Ababen kiyayewa lokacin buda baki da sahur, daukar nauyi Jamilu Lion

Ababen kiyayewa lokacin buda baki da sahur, daukar nauyi Jamilu Lion

Ababen kiyayewa lokacin buda baki da sahur, daukar nauyi Jamilu Lion

0
0

Dan takarar Dan majalissar wakilai a karamar hukumar Faskari da Sabuwa da kuma Kankara Hon. Dr. Jamilu Lion ya dauki dawainiyar a tunasar da yan uwa Musulmi sadaka fisabilillah a kan abin da ya shafi Sahur da buda baki.

SAHUR: Manzon Allah SAW yace “Ku yi sahur saboda akwai albarka a cikin ta” [ Bukhari Fat’h 4/139]. Sahur na nufin cin abinci ko abun sha wanda mutum zai yi kafin fitowan Alfijir saboda azumtan wannan yinin. Yana daga cikin Sunnah ta Manzon Allah SAW jinkirta Sahur zuwa kusa da lokacin da Alfijir zai fito.

Buda Baki: Manzon Allah SAW ya kasance yana gaggauta buda baki. Ma’ana, yana yin buda baki da zarar rana ta fadi. Jingirta buda baki baya daga cikin sunnah ta Manzon Allah SAW. Yana da kyau mu fahimci yanda Manzon Allah yake buda baki da sahur. Ya kasance yana jinkirta sahur kuma yana gaggauta buda baki.

Anas Bn Malik RA ya kawo hadisi inda yayi bayanin yanda Manzon Allah SAW yake yin buda baki; “Manzon Allah SAW yana yin buda baki da dibino kafin yin sallah (Magariba), idan babu danyen dibino yakan yi da busasshe, idan kuma babu sai ya kurbi ruwa”. [Tirmizi 3/79]

Yana daga cikin sunnah karanta Addu’an buda baki kamar yanda hadisi daga Ibn Umar RA ya ya bayyana cewa Manzon Allah SAW ya kasance yana wannan addu’an a lokacin da yayi buda baki. Addu’an shine “Zahaba zama’u, wabtallat il-‘uruq, wa thabbat al-ajru in sha Allah (kishin ruwa ya tafi, jijiyoyi sun dawo suna gudana, kuma lada ya tabbata a wurin Allah Insha Allah)”.

 

Sakon tunasarwa daga Hon. Dr. Jamilu Muhammad Rabiu (Lion)

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *