Tsohon shugaban karamar hukumar Faskari Hon. Nafi’u Garba na yi wa al’ummar karamar hukumar Faskari, Sabuwa da Kankara barka da sallah – Musa Sanusi

Tsohon shugaban karamar hukumar Faskari Hon. Nafi’u Garba na yi wa al’ummar karamar hukumar Faskari, Sabuwa da Kankara barka da sallah – Musa Sanusi

Tsohon shugaban karamar hukumar Faskari Hon. Nafi’u Garba na yi wa al’ummar karamar hukumar Faskari, Sabuwa da Kankara barka da sallah – Musa Sanusi

0
0

A wani taron manema labarai da ya kira wani matashi kuma jigo a jam’iyyar PDP a karamar hukumar Faskari dama jihar Katsina baki daya wato Comr. Musa Sanusi Yankara ya shaidama wakilin Katsina Post cewa, “Amadadin tsohon shugaban karamar hukumar Faskari kuma dan takarar majalisar wakilai mai wakiltar kananan hukumomin kankara, da Faskari da kuma Sabuwa a zaben 2019 mai zuwa, wato Hon. Nafi’u Garba Faskari (Amsa Baba) Raya Karkaran Sarkin Yamman Katsina Hakimin Faskari, na mika sakon barka da sallah ga daukacin al’ummar musulman duniya, musamman yan asalin kana nan hukumomin Kankara, da Faskari, da kuma Sabua, jihar Katsina dama kasarmu Nijeriya baki daya, dafatan Allah Ya karbi ibadunmu kuma ya sa muna cikin ‘yan tattun bayinSa, Allah ya maimaita mana amin.

Comrd. Musa ya kuma kara da cewa zai yi amfani da wannan dama duk a madadin Amsa Baba, domin jajantawa al’ummar garin Yankara bisa iftila’in da ya sami al’ummar garin na rushe-rushen muhalli da kuma asarar rayuka a sakamakon mamakon ruwan sama da aka samu a kwanakin baya a garin, muna rokon Allah Ya ji kan wadanda suka rigamu gidan gaskiya Ya kuma mayarwa da wadanda abin ya shafa da mafificin mafificin AlkhairinSa Amin.

A karshe kuma matashin ya yi wa wakilin namu karin haske kamar haka: “Hon. Nafi’u Garba Faskari na kara godiya ga al’ummar wannan yakin bisa kwarin gwuiwa da nuna goyon baya dari bisa dari da suke ba shi, ya gode kwarai da gaske Allah yasaka wa kowa da Alkhairi, Allah Ya bamu lafia da zama lafia, Ya albarkaci al’ummar kana nan hukumomin Kankara, da Faskari da kuma sabua, Allah Ya kuma bamu damina mai albarka, da fatan za a yi shagulgulan karamar sallah lafia, Allah Ya sa haka Amin.

Mungode!”

 

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *