CANJIN RAYUWA [Kashi na Hudu] Tare da Halima K. Mashi (Shafi na 91 – 100)

CANJIN RAYUWA [Kashi na Hudu] Tare da Halima K. Mashi (Shafi na 91 – 100)

CANJIN RAYUWA [Kashi na Hudu] Tare da Halima K. Mashi (Shafi na 91 – 100)

0
0

Ismail zaiyi wata magana mahmud ya daga masa hannu, tare da fadin an wuce wannan. Ka samu Malam, akwai wani sanata faruk da ya samu malam da maganar ‘yarsa. Banji dai kan zancen ba, amma tabbas naji malam yace mutumin ya baka ‘yarsa. Ismail yace, Hanan umar faruk kenan.

Nasan yarinyar daliba ta ce a Abuja. Tanan kuma ta biyo? Mahmud yace bakamin zancenta ba. ismail yace banida ra’ayin auren  yaran masu kudinnan, amma tana da hankali. To in anyi haka ya zanyi da zainabu? Banyi mata adalci ba. Duk zantukan da zukeyi, mimi mutuwar zaune tayi. Sai alokacin ta gane ba wai zainabu kawai take kishi ba. Duk matan duniya takeyin kishi dasu akan mijinta. Saidai ba tada ikon cewa komai akan wannan. Sun juya harshensu zuwa larabci, inda ismail ke qorafin ba’ayi ma zainabu adalci ba.

Mahmud yace kafin kayi masu, sune suka fara yi maka. Sannan yarinyarnan tana matuqar sonka. Ina mamaki da kullum kuna tare, amma ni na gane hakan, kai ka kasa. Ismail yace nima inaso in fahimci hakan, sai tayi ta maganar saki, saki. Shiyasa naga kawai in haqura. Yace to ka gwada mana, zaka iya ganewa ta hanyar ta6a jikinta. Mahmud kaqi yarda cewa kana sonta. Alhalin shine dalilin daya hana ka daketa. In kaqi yarda dani ynxun, zaka yarda dani a gaba.

Mahmud ya miqe, tare da cewa, bari inje gida nima, kar Rabi’a ta kullemin qofa. Ismail ya kalli mimi, ya tausasa murya, ina makullin motar in saukeshi a gida? Ta kalli kujerar da suke kai, tana qasan nan. Suka ciro suna dariya. Ismail yace babu irin leqen qasan kujerar nan da banyi ba, ashe yana ciki. Sai daya miqe mahmud yace, dama saboda ta nuna makullin nayi shiru, amma da mashin nazo.

Bayan ya rakashi ya tafi, shi kuma ya kulle gida, ya kulle qofa. Har lokacin mimi tana zaune anan, amma ta zurfafa a tunani. Wacece Hanan? Ya zauna kusa da ita, “khadija hakan yayi miki ko? Ta kalleshi firgigit, batasan ma yazo kusa da ita ba, ta sauke ajiyar zuciya, “wai itama Hanan din kana sonta? Yace ban sani ba, sai naje na ganta sosai. Ya kalli cikin idanunta data tsareshi dasu. Kishi ya gani qarara a ciki. Tace, itafa tana sknka? Yace gsky tana sona, domin ta nuna min alamu. Tace, dama kana iya gane alamun mace, tana sonka?

Yace, sosai kuwa. A ranta tace, to baka qware a wannan fannin ba, tunda ka kasa gane irin wanda nakeyi maka. A fili sai tace, tanada irin kyawun da kake so kenan? Yace banyi mata kallon qurilla ba. Ya rufe wannan da cewa, yau kin tsorata ni. Don Allah karki sake yi min haka kinji? Kallonsa kawai Mimi keyi, amma ita tamaicinta yafi tunaninsa. Ta miqe, bari inje in kwanta. Yace duk yinin da kikayi a gado a kwance baki gaji ba? Tace, karka damu bana gajiya da varci kai ka sani. Ya bita da kallo, damuwarta tana matuqar damunsa. Ya miqe shima yabi bayanta.

Tana fitowa ban daki ta ganshi zaune a bakin gadonta. “Lafiya?” ta jefo masa tambaya. Yace, babu inda yake miki ciwo? Ta girgiza kai, a’a yace naga kina cikin damuwa ne har ynxun. In dai maganar zainabu ne ki dauka ya zama tarihi. Tace kaje ka kwanta kawai, ya wuce nima. Ya miqe ya nufi fita, sai kuma idanunsa suka hango wayarta dake kan madubi. Yace waccan wayarfa? Tare suka isa gurin, ya rigata dauka. Cikin sa’a ta amshe, tare da cewa, wayata ce bani. Yace shine baki ta6a kirana ba? Tace, ni bana kira da ita, sai dai inajin rediyo. Yace shikena  saida safe.

Ya jima yana kai-kawo a dakinsa, zai tattara alamomin so da mimi take nuna masa, to me zai hana ta fada masa? Kuma meya kawo ta dinga batun saki? Wata zuciyar tace kaima ya kamata ka tantance kanka, shin kana sonta ne? Ko tausayinta kk ji? Ko ko sbaquwa ce? Can qasan zjciyarsa sai yaji an amsa da cewa duka ka hada.

A fili yace, khadija! Babu batun saki. Ko da baki sona, balle zan gwada ki in gani. Washegari da safe, tana kicin tana hada masu abin karyawa, ya shigo cikin rashin walwala, ta kalleshi, “barka da safiya? Yace barkanmu. Ya kusanto ta, “bar ynxun baki huce ba Dija? Ko itama Hanan din baki sonta ne? Ta kalleshi, sannan ta ta6a baki. “in kai kana sonta, me ya shafi khadija? Yace Allah in bata miki ba, sai in fasa. Ta zaro ido, ni asuwa dan wake a hotel? Yace da gske nakeyi, amma in zaki yarda da wani sharadi guda daya.

Tayi ‘yar dariya, “inji sharadin. Yace zan turo miki a message. Sai ki bani amsa. Tace, sbikenan ina jira. Ta dauki tiren da abicin karin su, muje mu karya. Ya lura da yadda ta saki ranta daga yin wannan ‘yar maganar. Suna karyawa, kowa da tunaninsa. Bayan sun gama ya miqe bari in fita. Tace Allah ya tsare. In ka shigo anjima zanje na wanke gashi na. Yace ki bari na kaiki da dare. Da mimi taji alamun shigar saqo a wayarta, sai ta duba, sai taga MTN ne. Kusan biyar na yamma ya dawo. Tayi kwalliya cikin riga da siket na atamfa. Ta yi masa sannu da zuwa.

Ledojin daya shigo dasu ta amsa ta nufi kicin. Ya biyo ta a baya, kin jini shiru ban dawo ba? Tace nasanka da uzuri ai. Daidai lokacin ta bude ledar, kaji ne guda hudu, sai dayar kuma danyen kifi. Ta soma zubawa a freezer, tana cewa farfesun kifi zamu sha anjima kenan? Yace naje sai miki kifin, sai ga wani bawan Allah. Sai kawai ya biya, Kuma yasa asa min kaji. Shiyasa kk ga bana son yin siyayya a unguwar da aka sanni. Sai kawai wani yace zai biya. Tace, arziki ne hakan ma.

Yace bari inje inyi wanka, zamu fita da ismail. Gabanta ya fadi. Ina kuma zaku je malam? Ya dubeta, gidansu Hanan. Ta rufe freezer, sannan ta biyoshi, to ba ka fadi sharadinka ba. Ko dama kana yi min wasa ne? Yace oh na manta. Ina zuwa. Ya shiga dakinsa, bakin gado ya zauna. Ya rubuta cewa, “in kin yarda in sumbaci bakinki sau daya kullum, to zan haqura da Hanan. Idanu ta zaro, tana qara maimaita abin da ta karanta. Sai taji tanajin kunyar bashi amsa, amma tunda ya ta6a bata amsa da cewa shiru alamu ne, to tayi shiru. Baiga amsa ba. Don haka yayi shirinsa na fita. Ba wani gidansu Hanan zasu ba, don dai ya gwada tane. Rashin ganin amsarta, sai ya zata ko batayi na’am ba, don haka, sai ya shareta. Ita kuwa tanajin fitarsa, amma kunya ta hanata fitowa.

Har washegari ba suyi batun ba, duk da sunci abincin dare tare, daren ranar qananan kaya yasa, abinda bata ta6a ganinsa da su ba. Ta kasa daina kallonsa don burgeta da yayi. Sam baiyi niyyar fita ba, kuma dama ya siyo qananan kaya ne don ya burgeta. Amma sai yayi nufin gwada ta. Ya dauki makullin mota zai fita, da sauri tace, ina zaka? Yace, khadija ya kamata ki daina tambayata in zan fita kamar wannan lokacin tunda kinsan komai. Ya kusa kai bakin qofa ta rasa me zatayi, sai kawai ta riqe ciki, “wash Allah na cikin! Ya waiwayo da sauri, yasan cewa qarya tayi, amma sai ya biye mata.

Ya riqeta, ya kwantar da ita a cinyarsa, yaja rigarta sama kadan, ya soma yi mata addu’a yana shafa mata a cikin. Lamo tayi cike da burin dama su kwana a haka. Can yace, kinji sauqi? Tace eh, amma kar ka fita. Yace shikenan na bari sai gobe. Tuni Hajiya taba Alhaji shawara akan su miqa ma minista jikansa, sbd dalilinta data fada masa cewa, mutuncinka zai zube a idon jama’a, in kayi la’akari da cewa Abbas shine ubansa. Gashi ‘yan jarida sunata bin shari’ar, ana ta yada ku a media. Yace shikenan. Da kansa yaje Abuja, ya kira Abbas yace ya zo ya dauki dansa.

Sai dai sati biyu da daukar yaron ya farka da ciwan kunne. Sun kaishi Asibiti sun dubashi, sun basu gado. Kafin yamma ashe ciwon ajali ne, sai kuwa yace ga garinku nan. Hankalin ko wane 6angare ya tasbi. Na’ima kuwa kamar zatayi hauka. Amma dole suka dangana. Allah ya raba musu gardama. Abbas ya tura ma Na’ima saqon sakinta. Bayan watanni kuma sai ta nemi jami’a anan Abuja ta samu ta shiga, amma duk ta rame. Yanxun burinta taga mimi ta nemi gafara. Momy Nafisa kuwa tafi Na’ima da na sani. Hasana da Husaina sun sama mazaje, suna shekararsu ta biyu a jami’ar ‘yar adua. Usaina, Abokin yaya mukhtar, kaduna yake.

Ita kuma Hasana, Lecturer ne na makarantarsu, amma dan Gusau ne. An basu, amma sai sun qare karatu sannan za’ayi bikin. Shi yasa suka matsawa Hajiya sauda kan don Allah suna son abarsu suje gurin Sis mimi tunda an fada musu unguwar da take. Sun san Gidan ma. Hajiya sauda tace, susa  ransu a inuwa daddyn sh ma yace, in ya dawo daga ganin likita a England zamuje gidan gaba dayanmu. Suka dauki murna. Burinsu dai ynxun daddy ya dawo.

Mimi kuwa tunda malam ya fita da safe take tunanin wane irin lambon da zatayi in dare yayi don kar ismail ya fita zuwa gidansu Hanan. Wanka tayi, taci kwalliya sosai, da riga da wando masu dame jiki. Ya shigo bayan la’asar. Tana kallonsa  yayi ta satar kallonta, lokacin da yakecin abinci. Bayan ya dawo sallar isha’i, yayi kwalliya da qananan kaya, jeans ne baqi sai farar T-shirt mai gajeran hannu. Gaban rigar an rubuta, da harshen turanci cewa ina Alfahari kasancewa ta musulmi. Lokacin itama ta canza kayanta zuwa doguwar riga irin mai rawa dinnan ta kama gashin kanta a tsakiya. Da makullinsa a hannu ya fito, ta dubeshi, “sai ina kuma yau? Jiya ban samu zuwa gurin hanan ba, kuma na fada mata, kinga ai ya dace yau inje ko? Tayi shiru tana kallonshi.

Yace sai na dawo, har ya fita daga falon, sai ta bishi, “Malam! Ya tsaya. Sannan ya waiwayo, menene kuma? Tace kalli garinnan hadari ne, kasan kuma ana fara ruwa Nefa zasu dauke wu, kuma inajin tsoro. Ya kalli sararin samaniya, tabbas hadari ne. Yace, zan dawo kafin ruwa ya sakko, wadannan qananan kayan na siyosu ne don ita. Biyu ne kacal, jiya nasa daya, yau ma gashi nasa dayan. In na bari sai gobe me zan sa? Kuma in banje ba, na zama qaramin mutum. Jiya nace, ganinan banzo ba, yauma haka? Ko zamu tare? Shiru tayi masa.

Har ya kai gurin motar, guguwar hadarin ta taso. Da sassarfa ta nufeshi, “kazo ka koyamin karatu mana, wai ba ka bani sharadi ba, kuma na Amince? Ya lumshe ido don dadi. Ya juyo, “amma baki fadamin ba, kuma baki turamin message ba. Tace, to ba kace min shiru alamun eh bane? Ya kai hannu ya kamo tafin hannunta, ni kuma sai nayi zaton baki harda bane. Ya fizgo ta da qarfi ta fado qirjinsa, a kunne ya rada mata, tunda kin amince, bari in fara ynxu. Dumin sautin muryarsa a kunnenta, yasa tsigar jikinta tashi.

Tafin hannunsa guda biyu yasa, ya lalubo fuskarta. Ya sa bakinsa ya sumbaci le6unanta. Ta zata shi kenan, sai kawai taga ya saka harshensa ya bude mata le6e. Wata kalar sumba yake mata. Kafin minti biyu, ta rasa duk wani kuzarinta. Jin cewa zata zube ne, sai ya jingina ta jikin motar. Saukar ruwan saman bai sashi barinta ba, sai da tace, Ma..lam ru..wa! Cak ya dauketa zuwa cikin falonsu, duk sun jiqe.

Kan kujera ya shinfide ta. Sannan yaje ya rufe falon. Har lokacin tananan lamo babu kuzari. Ya dubeta, muryarsa a dushe, “tashi muje ki kwanta. Sai kuma na gobe ko? Ya lura ba zata iya hanzari ba. Don haka ya riqe mata hannu, har bakin qofa ya kaita yace, saida safe.

“Lamo tayi akan gado tare da maqale filo, idanunta rufe tana tuna abinda ya faru. Ta kasa tashi ta cire rigarta data soma jiqewa. Shi kansa Malam din juyi kurum yakeyi akan gado. Qarshe dai ya gano mafitarsa daya ce, ya watsa ruwa. Yafi minti biyar ruwan sanyi yana sauka daga tsakiyar kansa zuwa tafin kafarsa. Tsigar jikinsa data tashi ce yasa yasan cewa da akwai matsala. Ya fito kafin yayi wani yunquri har zazza6i ya rufeshi.

Singileti da gajeran wando ya saka, sannan ya qudundune da zanin gado. Haka ya kwana. Lura da Mimi tayi yau Malam bai buga mata qofa ba shine yasa data idar da sallah ta nufi dakinsa. Tana turawa ta sameshi yana kakkarwa. Cikin sauri tace, malam lfy? Ta zauna a bakin gadon. Tanason takai hannu ta ta6a wuyansa kuma ta kasa. “In kawo maka magani? Bai iya amsawa ba. Da sauri ta sauka ta dauko panadol da ruwa. Da qyar ya tashi zaune, ya amsa ya sha, sannan yace, “rufamin bargo.” ta janyo bargo ta rufa masa, sannan ta zabga tagumi tana yi masa sannu.

Kusan minti shabiyar sannan ya ture bargon, zufa ta soma zubo masa. Tace mura ce ko? In dafo maka ruwan zafi? Tea yace eh, bari inyi sallah. Ya shiga bandaki ita kuma ta sauka kicin. Kan sallaya ta sameshi, ta zauna itama ta aje tiren a gabansa, sannan ta tambayeshi, tun yaushe ne bashida lfy? Ya kalli cikin idonta, kece kika zama silar ciwo na. Ta zaro ido, cikin shagwa6a tace, da nayi me? Ya kusanto kunnenta sosai yayi mata rada.

Ni dai banji me yace ba, naga dai ta sunne kai a cinya, tare da fadin “kai Malam!” shi kuma yasa dariya. Murmushi nayi don salon soyayyarsu yayi matuqar burgeni. Ranar haka ya yini bai fita ba, wai yana jinya. Ko sallah shine yayi ta musu jam’i. Yayin da mimi tayi ta JI dashi.

Bayan sallar isha’i ne ta leqo don yi masa sai da safe, “yau baki amshi karatun ba” Tace wane karatu? Yace, kin manta ne? Jiya fa kk ce in dinga koya miki karatu. Tace ai jiya ne kawai nace.

Yace, naga alamun kin manta da karatun da nike nufi. Zokiji, ta zauna a gabansa yana kan sallaya. Jallabiya ce, a jikinsa mai ruwan qasa, kuma mai gajeran hannu. Ta lura yayi wanka ne bayan fitarta. Ya matso da bakinsa kunnenta, abinda ta zata shine ya fada mata. Ta zata ya manta, domin tana sane ita, kuma tana ra’ayi. Don haka zama ta gyara. Ya tallafe fuskarta suka kalli juna a cikin ido. A hankali yake magana. “INA SONKI KHADIJA…” Wani dadi taji ya rufeta.

Har ma ta lumshe ido, lokacin ne ya saukar da la66ansa akan nata. Sai da ta koma tamkar ba tada rai sannan ya barta, don in yace, zai wuce gona da iri ma ya lura ba zata hana ba. Amma yanason koya mata komai daki-daki. Don sai ya raina wayewar da take iqirarin tayi. Domin ya lura batasan komai ba a wannan karatun.

Rana ta uku ne ta soma biya karatun daya koya mata. Don haka a dare na hudu, sai yace, suyi wata sallah raka’a biyu. Bayan sun idar ne, ya dubeta, “kin san sallar nan da mukayi ta mecece?” ta girgiza kai, yace ta ma’aurata ce. Yau karatunmu zai canza salo. Kije kisa turare a duk ga6o6in jikinki kizo. Sam bata iya yi masa gardama ynxun, ko menene dalili? Oho! Tabbas yau sabon darasi ne, sai da karatun yayi nisa, sannan ya rada mata a kunne, “in barki haka ko?

Tace, da wuya? Yace ba zan bari kisha wuya ba, sbd naga ke budurwa ce har ynxu. Idanuna ba zasu iya kallonsu ba. Don haka na tura qofa a hankali na fita don barin ma’aurata da sirrinsu. Saidai daga bakin qofa nake jiyo ismail yana karanta addu’ar da mazaje na qwarai sukeyi lokacin kusantar iyalinsu. A fili nace, “an kashe Boss kenan.” ban koma dakin ba saida na kusan awa biyu. Lokacin dana leqa ban gansu ba .

A raina nace, suna bandaki. Ina nan la6e suka fito. Ya kwantar da ita, shi kuma ya shimfida sallaya. Nace su mimi Amaren asali, kin kai masa mutunci. Shi kuwa sallar godia ce ga Allah yayi. Da asubahi mimi batayi ragwanta ba, tashi tayi ta nufi dakinta don yin sallah. Bayan ta idar, ta kwanta a gadonta, tana tuna abinda ya faru jiya. Gsky Malam ya wuce da tunaninta. Mamakin sa kawai takeyi, dama zata iya tambayarsa, da tace, ina ya koyi salon sa mace ta manta da duniyar da take? Sai dai kashh, tanajin kunyarsa. Barci yayi gaba da ita.

Ismail daga masallaci dakinta ya nufa ya kwanta bayanta ya rufesu. Barci sukeyi tamkar wasu taurari. Naso in musu hoto. Sai tara saura ya tashi. Shine ya hada musu abin kari. Lokacin daya dawo saman tana wanka. Ya tsaya jikin bayin, “inzo in taya ki? Tace na gama. Ta fito ta kasa kallonsa. Yana zaune ta gama shiri, harda taya ta gyara gashin kanta. Suka nufi qasa don yin karin kumallo.

Cikin sati dai ismail baya nisa, launukan karatun da yake koya ma amaryar tashi kam babu dama. Itama batason yayi nisa, shiyasa ma ta yanke a ranta in zai koma Abuja ba zai barta ba. Haka kuwa hutunsa yana qarewa, tace, Malami na zaka dani? Yace dama izininki zan nema. In kinji zuwa daya kenan. Da ma kema ki soma karatunki. Tace amma zan canza layi. Islamic zan karanta, don sai ynxu na fahimci Musulunci yazo da komai na wayewa.

Sam ismail ya manta da wata zainabu, khadija ce a gabansa, wadda yake kira my Dija. Kafin wani lokaci, mimi tayi kyau, ta goge.

Da kanta tace, ismail ashe na jima ina cutarmu. Kuma ka san na dade ina sonka? Yace, na gano haka tun ranar dana saci wayarki na bincika sai naga ashe kece matar dake ta damuna a wtsapp. Tayi dariya, shine baka fadamin ba? Yace gashi ynxun na fada. Yaya Amina kuwa tunda taga Mimi, tasan an kashe boss, domin ta  ciko masha Allahu. Sam Na’ima basu ta6a haduwa da mimi ba, ko don ba department daya suke ba, oho.

Lokacin da Alhaji ya dawo daga ingila, sai ya samu labarin Mimi suna Abuja kuma tana karatu. Yaji dadin haka, kuma ya jinjina wa malam ismail. Shima ismail ynxun abu daya ya rage masa, shine ya sada Mimi da iyayenta. Amma ya bari sai sunje katsina. Cikin haka, Mimi ta soma laulayi. Ta ga gata ganin idonta. Har da kanta ta darsa a ranta cewa data bar ismail, da ta tafka asarar da ba zata iya maida ta ba. Kullum tayi sallah, sai ta godewa Allah, ta kuma godewa mahaifinta daya za6a mata ismail, ta samu CANJIN RAYUWA.

Cikinta wata bakwai sukazo katsina, domin za’a bude makarantarsa, kuma zaya kai Mimi gidansu. Bayan an gama kai kawon bude makaranta, da sati daya, tuni ma an soma karantarwa. Ya danqa komai gurin wani bawan Allah dake nan unguwarsu malam Aminu. Shine ma ya kawo shi, yace tunda Ismail baya zama. Sai ismail ya amince, don yasan malam ba zai kawo musu bara gurbi ba. Kuma ya zuba qwararrun malamai a makarantar. Safiyar juma’a, Mimi tana kwance kan cinyar ismail, yace muje in taimaka miki kiyi wanka , zamu fita.

Tace zuwa ina malamina? Yace inda muka kwana biyu bamuje ba. Kinsan falalar zumunci. Gashi ke nake jira ki haihu, zamu tafi Madina don neman digiri dina na biyu. Bayan ta fito tana zaune, ya shafa mata mai, sannan yace, wane kaya zamu sa? Tace ka san dai yau juma’a, kuma kamar yadda muka tsara ma kanmu rana ce ta saka kayanmu na al’ada. Dubamin shadda ko atamfa. Sabbin riga da zani ya fito mata dasu na super mai kalar popple, sai ratsin baqi, har da sarqa da dan kunne masu kyau yasa mata. Shima ya shirya tsaf, cikin shadda sabuwa.

Tasha hijabi da niqabi, suka shiga sabuwar motar da yayi kakara, ya canza. Saida sukayi tsarabar kayan sha, dana zaqi, sannan ya tuqa su zuwa unguwar. Sam Mimi bata fahimci inda suka dosa ba, sakamakon an samu canje-canjen gine-gine. Wani gurin ma babu gini da. Ko gidansu, saida suka shiga ta ganeshi, sakamakon an canza gaban. Ta kalli ismail, “yaya zaka yi min haka? Gsky mu juya, tunda ba wanda ya ganmu.

Yace ni ba wannan ya dameni ba. Baki lura da yawan motocin da ke harabar gidannan ba? Sannan ga mutane can ansa rumfa. Da  alamun anayin wani abu agidannan. Kai tsaye tace, Allah dai yasa ba daddynh bane ya rasu. Sai kuma ta bude qofar da sauri, ta fito. Shima ya fito, ya riqeta. Yi sannu My Dija. Babu abinda ya faru, sai alheri. Alhajin ne suka fito daga falonsa tare da qaninsa kawu shafi’u da kuma su Alh kabiru, da Alh isah.

Ismail yace, to ga  Alhajin nan ma. Da sauri ta nufesu tana fadin daddynah! Cak ya tsaya domin ko cikin mjrya dubu zai fidda ta Miminsa, ko da zai shekara dubu bai ganta ba. Cikin sauri yaje ya daga niqaabinta. Kamar yadda ya zata Miminsa ce. Yace, uwata. Idanunta suka kawo hawaye, na’am daddy. Sai ya rungume ta, idanunsa suna masu kawo hawayen farin ciki.

Ya kalli Alhaji kabiru. “yanxun fa mukeyin maganarta. Ance min kunzo gari. Ina jira a gama hayaniyar biki, muje gidan. Tace daddy wa ke aure? Yace ‘yan biyu, sai mukhtar. Tace nazo a sa’a. Ta kalli mijinta wanda ke kallonsu cikin tausayi, tace Malam baka gaida su daddy ba. Ya qaraso tare da cewa, na jira ne ku numfasa. Nan suka gaisa suka nufi ciki. Shi dai Alhaji nan ya juya shima yabar abokansa da qaninsa. Falonsa ya yace ismail ya shiga. Ita kuma ta rufe niqabinta. Alhajin ya tasa ta suka nufi ciki.

Hajiya sauda tana gaisawa da wasu baqi da suka shigo, Alhajin ga shigo yana kwada mata kira, tace Alhajina ho! Yau dai gidanmu da jama’a… Ya katseta, baquwa kikayi. Ta kalli Mimi fuska rufe, tace to ta shigo daga ina? Mimi taje ta rungume mahaiyarta. Sannan ta daga niqabi. Da sauri tace, Mimi ce! Nan dai akayi ta murnar ganin Mimi. Amare suna gidan mai musu gyaran jiki. Da yake sai washegari Asabar ne za’a daura auren. Hajiya da kanta ta kirasu ta fada musu, sai gasu.

Murna tamkar zu cinye ta. An kawo mata wannan da wancan duk an jibge mata, sai dai hankalinta yana can gurin mijinta. Hajiya sauda tasa ta gaba, tana cewa, in bakison wannan me zakici? Saboda kowa yaga tsohon cikinta. Ta kalli Hasana, “wai ina Malam ne, ko suna gare da daddy? Hajiya sauda tayi murmushi, yana tare dasu daddynku, harda sy yayanku. Sannan Mimi ta soma  tsakurar abincin don batajin yunwa, kuma ta saba ci da Mijinta.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *