An bankado haramtacciyar kasuwar hada hadar man fetur a jihar Katsina

An bankado haramtacciyar kasuwar hada hadar man fetur a jihar Katsina

An bankado haramtacciyar kasuwar hada hadar man fetur a jihar Katsina

0
0

Angano wannan kasuwancin a wani kauye Wanda ake kira Dan-Hako Wanda yake iyaka ne tsakanin Jibiya, Katsina da kuma Maradi ta jihar Nijer. Kauyen yana da mahadar titina daban daban tare da itatuwa.

Kauyen dauke yake da mutane da ke yaren faransanci da kuma wasu mutanen da me yaren Hausa. Kauyen Wanda yake kusa da maganar Ajiwa.

Kauyen Wanda ake haramtacciyar kasuwancin man fetur, Wanda yankasuwar man fetur suke zuwa daga Mali, Barkina Faso da nijer. Man fetur din ana safarar shi daga Jibiya.

Da misalin karfe 7 nasafe naje Jibiya inda na iske angama kammala duk yarjejeniyar da mukayi,sannan ansamo hayar mashina da zasu dauki man domin bi ta cikin yashi.an kuma umurceni da insaya kananan kaga domin samun natsuwa.

Kowane mashin yana dauke da jarka 8 zuwa 10 domin yafi saukin bin hanya mai gashi da kuma isa cikin lokaci.ko wane mashin zai iya daukar lita 250 ta man fetur. Wani abun daure kai da mamaki jami’an tsaro na Nijeriya da na Nijar sanata tsaurara bincike.

Alokacin da muka shigo yar kasuwar zamu boye acikin itatuwa, sukuma manyan motoci zasu shigo domin azuba masu.

Akwai injina na musamman domin zuba man fetur din, mun iske kusan motoci 15 suna layi domin azuba masu. Mafi akasarin masu aikin matasa ne wadanda basu wuce shekaru 18 zuwa 40 ba suna ta kai kawo.

Akwai wata mota mai kirar fijo J5 wadda take dauke da man fetur din. Yar karamar kasuwar tana cine akowane lokacin, ga kuma masu sai da abinci da ruwa ko ina.

Ana hudda taiyar kasuwancin da kudin Nijeriya da kuma na kasar Nijer. Bincike ya nuna  mafi yawancin Yan kasuwar suna yo hayar Motocin ne, sannan suna biyan kowace mota daidai adadin da zata iya dauka.

A jihar Katsina, karsncin man fetur yakai 1.3miliyon ta Lita a duk rana Wanda yayi saidai da ganga 20.

 

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *