CANJIN RAYUWA [Kashi na Hudu] Tare da Halima K. Mashi (Shafi na 81 – 90)

CANJIN RAYUWA [Kashi na Hudu] Tare da Halima K. Mashi (Shafi na 81 – 90)

CANJIN RAYUWA [Kashi na Hudu] Tare da Halima K. Mashi (Shafi na 81 – 90)

0
1

Ta katse masa tunani da cewa, kayi shiru? Yace, kina ganin zamana babu aure ba ragewar mutunci na bane a matsayina na mai fadakarwa? Ta miqe tsaye, tayi dan taku daya zuwa uku, sannan ta kalleshi, ni da kaine kawai muka san cewa ba kada mata, amma Duniya ta jima da sanin cewa kanada aure. Yace naji saidai karki manta ni fa mutum ne, kuma ba yaro ba, wanda yakai. Kinsan dole ina buqatar abokiyar halittata. Kinsan shekaruna nawa ynxun? Tace ban sani ba, qila zaka gota talatin. Yace yauwa, to in na rantse miki ba zanyi kaffara ba, a takure nake, sannan inason yara. Ynzun dubi mahmud, matarsa tanada ciki na biyu. Ya numfasa, khadija saka idonki cikin nawa, ta kalleshi.

Yace ina buqatar abokiyar rayuwa. Ta sunkuyar da kai, wannan ai zancenka ne da kuma wadda zaka aura. Kukan Aishatu ta jiyo, ta miqe da sauri, har tana tuntu6e da qafarsa zata fadi. Ya sa hannuwansa ya tare ta. Sai tsintar kanta tayi a jikinsa.Duk zun jisu cikin wani yanayi. Shine yayi ta maza. Yace ina zakije haka? Kike sauri zaki fadi kije ki karye, dama gaki nan kamar ‘yar tsinke. Ta tashi da sauri, bakaji kukan Aishatu ba?

Da sauri ta nufi gurin Aishatu. Ta shigo riqe da hannunta, sai lallashinta takeyi. “Yarinya tana kuka kin firgice, ranar da kk haifi naki, sai yaya? Ta harareshi cikin wasa, me zai hadani da haihuwa? Yayi qasa da murya, “wai ba kyajin komai game dani? Tace Aishatu dai tana kallonka. Ya miqe, bari dai in gafi tunda kin fasa yajin. In yaya ta dawo ki fada mata cewa nazo, kuma batun tarewa ya kawoni. Ynxu zance in samu mahmud ne muje kasuwa mj sayi abinda ya sauwaqa, mu zuba a gidan, to shikenan.

A zaure zuka hadu da yaya. Nan suka gaisa yayi mata bayanin dalilin zuwansa har yadda sukayi da mimi. Dariya yaya tayi, domin ta gama gano mimi tsabar son mijinta takeyi, amma sai bata nuna ma Ismail din ba.

Tace khadija kenan ‘yar daru, ‘yar shagwa6a. Zamuyi magana da ita. Amma ni shawarata karka tsaya bata wani za6in ko nan ko can. Kawai kace mata ku koma, ko don sbd kauda hankalin mazu zaton bakada aure. Yace nima haka nekeso, amma kinsan rigimarta. Gashi zai da’awar in saketa takeyi. Ni kuma gsky sai inga in nayi haka ban kyauta wa mahaifiyarta ba. Yaya tace wannan ma bata taso ba. Kudai koma din, qila ma ku sasanta.

Ismail yace, Allah yayi mana jagora. Yaya tace Ameen. Sukayj sallama tayi ciki shi kuma yayi waje. Kafin sati daya, ismail ya sayi abinda ya sauwaqa, sun kai sjn shisshirya. Sannan sun shirya walima, inda su yaya da maqotanta sukayi musu girki, shinkafa ce da waina, sai kaji. Girkin yayi kyau sosai, ga kuma abin sha. Bayan sun tashi daga walimar ne, sannan sukazo suka kwashe kayan sawar mimi, shi da mahmud. Kayan Gado dai tabarma su Ummi.

Duk da haka basu koma ba, sbd ismail zasuje kaduna da kuma Abuja, don gabatar da wasu muhadarori, da kuma lakcoci. Haka kuma suna durowa katsina, ya tarar da takardar gayyata daga gwamnatin jihar katsina. A hannun Malam Aminu ya samu saqon. Yace wannan taro ne na manyan malamai, to ni meya kaini gurin? Malam yace daukaka ce daga Allah, ismail. Shawarar da zan baka kayi taka tsan tsan, domin Malamai ma wasu basa tsoron Allab, musamman in sunga Allah ya baka nasibi.

Sannan kar kayi sanyi gurin fadar gsky, komai dacinta. Ismail yace shikenan zan kula insha Allah, nagode. Gidasa ya wuce, sai da yayi wanka ya huta, sannan ya fita zuwa gidan yaya Amina. Yayi matuqar qosawa Mimi ta dawo, ko don Abinci. Gashi a gida mai kyau, amma abinci sai ya siya. Can yaci abinci, sannan yace, yaushe zaku raka mimi can gidan? Tace sai jibi.

Washegari ya samu halartar gayyatar da akai masu. Maqasudin zaman dai, sbd tafsir ne na Azumin dake gabatowa.

An yi musu jan hankalin hadin kai, su daina zagin juna, da kafirta juna. Sannan kowa yayi wa’azinsa ba tare da izgilanci ba, ko cin mutunci. Ka abinda Allah da manzan sa sukace, a tsage gsky komai dacinta. Malamai sunyi bayani, inda shima ismail yayi nasa bayanin, wanda ya gamsar da dukkan mahalarta taron. Sbd ismail, Allah ya hore masa hikimar iya magana. Shi mutum ne wanda zaiyi wahala yayi maka bayani baka gamsu ba.

Bayan an fito ne, ismail ya miqa hanya da nufin neman dan aca6an da zai kaishi gida, sa6anin sauran malaman da suka zo da motocinsu. Wannan dalilin shine ya kawo inda aka bincika cikin malaman da suka halarci taro, aka fidda guda hudu wadanda basuda abin hawa. Washegari saiga mota sabuwa dal, babu ko lamba an kawowa ismail.

Lokacin da Malam Aminu ya kirashi yazo, shiru yayi ya kasa magana, lokacin daya gabatar masa da motar. Bai san da wace kalma zai fara magana ba, duk wani alheri da zaizo masa ta gurin Malam Aminu yake tahowa. Yace Malam, Allah ya saka maka da aljanna. Sunyi ta murna. Ya kira mahmud. Dama mahmud ya iya mota. Nan suka shiga suka zagaya gari, tare da zuwa gurin abokan arziki. Sunje gidansu, inda ‘yan gidan suka fito suka ga mota sunata murna. Ta fito wanka , tana shafa, ummi ta shigo da gudu. “Aunty zo kiga motar kawunmu, sabuwa dal, baqa kuma qatuwa.

Mimi tayi dariya sbd yadda Ummi ta jero maganar, tare da cewa, Allah yasa alheri. Sai gashi da kansa, khadija kizo ki gani mana, munyi mota. Mimi ta miqe taje taga mota, kuma tayi murna. Yace ki shiga mana ko kin manta da yadda akeyin tuqi? Murmushi tayi, sannan ta amshi makulli, su Ummi suka shiga, ta tashi motar ta tuqa zuwa cikin layi, suka dawo. Ummi sai mamaki takeyi, tana cewa, anty yaushe kk koyi tuqa mota? Ismail ma cewa yayi ashe baki manta tuqin ba. Tace in manta tuqi? Ashe zan manta da yadda zanyi tafiya da qafata. Suka sa dariya.

Washegari Ismail da mahmud suka soma fita don koyo ma ismail tuqi. A yammacin ranar ismail, ya kira yaya Amina yace, su shirya zasuyi tasu walimar a gidansa. Bayan la’asar suka zo kwashi su yaya Amina, suka biya suka dauko Rabi’a da innarsu mahmud. Bayan sun kaisu ne, sai suka koma suka dauko su inna, dasu fatu.

Dukda ba wani alatu. Ismail ya zuba a gidanba, gidan yayi kyau sosai. Katifu ne a dakunan da sabbin zannuwan gado da fuloli, sai labulaye masu tsada. Sai falon ne ma ya gyarashi sosai, don tsadaddun kujeru ya zuba da kafet din tsakiyar, shi ma mai tsada ne, TV da sauran kayan kallon zamani. Sai dai falon saman bai saka komai ba. Yace sai ahankali zai saka komai. Mimi taga qorarinsa sosai, tunda tasan shi talaka ne. Sun je sun kawo musu abin sha na gora.

Daf da magriba suka koma kai su innarsa, sannan su yaya Amina. Mimi harda kuka wai abar mata Ummi. Yaya tace a’a za dai tazo miki hutu, kuma kinsan zata tayani aiki, ga makaranta. Mimi tace yaya baga saddam ba. Kuma indai makaranta ce ai zan kaita tunda ga mota a hannun kawunsu. Tace kiyi haquri har suyi hutu. Ismail dake kallonta burgeshi takeyi, don yanason shagwa6arnan tata. Shiyasa ma yaqi sa musu baki, don yanason kallonta a haka.

Ita kuwa yaya Amina, taqi barin Ummi ne don zamansu, su biyun wata  hikima ce, tana sa ran su shirya kansu. Sun barta da Rabi’a in sun dawo kaisu yaya, sai mahmud ya tafi da matarsa. Bayan tafiyar su ne, sai kuma suka shiga kicin don ganinsa. Freezer ce, sai tukwane da kuloli, plates da cokula, amma babu risho ko wani gas. Rabi’a tayi dariya, tace to da me zakuyi girki? Mimi tace oho masa. Suka koma sama sukayi sallah, sannan suka dawo qasa suna ‘yar hira.

Ranar Mimi harta dan saki jiki da Rabi’a, don ta lura Rabi’ar ta san me takeyi. Rabi’a tace, niko da ace zaki yarda da na baki shawara. Mimi tace, me zai hana? Rabi’a tace kar kibar wata mace ta shigo gidannan a matsayin matar malam ismail. Mimi ta tattaro hankalinta gurin Rabi’a. Ta yaya zanyi hakan? Nasan dai kinsan komai dake tsakaninmu da malam din, tunda Aminin mijinki ne.

Bafa son juna mukeyi ba. Rabi’a tace ni kuwa sai ina kallon so acan cikin qwayar idanunku. Na farko da baya sonki, da tuni ya sakeki. Rashin sakin jikinki shine ya hanashi nuna miki. Mimi tayi murmushi, ya fada miki ne? Rabi’a tace a’a nice nayi hasashen hakan. Mimi tace bana zaton zai soni, sbd na samu labarin yadda yakeson wata Zainabu. Rabi’a tace, tabbas yanason zainabu, amma da kinso, da tuni kin mantar dashi ita. Kiyi tunani. Mimi ta sauke ajiyar zuciya, ni damuwa ta ma ko auren namu yananan daram ko ya lalace? Oho.

Kafin Rabi’a tayi magana, sai gasu sunyi sallama. Don haka, sai suka rufe bakin hirar. Tare suka tafi dukkansu, aka kulle gidan. Mahmud ne ya jasu zuwa gidansu. Sun danyi hira, sannan Mimi ta jawosu zuwa gida. Ismail yaji dadin yadda Mimi ta saki jiki da Rabi’a. Bayan tayi wanka tayi isha’i, ta saka kayan varci, ya buga qofarta, taja hijabi ta saka, sannan tace, shigo mana.

Bakin katifa ya zauna, sannan yace kinga dan kayan dake kicin din ko? Sai a hankali zamu qara abinda bamuda shi. Tace maimakon kabar wani abin ka siyo gas ko risho, to dame zamuyi girkin? Ya zaro idanu, alamun sam ya manta da Risho. Sannan yayi dariya, lallai yau akeyinta. Sam na manta fa. Kinsan abubuwan da yawa, gashi ba wai inada kudin bane. Amma karki damu zuwa gobe ko risho dinne, sai in samo.

Gas daga baya zamu samu. Ina son ma ki zauna ki rubuta abinda muka fi buqata, sai muyi ta siya a hankali. Ki fara da wanda muka fi buqata. Tace mu bari saida safe. Yace rubuta dai ynxun. Ta dauko takarda da biro, shi kenan dame zamu fara? Yace kayan gado, sai falon sama, abubuwan cikin ban daki, sai me? Tayi dariya sannan ta soma tuno wasu tana fada, suna rubutawa. Sun kai kusan sha daya, kafin yace mata bari ya tafi saida safe.

Ya jima kafin yayi varci, sbd gsky haqurinsa zai gaza. Ko da bayason Mimi, to yasan yana muradinta a gefensa. Ballantana yana da tabbacin cewa wani sashe na zuciyarsa yanason Mimi. Duk lokacinda yazo da niyyar sanar da ita hakan, sauta 6ullo masa da zancen saki, sai dai wasu abubuwan da takeyi, sai yana zargin cewa tana sonshi.

Washegari da safe, yana zaune a falon qasa, yana duba wani littafi, ta sauko tayi wanka tasa daguwar riga ruwan qasa, mara nauyi, bata daura dankwali ba, ta kama gashin kanta a gefe. Tunda ta nufo shi ya kasa daina kallonta har tazo ta zauna akan kafet kusa dashi. Tace ina kwana? Yayi murmushi, “lafiya lau” kefa kina lfy? Tayi dan fari da ido ” qalau” ta gyara zama tace ynxun yaya zamuyi, tunda bamuda abinda zamu hura wuta?

Yayi murmushi. Fita zanyi in siyo mana abinda zamuci. Tace a’a kawai muje gdn yaya Amina muci. Yace kinsan yau dai ba zasuyi damu ba, amma bana siyo butar dafa ruwan zafi ba? Tace haba? Ni banganta ba. Ta miqe zamu dafa ruwan tea. Yace muje in gani, amma tabbas na siyo Butar ruwan zafi. Sun dafa ruwan zafinsu, suna sha, suna labari kadan-kadan. Daga bisani yayi wanka ya fita.

Ranar da suka cika kwana uku, Ismail yaji haqurinsa zai kasa. Don haka yaga babu abinda yafi illa ya ziyarci zainabu. Koda ya shawarci mahmud sai yace masa kar ya soma, ya dai yi qoqari ya sasanta da matarsa. Sam ismail zancen bai shigeshi ba, domin yasan tun filazal ba sonshi da Zainabun sukeyi ba. Don haka ya yanke shawarar kiranta a waya don ya fada mata cewa zai kawo mata ziyara. Misalin qarfe hudu bayan sun fito la’asar ya ciro wayarsa ya soma neman lambar zainabu.

Koda yazo kan lambar saida yadan jima yana tunani kafin ya danna kira ya tafi, lokacin zainabu tana kwance a qofar dakin innarta tana buga game din maciji, sai kawai taga kira ya shigo. Ganin sunan dake rawa akan fuskar wayar, saita zaro ido tare da murza idon, sannan ta dauka cikin sauri tare dayin sallama. Sun gaisa sannan yana ganin saqonta na gaisuwar juma’a kuma yana godia, tace ashe kana gani, nayi zaton ma baka gani tunda kuna hulda da jama’a sosai. Yace ina gani, ko zan sameki anjima? Cikin sauri tace, inanan Malam. Yace, qila in shigo anjima. Tace to Malam, Allah ya kawoka. Duk mahmud yana jinshi.

Misalin takwas da mintuna mimi tana daki tana danna wayarta, so take ta tsokani ismail tana kiranshi amma yaqi dagawa, sai kawai Mimi taga ya fito cikin shadda wagambari sai maiqo takeyi. Mai kalar blue, haka hularsa. Ta wundo ta hangoshi. Cikin sauri ta 6oye wayar sannan ta fito, ina kuma zakaje da darennan? Yace wata ‘yar unguwa zanje bazan jima ba. Tace inzo in raka ka? Ta fadi haka ne don ranta ya raya mata ko gurin wata zashi.

Yace a’a ki barshi ba ni kadai bane nida mahmud ne. Tace kasan dai inajin tsoro, don Allah karka zauna. Yace ynxun zan dawo. Tace amma bada mota zakaje ba? Yace da ita zanje mana. Nifa na tuqo motar daga unguwar su mahmud dazu, bare ynxun da babu cunkoso. Ta windon su na sama take leqensa ya fita da motar, sannan ya dawo ya rufe gidan, ta saki labule, ta koma ta zauna tana ta karanta wasiqar jaki. Yana isa gidansu zainabu, ya kira ta cikin waya ya fada mata ya iso.

Cikin soron gidansu suka zauna. Sun gaisa sannan ismail yace, gani nazo a karo na biyu, banda zuciya ko? Cikin sauri tace, malam kayi haquri, ko da ba laifina bane. Wlh ina sonka, shine ma dalilin da ban iya zama gidan Alhaji ba. Yayi murmushi, to ina fatan ba zan sake samun matsala ba, don wannan karon banason aja lokaci. Tace ni ko gobe ka turo, don dama zaman jiranka nikeyi. ‘yar dariya yayi, sannan yace shikenan ko ban sake zuwa akan lokaci ba zamu dinga waya.

Wasegari ya samu gayyata daga abuja, jami’ar da ya nemi koyarwa. Yaje kuma sun daukeshi, yayi murna sosai. Haka ma dangi sunyi murna, illa mimi kadai da take ganin cewa za suyi nisa da juna. Yayi mata tayin ziuwa abuja tace, ko sha’awar zuwa bataso. Yace, nasan ba zaki iya zama ke daya ba, yaya kk son ayi? Tace zan koma gidan su yaya Amina, in ka dawo sai in dawo. Da kanta tace, ya sakata islamiyya a unguwar su yaya. Sam in kaga Mimi ba zakace ita bace. Sbd dogon hijabi da niqabi.

Lecturing daya soma sai ya dauke hankalinsa daga kan batun auren daya so yi cikin gaggawa. Amma dai suna waya da zainabu. Duk sati yake zuwa, wani lokacin sati biyu. Shi mahmud ABU zaria ya samu. Ismai ya kira masu aiki sun duba filin dake gidansa sun tabbatar masa zai iya yin makaranta harda madaidaicin masallaci. Bayan sun bashi tsarin ginin, sai ya soma tunanin yadda zai samu kudin ginin don kudin da aka qiyasta makarantar zataci ba qanana bane.

Harkoki sun bude ma ismail, ga alherai da yake ta samu daga jama’a, domin ranar da akayi wata hira dashi a gidan TV na Africa, lokacin gidan TVn yana sabon budewa, har ya sako bayani akan makarantar da yakeson ginawa, ko sati ba’ayi ba, saiga shi mutane sun fara kiransa don son bashi gudunmuwa. Kafin wani lokaci tuni an soma gini. Babban qalubalenshi mata. Ko a makaranta, mata ne keta kawo mashi hari.

To don yana malami, shi kam ba waliyyi bane, da yawa ana jarabtar Malamai da son mata da kuma kudi, in bakayi taka tsantsan ba, sai ka fada halaka. Shi yasa ya gama yanke hukunci. Yana samun hutun qarshen zango yazo, to kuwa aure zaiyi, ko ma da wacece. Wata asabar ya dauki takardar da Mimi ta rubuta duk abinda suke buqata, ya shiga kasuwa, sai da yayi rabi, tun daga kan gado zuwa saurensu. Dakin mimi kuwa saida ya tsara mata shi fiye da nasa, sannan yayi mata sayayyar kayan sawa, sannan ga sabuwar waya da kuma layi, tsohon nasa ne ma ya bata. Don har ynxun baisan tanada waya ba.zainabu ma yayi mata ‘yar sayayya.

Bayan sunyi hutu, dukda cewa sati biyu ne hutun nasu, amma cikin sati biyun zai yaye ma kansa damuwa. Shiyasa ma washegari da safe yana zaune falon qasa yanashan tea, saida yaga itama tazo ta zauna , sai ya dauki wayarshi yana kiran layin zainabu, da farko hankalinta baya kansa, saida taji yace zainabu, cak ta tsaya ta kada hadiye tea din data kur6a. Yaci gaba ina gari zan shigo anjima yaudai zamu gama magana. Inason kafin hutunnan ya qare zaki zama a gidana. Cikin murna take fadin sai kazo. Yana kashe waya mimi ta maida tea din dake bakinta cikin kofin, sannan cikin wata irin murya tace magana zaku gama?

Ya dubeta fuska daure, “khadija aure zanyi” ji tayi tamkar ya soki zuciyarta da qaho. A hankali ta jingina da kujera, sannan ta lumshe ido, ta rasa me ma zatace. Sai kawai ta tashi ta nufi dakinta. Bakin gado ta zauna, rashin wanda zai baka shawara matsalane. Tasan tunda yace mata aure zaiyi, to kuwa yana nufin rabuwarsu tazo kenan. Wata zuciyar tace, lokaci yayi da zaki koma gidan iyayenki.

A fili tace, kai da saura. Haka zan koma musu bayan shekara uku, babu wani ci gaba, ba kuma auren da suka daura min, bayan tsohon laifina na baya? Ta girgiza kai, lokaci baiyi ba. Mafita ya kamata in nema. Ya turo qofarta ya shigo. Jikin sif dinta ya jingina. Khadija ban zaci zakiyi fushi ba, Nafi zaton zakiyi murna, don lokaci yayi da zan warware aurenmu.

Ta daga masa hannu. Don Allah ka fita! Inason inyi tunani. Yace inace kin gama tunani daga yau? Ta miqe, ta ra6a ta gefensa ta fita, qasa ta koma ta kwanta kan doguwar kujera. Murmushi yayi, sannan ya shiga dakinsa. Wayarshi ta gani da sauri ta dauka ta shiga kicin. Bata sha wahala gurin ganin sunan zainabu ba. Ta dauki lambarta. Sannan ta dawo da wayr inda ta dauka. Bayan ta shiga dakinta ma harda shiga bandaki. Layin zainabu ta kira, bayan ta daga mimi ta soma magana da kakkausar murya, “kece zainabu?” tace eh nice.

Dama na kiraki ne in fada miki cewa ki fita harkar mijina, in har kinason zaman lfy. Zainabu tace wai waye mijin naki? Mimi taja tsaki, “kinsanshi tunda har kina shirin aurensa. Zainabu tace, oh wai kina nufin malam? In shine sai ince kinyi kuskure. Domin aurensa shine abinda nake buri koda zaki zama ajalina. Ki sani kafin ya soki, ni ya soma so. Kuma ina sonshi, aure babu fashi! Mimi tace, mu zuba! Ni dake zanga wanda keda nasara! Ta kashe wayar, sannan ta fito daga ban dakin, ta jefa wayarta akan gado.

Ta shiga yin kai kawo a tsakar dakin. A fili take fadin, wai meyasa ni bana burgeshi ne? Dame zainabu ta fini ne? Ta janyo hijabinta da niqabi ta saka, sannan taja durowa ta dauki kudi ta nufi qasa. Bata zaci yana qasan ba. Saida taji yace, ina zaki? Ba tare da ta tsaya ba, tace gidan yana Amina. Ya daga murya. Ba zaki je ba. Ga waiwaya ta dubeshi, fuskarsa murtuk, sama ta koma fuuuu.

A zuciyarta da qudirin cewa shima kuwa sai tayi masa abinda ba zai fita anjima ba. Haka suka yini kowanne zuciya babu dadi. Da dare tanata fakonsa , ya shiga dakinsa yana tashi, sai kuwa ta sauka qasa , ta dauke masa makullin mota, ga jefa qasan kujera. Sannan ta kulle qofar falon ta saka makullin cikin rigar mamanta, sannan ta koma dakinta.

Tana kwance, rigingine kusan minti shabiyar, sai kurum taji turo qofarsa. Tashin da tayi da sauri shine ya kawo har yaji qaran makullin. Yace bani makullin mota dana qofar fita. Tace ajiya ka bani? Inama zakaje? Ni gsky tsoro nakeji, ba zaka fita ba. Yace, tadi zanje ki bani, karki 6atamin lokaci. Cikin 6acin rai tace, nifa bazan zauna ni daya ba. Yace to kizo muje tare. Da qarfi tace, Allah ya tsare ni.

Har inda take ya tako, daf da ita ya tsaya, ya sa hannu ya dafa kafadarta, girgiza ta yayi don yaji daga ina yaji qaran makullin. Amma sai baiji qaranba, sbd sun samu mazauni mai kyau a tsakiyar qirjinta, makari guda biyu sun taresu. Sai ya soma yi mata wani irin lalube tun daga qugunta yake shafawa da hannuwa guda biyu gaba da baya. Hakan ya kashe mata jiki, har ya tilasta mata lumshe ido, daga ita harshi. Haka nan yanajin makullin, sai ya zura hannunsa ta saman rigarta don ciro makullin. Ya ciro, amma yanayinsa gaba daya ya raunana, kamar yadda itama ta sukurkuce. Ta bude idanu ta kalleshi, shima fuskarta yake kallo.

Cikin ido suka kalli juna, sannan a hankali yace, saina dawo. Ta fahimci muryarsa ta canza. Kan gado ta fada ta soma kuka. Kusan minti biyar ta tashi ta rufe qofarta. Shi kansa baisan meya hanashi yin wani zance mai muhimmanci ba, aun daiyi ‘yar hira yace, zai dawo kan batun aurensu, yana sauri ne don matarsa ba tada lfy. Ta so ta fada masa  kiran da matar tasa tayi mata, sai kuma ta fasa. Lokacin da ya dawo, ya hau sama, kai tsaye qofar Mimi ya murda, amma sai ya jita gam.

Don haka sai ya wuce zuwa nasa dakin, bayan yayi duk abubuwan da yakanyi kafin ya kwanta, sai ya kwanta. Juyi kurum yakeyi tare da tuno yadda ya caje matar tasa. Ya gama yarda itama ko bata sonshi, to kuwa tana buqatarsa, don ya lura da halin data shiga a lokacin. Yanke shawara yayi ya tuntu6eta da batun, amma sai ta huce daga wanna  fushin da tayi. Da asubahi, kamar kullum saida ya qwanqwasa mata qofa kafin ya wuce masallaci. Ita kam tuni idanunta biyu, domin dai yau duk satar varci, saida yayi mata haquri.

Ta amince, baya sonta tunda har ta zubarda kimarta ta 6oye makulli, amma saida ya dauka kuma ya tafi. Zucigarta dai tanata bata shawara akan ta fito fili ta fada masa abinda ke ranta. Sai dai ita tsoronta kar sai yaji sirrin zuciyarta, sannan yace, ba irinta yakeso ba, kamar yadda yayi ta fadi a baya. Takaici ne ya hanata fitowa daga daki. Koda gari ya waye, shi kuwa shareta yayi, har ya gama komai ya fita, sai dai alamu sun nuna bata bude qofar ba, har ynxun qarfe hudun yamma.

Yaje ya daga labulen windonta, tana kwance akan sallaya, da alamu tayi la’asar ne. Yace khadija, ki tashi ki bude qofa mana! Tana jinsa tayi shiru, daman so takeyi ya lallasheta, amma ko zata bude ba ynxu ba. Yace kinci wani abu ne? Bata tanka ba. Ya sauka qasa. Baisan me yarinyarnan keso dashi ba. Yau duk ta hana rayuwarsa sukuni, don koda ya fita, hankalinsa yana gida. Baisan mimi da gske takeyi ba saida yaga anyi sallar isha’i ya dawo bata fito ba. Da ya leqa ya ganta kwance rub da ciki akan gado.

Yace kadija ki dubi girman Allah ki bude, muyi magana. Nifa bansan dalilinki ba. Hava khadija ya kk so inyi da rayuwa ta. Ganin bata tanka shi ba, sai ya yanke shawarar kiran mahmud. Kafin isowar mahmud din, ismail yaci gaba da lallashinta, amma ko motsi batayi ba. Bataji takun shigowar mahmud ba, sai dai muryarsa taji yana cewa, don Allah khadija ki bude qofar nan, muyi magana. 

Don Allah zaki bude ba don ni ba. Kuma ina bayanki akan kowane dalili ne yasa kika rufe qofar. Sunfi minti biyar kafin ta taso ta bude, tana layi. Cikin hanzari ismail ya shiga ya kama hannunta. Dukda qaton hijabin sallar data saka ya hada, ya dauke ta zuwa falon qasa. Yunwa da damuwa sun hadu sun ramar da ita. Ya zaunar da ita akan kujera. Yace haba khadija kowane irin laifi nayi miki, ya dace ki yanke ma kanki irin wannan hukuncin?

Cikin raunanniyar murya tace, ku barni don Allah. Mahmud yace, ka kawo mata ruwan zafi, tunda bataci komai ba, hanjinta zai warware. Ya nufi kicin ya hado mata ruwan zafi. Saida yayi ta lallashinta, sannan ta amsa tanasha. Kafin tayi rabin kofi, zufa ta rufe ta. Sannan taji qarfi a jikinta. Ta kama gefen hijabinta tana sharewa. Mahmud ya dubeta khadija bai dace kiyi irin wannan ba. Horon kanki da yunwa, wannan ba dabi’ar musulmi na gari bane. Ismail yace mema akayi mata ne?

Taqi bani dama in nuna mata muhimmancinta. Kullum zancenta daya ne in saketa. Nace mata in nayi aure zanyi mata abinda takeso, kuma ynxu na soma neman aure. Sai tazo tanayin irin wannan? Sai kawai sukaji muryarta tace, duk wadda zaka aura, ka aura amma banda zainabu. Cikin sauri ya miqe, sbd me zakice haka? To ai wannan ba huruminki bane. Wadda zan aura sai kin za6a min, sai kace uwata? Ok, na gane nufinki, wato tunda baki sona kar wadda ta soni ko?

To na gaji da wannan mulkin naki. Kuka ta soma, tare da fadin dole ka barta, kamar yadda dole tasa na haqura da khalil. Yace in ba haka ba fa? Tace za kayi da ka sani. Mahmud dake kallonsj, bai katsesu ba, sai yayi murmushi. “Da ace zaku fito da abinda ke zukatanku, wlh da kun huta. Sukayi shiru. Yace shikenan zainabu an bar maganarta. Zai canza wata. Haka yayi miki? Tace eh.

Comment(1)

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *