Yanzu-yanzu: Ingila ta doke Najeriya 2-1 a Wembley

Yanzu-yanzu: Ingila ta doke Najeriya 2-1 a Wembley

Yanzu-yanzu: Ingila ta doke Najeriya 2-1 a Wembley

0
0

Ingila ta doke Najeriya 2-1 a wasan sada zumunci da suka fafata domin shirin gasar cin kofin duniya da za a gudanar a Rasha.

Cahill ne ya fara zura kwallo a ragar Najeriya ana minti bakwai da soma wasa, yayin da Harry Kane ya zura ta kwallo ta biyu bayan an dawo hutun rabin lokaci.

Daga bisani ne kuma Iwobi ya rama wa Najeriya kwallo daya a ragar Ingila.

Kasashen biyu sun fafata ne a filin wasa na Wembley.

Kuma karawar wani zakaran gwajin dafi ne ga kasashen biyu kafin fara gasar cin kofin duniya.

Najeriya har yanzu ta kasa doke Ingila a haduwa uku da suka yi.
Sun taba haduwa a gasar cin kofin duniya da aka gudanar a 2002 inda suka tashi babu ci.

Ingila kuma ta taba doke Najeriya ci 1-0 a karawar da suka yi a 1994.

Najeriya za ta sake karawa da Jamhuriyar Czech a wasan sada zumunci a ranar Laraba kafin tawagar ta Super Eagles su nufi Rasha.

Najeriya za ta fara fafatawa ne tsakaninta da Croatia a gasar cin kofin duniya a ranar 16 ga watan Yuni, kafin ta fafata da Iceland da kuma Argentina a rukuninsu na D.

Ingila kuma za ta sake buga wasan sada zumunci da Costa Rica a ranar Alhamis kafin tawagar kasar su nufi Rasha.

Ingila na rukunin G, inda za ta fara karawa tsakaninta da Tunisia.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *