YANDA TARON RANAR MARUBUTAN HAUSA NA DUNIYA YA WAKANA A KATSINA

YANDA TARON RANAR MARUBUTAN HAUSA NA DUNIYA YA WAKANA A KATSINA

YANDA TARON RANAR MARUBUTAN HAUSA NA DUNIYA YA WAKANA A KATSINA

0
0

Kungiyar Marubutan Hausa ta gabatar da Taron tan a Duniya a katsina,wanda aka samu halartar muatane da dama ciki da wajen kasar nan.Dama dai hausawa kan ce kome nisan dare gari zai waye.taro dai an riga an yi shi, ya wuce koda yake dai ba zaa rasa yan korafe korafe ba, nan da can, wasu daga ciki na gaskiya ne, wasu kuma irin wadanda aka san dan Adam da su ne wadanda basu da tushe .

NASARORIN DA TARON YA SAMU 

Mutane da dama suna ganin,taron ya samu wadansu nasarori kamar haka Yadda wani wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya fada:-

“ Nasara ta farko ita ce duk bakin mu da suka taho daga wurare daban daban sun iso lafiya cikin yardar Allah ba mu samu labarin wani ko wasu ya samu wata matsala a hanya ba, haka kuma muna fata Allah cikin ikon sa, da kaddarawar sa, ya mayar mana da kowa gidan sa lafiya .

“Nasara ta biyu da taron ya samu ita ce haduwar dunbin masana masu tarin yawa daga bangarori daban daban, musaman farfesa ABDULKADIR DANGANBO, FARFESA IBRAHIM  MALUMFASHI, FARFESA ALIYU MUHAMMAD BUNZA, da dai sauran manyan masana da suka hallara . Lallai tara wadannan a wuri guda ba karamin alamari bane .

Nasara ta uku da taron ya samu, ita ce ta amsa kiran da dumbin marubuta daga ko ina suka yi, su ka halarci wannan taro mazan su da matan su, manyan da kanana, babban abunda ya fi burgeni shi ne, samun damar halartar da iyayen mu su DANAZUMI BABA CEDIYAR YAN GURASA, UMMARU DANJUMA KATSINA ( KASAGI ) INJINIYA MUSA  ABDULLAHI, DA ADO AHMAD GIDAN DABINO (mon)  DA SULE MAJE REJETO, DA HAJIA HALIMA SARMAI DAGA NYAME ,DA ALHAJI KABIRU ASSADA,  Da dai sauran manyan marubuta daga ciki da wajen kasar nan .

 

KALUBALEN DA TARON YA SAMU 

Duk inda aka samu Nasara to akwai kalubale kamar yadda ya bayyana:-

Babban abun da mahalarta taron suka fi korafi a kai shi ne, rashin ba wa marubuta fifiko a wurin taron, maimakon haka sai aka fi maida hankali a wurin bayarda dama ga makada, da mawaka suka barje gumen su, wanda hakan ne ya sa wasu daga cikon marubutan da abin bai yi wa dadi ba, suka rika tambayar , wai taron makada da mawaka ake yi ko taron ranar marubuta a ke yi ?

Hakanan kuma wani kalubale da mahalarta taron suka lura da shi shi ne na rashin halartar, SARAKUNAN KATSINA DA DAURA KO kuma wakilan su, haka kuma baa ga kiccin manyan jami’an gwamnatin jihar Katsina a wurin taron ba, sai dai kawai lokacin taron bada kyaututtuka, haka nan kuma ba’a ga dandazon mahalarta taron daga cikin jama’ar gari ba, kamar ma mutanen gari ba su san ana yi ba .

Wani abin da kuma na lura mahalarta taron da dama sun rika yin korafi a kai shine, na nuna halin ko in kula da masu jan ragamar taron suka rika nuna wa ga wasu daga cikin mutanen da ya kamata a ce taron ya basu kulawa ta musamman, lallai abun damuwa ne matuka irin yanda aka yi taron aka gama ba tare da ko sau daya an bada wata dama ga shugaban kungiyar marubuta ta jihar katsina MAL SHAMSUDDEN IBRAHIM FATIMIYYA ya ce wani abu ba, kuma kowa ya san ko a ina ake taro irin wannan shugaban alummar da suke karbar bakuncin taron  ana bashi wata dama akalla ko dai ya marabci baki, ko kuma ya yi godiya a madadin sauran jamaar sa, amma a wannan taron sam ba’a yi hakan ba . Lallai Fatimiyya ka cika shugaba mai hakuri, abin koyi Allah ya saka maka da alheri .

 

Hakanan  kuma wani abun dubawa shine irin yanda taron ya yi shakulatin bangaro da jarumar da ta yi sanadiyyar assasa taron tun farko, wato FADILA H ALIYU KURFI, abun mamaki ne a ce ko a cikin takardar tsarin jaddawalin taron sam babu sunanta, kuma ko sau daya taron bai ambaci sunan ta ba, tabbas wannan  babban butulci ne, da babu wami abun da ke haddasa shi idan ba hassada ba, koda yake dai hausawa sukan ce baa sauya wa tuwo suna,. Saboda haka ko an ambaci sunan Fadila H  Aliyu Kurfi ko ba’a ambace ta ba , ko an bata wata kulawa ko ba’a bata ba,babu wani mahaluki da ya isa ya sauya tarihin cewa ita din dai ce ta yi sanadiyyar assasa wannan abun alherin da wasu suke ta dagawa suna hura hanci da shi .

 

Haka nan wani abunda ya so zama cikas ga taron shi ne hatsaniyar da ta biyo bayan wata magana da mai gabatarwa ya yi a wurin taron bada kyaututtuka da ya gudana ranar Assabar da dare wato MAL NASIR WADA KHALIL, inda ya danganta marubuta da makaryata, hakan ya yi matukar bata ran wasu da dama daga cikin mahalarta taron .

 

Daga karshe anyi jinjina ga wadansu wadanda suka bada Gudummuwar su domin samun ci gaba.

 

JINJINA TA MUSAMMAN GA WADANNAN MUTANE WADANDA TABBAS BA DAN SU BA WALLAHI TARON NAN DA BAI YUWU BA

 

MAL DANJUMA KATSINA

DOKTA BASHIR ABU SABE

MAL ABDURRAHMAN ALIYU

KOMARED LUKMAN UMAR KANKIA

AISHA MUHAMMAD SABITU MOBIL

BISHIR SULAIMAN (BASH TWINS )

FATIMA S MUHAMMAD

FADILA H ALIYU KURFI

BELLO HAMISU IDA

S.I FATIMIYYA

ABDULHAMID MATAZU

ABUBAKAR AL-MUSTAPHA YAR’ADUA DA SAURANSU.

GODIYA TA MUSAMAN GA DUKKAN BAKIN DA SUKA SAMU DAMAR HALARTAR  WANNAN TARO, DA FATAN ALLAH YA MAIDA KOWA GIDAN SA LAFIYA .

 

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *