Gov. Masari muna neman daukinka ka ceci karamar hukumar Bakori kan babbar matsalar da ta tunkaro mu – Kabir Sa’id Khalil

Gov. Masari muna neman daukinka ka ceci karamar hukumar Bakori kan babbar matsalar da ta tunkaro mu – Kabir Sa’id Khalil

Gov. Masari muna neman daukinka ka ceci karamar hukumar Bakori kan babbar matsalar da ta tunkaro mu – Kabir Sa’id Khalil

0
0

Assalamu Alaikum ya maigirma gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari Ina fatan kana cikin koshin lafiya? Ya maigirma gwamna kamar yadda mukasanka adali kuma hazikin gwamna da jihar Katsina ba’a taba gwamna mai son zaman lafiya kamarka ba. Wannan ne yasa muka kawoma kokenmu mu yan karamar hukumar Bakori bisa abubuwan da ke faruwa a kafar yada labarai ta fasbuk (Social media) Abubuwan da ke faruwa a cikin karamar hukumar Bakori ga ma’abota fesbuk na daga cin zarafi kage, zagi da cin mutunci juna sun wuce misali saidai muce Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un domin abubuwan kullum kara munana sukeyi, musamman wani dandali mai suna Bakorian wallahi Maigirma Gwamna Babu wani dandali a cikin jihar Katsina da yafi wannan dandali munana domin nan gaba kadan sai an dauki makamai an fara yaki ta dalilin Bakorian idan ba’a dauki mataki.

Kiranmu ga Maigirma Hazikin, adali gwarzon gwamna shine da ya taimaka ya tsabtace mana Social media a Bakori kamar yadda yayi a garin Funtua a cikin satin nan inda mukaji ka nada kwamitin mutum goma sha daya (11) domin tsabtace social media a funtua.

To Maigirma Gwamna muma muna rokonka da ka taimaka ka nad’a kwamitin da zai tsabtace social media a karamar hukumar Bakori domin abubuwan da suke faruwa a social media din Bakori yafi na Funtua matsala da kashi 60%. Maigirma Gwamna muna godiya muna addu’ar Allah yakarama lafiya, Allah yabaka ikon zarcewa a karo na biyu albarka Annabi da Alkur’ani Ameen ya Allah.

 

Kwamrad Kabir Saidu Khaleel
08062576909

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *