Da duminsa: Wata annoba ta kashe dalibai 3 a kwalejin ilimi ta IKCOE, Dutsin-ma 

Da duminsa: Wata annoba ta kashe dalibai 3 a kwalejin ilimi ta IKCOE, Dutsin-ma 

Da duminsa: Wata annoba ta kashe dalibai 3 a kwalejin ilimi ta IKCOE, Dutsin-ma 

0
0

Wata annobar da baa san ko micece ba ta kara bulla a kwalejin ilimi ta Isa Kaita dake Dutsinma.

Ya zuwa yanzu akalla mutane 3 suka rasu bayan wadanda suke kwance a asibiti.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton ba mu samu damar jin ta bakin mahukuntan kwalejin ba.

Idan baa manta ba, a watan jiya ma haka aka samu irin wannan annobar a makarantar kimiyya dake Kurfi inda aka rasa dalibai da dama, wanda daga baya gwamnatun jiha ta rufe makarantar don bincike da kuma yima makarantar feshi.

Haka ma dai mun samu cewa Gwamnatin jihar Katsina kalkashin jagorancin Rt.Hon. Aminu Bello Masari ta yanke shawarar sake bude makarantar kwana ta garin Kurfi bayan barkewar wata annoba wadda tayi sanadiyar mutuwar Dalibai da dama.

Sanarwar ta fito daga hannun sakataren ma’aikatar kimiya da fasaha ta jihar Katsina (Science and Technical Education a turance) Lawal T. Bosa yayin da wakilin mu na Katsina post ya aiko mana da shi.

 

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *