Kannywood Post: Rahama Sadau ta bada labarin yadda ta rasa budurcin ta

Kannywood Post: Rahama Sadau ta bada labarin yadda ta rasa budurcin ta

Kannywood Post: Rahama Sadau ta bada labarin yadda ta rasa budurcin ta

0
0

Sanannar jarumar nan da ta shahara a a masana’antar shirya fina-finan Hausa na Kannywood da ma na kudancin kasar Najeriya watau Rahma Sadau ta bayyana yadda akayi ta rasa budurcin ta kamar dai yadda ta taba shelantawa a watannin baya.

Jarumar wadda yar asalin garin Kaduna ce ta dai ta yi wannan karin haske ne yayin da take zantawa da wakilin majiyar mu ta Mujallar fim a satin da ya gabata.

Firar ta ta dai tana zaman ta farko ce tun bayan data dawo daga kasar Turkiyya inda taje ta shafe kimanin watanni uku tana karatu.

katsinaposthausa.com haka zalika dai ta samu cewa jarumar ta bayyana cewa maganar da tayi a watannin bayan na cewa ita ba cikakkiyar budurwa bace sannan ta kuma kara jaddada cewa l ba ta taba zina ba tun da Allah ya halicce ta.

Jarumar ta kara da cewa abunda take so ta fadawa duniya shine an taba yi mata fyade ne sadda tana yarinya karama kuma a lokacin ne ma ta rasa budurcin na ta kamar dai yadda ta fada.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa muhawara ta zafafa a watannin baya lokacin da jarumar ta bayar da ansa ga wani masoyin ta da ya tambayeta matsayin budurcin ta a kafar sadarwar zamani ta Instagram inda ta ba shi ansa da cewar ita ba cikakkiyar budurwa bace.

Wannan ikirarin na ta dai ya dauki hankali sosai inda jama’a da dama ke ganin bai kamata jarumar ta fadi haka ba duniya ta sani.

 

Ko ya kuke kallon wannan lamarin?

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *