Gwamna Masari ya baiwa alhazan Katsina Riyal 300 barka da Sallah

Gwamna Masari ya baiwa alhazan Katsina Riyal 300 barka da Sallah

Gwamna Masari ya baiwa alhazan Katsina Riyal 300 barka da Sallah

0
0

Gwamna Aminu Bello Masari ya bada umurnin cewa da zaran alhazai sun koma birnin Makkah a baiwa kowane Alhaji Riyal Dari Ukku (SAR 300) a matsayin goron Sallah.

Kakakin Majalisar Dokoki ta Jihar Katsina kuma Ameerul Hajji na wannan shekara ta 1439 bayan Hijira Alhaji Abubakar Yahya Kusada shine ya bayyana hakan lokacin da ya zagaya Hemomin Alhazan Jihar Katsina domin yi masu barka da fatar alkhairi da neman dacewa da alkhairan dake cikin wannan yini na Arfa.

Alhaji Abubakar Yahya Kusada ya yaba tare da yin godiya ga Alhazan Jihar Katsina saboda biyayya da nuna hakuri da suke yi a cikin wannan aikin ibadah mai cike da kalu bale.

Ya kuma tabbatar masu da cewa wannan kwamiti na kula da hidimar Alhazai da yake jagoranta ba zai yi kasa a guiwa ba wajen kyautata dukkan al’amurran da suka shafi walwala da jin dadin su.

Ameerul Hajjin ya kuma tunatar dasu a kan bukatar dake akwai ta asa kasar mu, Jihar mu da kuma shuwagabannin mu cikin addu’a musamman yadda zabuka ke ta matsowa. Muna rokon Allah Yasa ayi su lafiya a gama lafiya.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *