RA’AYI: Roko ga Injiniya Muttaqha Rabe Darma da ya ansa kiran al’umma – Daga Fahad Aliyu Gafai

RA’AYI: Roko ga Injiniya Muttaqha Rabe Darma da ya ansa kiran al’umma – Daga Fahad Aliyu Gafai

RA’AYI: Roko ga Injiniya Muttaqha Rabe Darma da ya ansa kiran al’umma – Daga Fahad Aliyu Gafai

0
0

Hakika Duk Dan Asalin Jihar Katsina Yasan Engr Muttaqha Rabe-Darma, Mnse, Mnim, Misds, Phd, DBA, Dsc, Mutum Ne Wanda Yabawa Wannan Jiha Dama Kasa Baki Daya Gudummuwa Tun Zamanin Marigayi Malam Ummaru Musa Yar’adua.

Engr Muttaqha-Rabe Darma Ya Jagoranci Hukumar Tsaftace Muhalli Ta Jihar Katsina Wato [SEPA] Wadda Ya Taka Muhimmiyar Rawa wajen, Kawo Shirye Shiryen Tsaftace Muhalli, Inda Ya Shafe Shekaru Kusan Ukku A wannan Matsayin Na Director Sepa.

Daga Nan Gwamnatin Marigayi Malam Ummaru Musa Yar’adua Ta Dauke shi Daga Hukumar Tsaftace Muhalli Ta Kaishi A Harkar Wasanni Da Kuma Matasa, Wato Akabashi [Commisioner Of Sport And Youths] Inda Nanma Ya taka Mahimmiyar Rawa A Harkar Wasanni Tareda Samar wa Matasa Abin Yi Dumin Su Dogara Da Kansu, Wanda A lokacin Mu A Jihar Katsina Kowa Sai Alasan Barka.

Haka Zalika Bayan Malam Ummaru Musa Yar’adua Yabar Gwamnan Jihar Katsina, Yaci Gaba Da Tafiya Da Engr Muttaqha Rabe-Darma Inda Aka Bashi ES Na [PTDF] Inda Nanne Engr Ya Taka Muhimmiyar Rawar gani Domin Anan Ne Ya Baje Kolinsa Ta Tallafawa Al’ummar Jihar Katsina Ta Hanyar Kirkiro Scholaship Ta Fidda Yayan Talakawa Wadanda Suka Gama Makarantun Secondary School Domin Yin DEGREE, Na Farko Ko MASTERS, Ko PHD, Akasashen Waje Irinsu England, Malaysia, Sudan, Indian, Norway, Da Sauransu.

Bayan Ya Dawo Gida Daga (PTDF) Babban Abun Burgewa Sai Ya Koma Aikin Koyawar Sa A Jami’ar Bayero Dake Kano (BUK) Wanda A Wannan Jami’a Ba Baƙo Bane Shi, Domin Yayi Koyawa A Wannan Jami’a Na Tsawon Shekaru Goma (10) Ya Shiga Harkar Siyasa Yanzun Kuma Gashi Yana Koyarwa Kyauta Duk Domin Jama’a Su Amfani Rayuwar Su.

Wanda Wannan Ba Karamin Cigaban Al’ummar Wannan Jiha Tamu Bane Dama Kasa Baki Daya, Inda Ya cigaba Da Tallafawa Al’umma A Wannan Ma’aikata Ta [PTDF] Tareda Kirkirar Dakunnan Karatu Na ICT Da Library, Wanda Ni Ina Daya Daga Cikin Wadanda Suka Amfana Da Wannan A Makarantar Govenment Day Senior Secondary School K/Yandaka Katsina.

Waɗannan Kadanne Daga Cikin Irin Gudummuwar Da Engr Dr Muttaqa rabe darma Yabawa Wannan Jiha Dama Kasa Baki Daya A Matsayin Sa Na Ma’aikaci Na Gwamnati, To Ina Ma Ace Ya Tsaya Takarar Wata Kujera Na Tabbata Sai Ansamu Ciga Fiye da Yadda Muke Tunani, A Siyasar Jihar Nan.

Saboda Haka Yakamata Yan’uwana Matasa Nake Ganin Da Mu fito Akafafen Sadar wa Muyi Kiranye Ga Mutane Irinsu Engr Muttaqha Rabe-Darma Dasu Fito, Su Tsunduma A Harkar Siyasa, Wanda Inada Tabbacin Zasu Taka Muhimmiyar Rawa Tareda Kawo Sauyi Acikin Al’umma Domin Samun Cigaba Mai Dorewa, Da Shan Roman Demokradiya.

Haƙƙi Ne Akan Ku Mu Jajirce Wajen Ganin Mun Samu Kyakkyawan Shugabanci Mai Ma’ana Wanda Zai Gina Mana Jihar Mu, Haka Kuma Wajibi Ne Akan Mu Mu Jajirce Wajen Nemo Mutanen Da Zasu Kula Da Haƙƙokin Ilmantar Damu, Mu Lura Da Kyau Zamu Gane Cewa Mai Ilimi Shi Yasan Darajar Ilimi, Dan Haka Kada Muyi Ƙasa A Gwiwa Wajen Nemar Ma Kanmu Shuwagabanni Masu So Da Kishin Al’umma Irin Su Engr. Dr Muttaqha Rabe Darma, Mnse, Mnim, Misds, Phd, DBA, Dsc,.

Muna Fatan Allah Yayi Mana Jagora, Allah Ya Ba Engr. Darma, Damar Amsa Koken Mu.

© Fahad Aliyu Gafai

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *