Dr. Lion ya kira ga masu hali da su akagazawa marasa karfi domin samun falalar azumi

Dr. Lion ya kira ga masu hali da su akagazawa marasa karfi domin samun falalar azumi

Dr. Lion ya kira ga masu hali da su akagazawa marasa karfi domin samun falalar azumi

0
0

Dan takarar kujerar Dan majalissar wakilai a karamar hukumar Faskari, da, Sabuwa, da kuma Kankara, Dr Jamilu Muhammad Rabiu wanda aka fi sani da Hon. Jamilu Lion ya yi kira zuwa ga masu hannu da shuni da su taimakawa talakawa a wannan watan na Azumin Ramadan, domin samun alfarmar watan.

Dr Lion ya kuma shawarci jama’a da su yawaita yin sadaka, karatun Al-Qur’ani, da kuma kiyaye munanan ayyuka, domin samun tsira ranar gobe kiyama.

Ya kuma yi wa al’ummar jihar Katsina, musamman na yankin Faskari, da Sabuwa, da kuma Kankara fatan alheri da fatan asha ruwa lafiya, Allah Ya karbi ibadunmu amin

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *