Ya dago yana kallonta cikin ido, sannan yace, banason in takura miki ne, kamar yadda nayi fa fada miki a tun baya. Abin da kikeso shi zan miki. Ta tura baki cikin jin haushi tace ni banida za6i. Ranshi ya sosu, cikin fushi ya miqe, shikenan, ni zan tafi. Duk lokacin da kk za6a, saiki fada min. Ni dai zan tare, kuma zanyi aure. Batasan lokacin da ta miqe tsaye a tsakiyar gadonba. Me kk fada? Yace nasan kinji. Tace ka auri dubu, amma kafin nan ka warware nawa auren dake kanka.

Yace, nufina kenan don nasan bakida burin daya wuce wannan. Amma sai kina ta shirmenki. A sanyaye tace, dama kazo ka sakeni ne? Kafin ya amsa, qaramar wayarsa ta soma ruri. Ya daga ya fita a dakin yana amsawa. Mimi ta zauna tasa kanta cikin gwiwarta tana kuka. Batasan dalilin kukan ba bare asalinsa.

Wata zuciyar ta ingizo ta tare da rada mata cewa, tayi tafiyarta. Ta sauka ta dauko akwatunanta, ta dauki daya, ta soma kwaso kayanta tana zubawa a ciki. Shikuwa yana gama waya ya dawo, da bango ya jingina yana kallonta. Bai hanata ba kuma bai tambayeta dalili ba, har ta gama ta dauki mayafinta tasa takalmi, sannan taja jakar, dariya ce taso ta su6uce masa, amma sai ya fasa. Ya tare qofar dakin.

Tace, ka bani hanya zan wuce! Yace zuwa ina? Tace ina ruwanka dani? In tafi ko ina ma, mun hada zuri’a ne? Kawai ynxun ka bani saki na. Kai ko baka sakeni ba ma tafiya zanyi. Ya girgiza kai, bamu bada zuri’a ba, sai dai bansan gaba ba. Amma ynxun kafin ki tafi tsaya mu gama magana, in yasa sai ki tafi, ba zan hanaki ba. Ya nuna mata bakin gado, ki zauna anan! Fuskarta  a daure ta zauna. Shima ya zauna.

Fadamin mecece damuwarki wadda tasa har zaki tafi ki barmu? Shiru tayi, domin ta rasa me zata ce. In zata fadi gsky, to kishi ne kawai ke cinye ta a zuciya. Amma sai tace, na gaji da kushe ni da kkyi. Duk lokacin da ka tashi, sai kace min mummuna. Sannan kaqi ka cika min alqawari na. Yayi murmushi, ni ban ta6a ce miki mummuna ba. Ta kalleshi, ba girmanka bane yin qarya. Domin kune masu fadin illarta. Jiyan nan kace min ko yaushe ina canzawa. Yace, canzawa nace ko muni nace?

Tayi shiru. yace, banda jiya sai kuma yaushe nace miki? Cikin qarfin gwiwa tace, da muke asibiti, lokacin da nace, bana sonka me kacemin? Inka manta in tuna maka. Cewa fa kayi kaima kafison mace mai kyau. Ya sake yin wani murmushin, tabbas nace haka, amma nace bakida kyau? Tace kusan haka ne? Yace ba dai hakan bane tunda kusan ne. To naji wannan sai kuma batun alqawari, duk alqawurran dana daukar miki a gaban Doctor salis wanne ne ban cika ba? Tayi shiru, tabbas yace zai nesanta ta da iyayenta kuma yayi.

Yace zai kula da ita daidai qarfinsa, kuma yayi, in zata duba tsawon lokacin da ta dauka tana jinya, sun yi ta dawainiya da ita. Ta dubeshi, sai na rabuwa, shine baka cika ba. Yace banda shi na cika sauran? Ta daga kai, alamun eh. Yace to bari in tuna miki. Kinsan na jima ina yi miki alqawarin cewa zan yi miki fiye da kk taso anayi miki na gata ko? Tayi shiru tana kallonsa. Ya tausasa murya, inason ki jira ni in cika wannan alqawarin, ko zamu rabu, ki bari in gama yi miki gatan dana tsara ma kaina, inji dake wani irin dadin da baki sanshi ba.

In yasa nan, sai inyi miki abinda kk so. Tayi wani dan tunani. Sannan tace, zan yarda ne kawai in kaima ka yarda da abinda zan fada ynxun. Yace inajinki. tace zaka daura aure ne lokacin da ka warware nawa auren. Yace ban fahimta ba? Tace, ina nufin ba zaka ki aure ba, sai lokacin daka warware nawa auren.

Yayi shiru don shi tun jiya ya gama tsarinsa. Ya tsara zai auri zainabu don ya gaji da zama haka, ita kuma lokacin data gama shirmenta sai su shirya don babu saki acikin zuciyarsa a ynxun. Daga nan sai ya kaita gaban iyayenta ta nemi gafararsu, duk da Hajiya tace zasu nemeshi in lokaci yayi. Amma dubi yadda ita kuma ta 6ullo masa da wata mamagana.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *