Hotunan wata mata da ta haifi ‘yan 3 a karamar hukumar Sandamu 

Hotunan wata mata da ta haifi ‘yan 3 a karamar hukumar Sandamu 

Hotunan wata mata da ta haifi ‘yan 3 a karamar hukumar Sandamu 

0
0

Wata mata mai suna Maryam Iliya yar kauyen Lugga-tori dake karamar hukumar Sandamu tayi saar haihuwar yan ukku reras, mata biyu da namiji daya.

Matar ta haife su a babban  asibitin karamar hukumar sandamu wato CHC Sandamu, a jiya Litinin. Ta haifi namiji daya da karfe 12 na rana, sai bayan awa 12 wato da karfe sha biyun dare sannan ta kara haifo mata biyun.

Matar ta zo asibiti da kanta, akayi mata yan Gwaje-gwaje a dakin awo, aka tabbatar da lafiyar ta, sannan ta koma dakin haihuwa don nakuda. Cikin ikon Allah ta haihu lafiya ba tare da wata matsala ba.

Wakilin Katsina Post HAUSA Anas Muazu Karkarku yaje har asibitin ya gano wannan jarirai tare da mahaifiyarsu, kuma ya zanta da shugabar maaikatan dakin haihuwar mai suna Maryama Aliyu inda ta tabbatar da aukuwar wannan lamari.

Ana kira ga gwamnati da kuma kungiyoyi don su taimaka ma iyayen wadannan yan ukkun kamar yadda aka saba don rikon yan ukku musamman a wajen marasa galihu yana matukar wahala.

Allah ya kara ma uwar da kuma yayan lafiya.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *