Dalilin Da Yasa Nayi Aure Sau Bakwai (7) Inji Sadiya Kabala

Dalilin Da Yasa Nayi Aure Sau Bakwai (7) Inji Sadiya Kabala

Dalilin Da Yasa Nayi Aure Sau Bakwai (7) Inji Sadiya Kabala

0
0

Jarumar Finafinan Hausa Sadiya Kabala, ta bayyana cewa abin da yasa ta yi aure sau 7 a cikin fim din ‘Kwadayi da Buri’ domin ta nuna illar son abin duniya ga ‘yan matan wannan zamanin.

Jarumar, wadda ta fito da sunan Salmah a fim din, ta yi aure barkatai sakamakon kawayen banza, da ta ke dasu wadanda suka rika bata mummunar shawara.

A cewar ta abin da yasa ta fito da wannan halin, domin ta nunawa masu wannan burin a zuciyar su cewa shi fa kwadayi mabudin wahala ne, kuma da mai kudi da talaka, dukansu Allah ya yi su, Allah zai iya azurta wanda yaso a lokacin da ya ga dama, kuma zai iya talauta wanda yaso a lokacin da ya ga dama.

Daga karshe ta shawarci ‘yan uwanta mata da su zamo mutane na gari.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *