Matasa ne mafita wajen warware matsalolin da suka addabi Nigeria – Jamilu Lion

Matasa ne mafita wajen warware matsalolin da suka addabi Nigeria – Jamilu Lion

Matasa ne mafita wajen warware matsalolin da suka addabi Nigeria – Jamilu Lion

0
0

Jigo a jam’iyyar APC a jihar Katsina Hon. Dr. Jamilu Muhammad Katsina ya kirayi matasa da babbar murya a kan da su maido da hankalinsu wajen samarwa Nijeriya mafita wajen warware matsalolin da suka dabaibaye ta.

Dr Jamilu ya fadi haka ne a Abuja lokacin da yake zantawa da manema labarai, inda ya ce matsalolin tsaro da ake samu na da nasaba da rashin samun kyakkyawan shugabanci da kuma ingantaccen tsaro, kamar yadda jaridar Leadership ta rawaito.

“Muna ganin yadda ake ta kashe-kashen rayuka ko’ina, shin matsalar tabarbarewar tsaro ce ko ta shugabanci ce? Kowane fanni na da taka rawarsa wajen samun katangalewar tsaro a kasar nan. Matasa yanzun sune yakamata su zaburo wajen kawar da wadannan matsalolin. Inji Dr Jamilu

Ya kuma kiranyi gwamnati da ta duba yiyyuwar karawa jami’an tsaro kudaden albashi da alawus-alawus dinsu, tare da samar masu da ingantattun kayan ababen hawa da kayan aiki, domin ganin sun sami duk abin da suke bukata wajen samar da kyakkyawan tsaro a cikin kasa.

A bangaren inganta noma kuwa Dr Jamilu ya ce “Ba za ka taba tura mutum zuwa gona ba tare da samar masu ingantacciyar hanya ko samar masu da isasshiyar wutar lantarki. A lokacin da manona za su je gonakinsu domin yin girbi, ba za su iya biyan kudaden da za a fiddo masu da hatsinsu zuwa kasuwa ba saboda tsadar kudin sufuri, ga koma hanyoyin gonakin karkara da suka yi matukar lalacewa … “Inda daga karshe ya nuna gwamnati yakamata ta kara kulawa sosai wajen warware irin wadannan matsalolin domin ciyar da noma gaba sosai

Ya karkare jawabinsa da cewa, shuwagabanni yakamata su sa zurfin tunani mai kyau a kan abin da yakamata su yi wa al’ummarsu. Su kuma matasa a yanzun ya zama dole su mike tsaye su samarwa kansu mafita ba tare da tsayawa jiran shuwagabannin da kawai abin dake gabansu shi ne canza gurbin mukamansu na siyasa, daga Gwamna zuwa Sanata, sannan sai su zarce wajen neman kujerar shugaban kasa.” inji Hon. Dr Jamilu Hon Lion Lion

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *